ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hukumar NCCE Ta Yi Tsare-tsaren Bunƙasa Horar Da Malamai

by Idris Aliyu Daudawa
3 months ago

Babban Jami’i kuma Shugaban hukumar kula d al’amuran kwalejojin ilimi (NCCE), Dakta Angela Ajala,ta bayyana tsare- tsaren da aka  yi wajen ƙoƙarin da ake yi na bunƙasa kwalejojin koyon aikin malanta, duk wannan manufa ita ce ta zummar shi ma Malamin makaranta ya kasance shi ma an inganta ilimin da yake da shi,domin kuwa hakan zai bada damar yin gyara a ɓangaren ilimin bai ɗaya wanda hakan zai sa ƙasa ta bunƙasa.

Ajala ta bayyana hakan ne lokacin da take ganawa da manema labarai akan taken: “Sabon babi kan ilimin Malamin makaranta a Nijeriya”a Abuja ranar Alhamis,ta ce hukumar ta ɓullo da wani sabon babi ne  da zai maida hankali irin sakamakon da za a samu daga cikin azuzuwa.

Ta ce hukumar ta ɓullo da wani sabon babi ne wanda zai mai da hankalin ta ne ta yadda za a maida hankali kan ilimin Malamin makaranta wanda ya dace ya yi daidai da yadda zamani yake tafiya, yayin da ɓanagre ɗaya kuma ayi ƙoƙarin shi yadda Malamin yake ya kasance ya yi ƙoƙari wajen bunƙasa yadda zai gane sana’ar ko aikin nasa na koyarwa.

ADVERTISEMENT

Kamar yadda ta ce, ilimin Malamin makaranta shi ne abu mafi muhimmanci wajen ci gaban ƙasa,ba domin kome ba sai don saboda babu wani tsarin ilimin da zai samu yin numfashi har ya samu wuce irin ingancin nagarta Malaman ta.

“Matuƙar Nijeriya tana buƙatar azuzuwa masu inganci da nagarta, dole ne sai Nijeriya ta samar da ingantattun Malaman makaranta. Idan Nijeriya tana buƙatar ingantattun Malaman makaranta,dole ne sai Nijeriya ta inganta da bunƙasa kwalejojin horar da Malaman makaranta kamar yadda ta furta,’’.

LABARAI MASU NASABA

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

Da take magana kan lamarin da ya shafi bada guraben karatu,Shugabar NCCE ta ƙara yin bayanin cewa ana ci gaba da tattaunawa kan hanya mafi dacewa ta bada guraben karatun kan lamarin da ya shafi ilimin Malamin makaranta,musamman ma tsarin bada gurbin karatu ga mai son ko sha’awar ya zama Malamin makaranta wato NCE,wannan ya haɗa da abubuwan da ake  buƙata ta jarrabawar shiga manyan makarantu UTME.

Ta bayyana dole ne ba za ayi wasa da sa ido ko amfani da duk wata doka ba, duk sharuɗɗan da aka ce dole sai an yi amfani da su, kamata ya yi ayi hakan.

“Dole ne mu cire da barin amfani da wasu dokokin da ba za su taimaka mana ba, amma kuma mu kula da dokokin da za su taimakawa shi aiki na koyarwa.”

Ajala  ta ce tsarin hukumar kulawa da kwalejojin ilimi NCCE  yanzu hukumar ta ta shi daga wadda ake yi mata kallon tana kamar mu bi Yarima mu sha kiɗa, ta kasance wadda ta ke sa ido kan abubuwan kawo ci gaba,ba kawai ta tsaya bane sai aikin amincewa da kwasa- kwasan da ake yi a kwalejojin ilimi ba wato rahoton da kuma abubuwan  da Kwalejojin ilimin suke buƙata ba, har ma sakamakon abubuwan da ake koya a cikin  azuzuwa.

“ Ba kawai za mu lura da lamarin kan abubuwan da suka shigo ba. Mu ma eda akwai buƙatar mu lura da  wacce irin ƙaruwa ce ake samu daga wurinmu.

“Malaman makaranta na wannan zamanin dole su kasance sun iya tafiyar da harkokin komfuta na zamani wato kafofin sadarwar, wato Malami ya kasance yana da basira sanin kome nene, ta ganewa,da kuma yadda zai iaya tafiya da wata damuwar da ta dame shi, yayin da kuma ba tare da fuskantar wata matsala ba,zai iya yin bayani ko kuma kwantar da hankalin wasu idan buƙatar yin hakan ta taso Abin ya dogara ne kan abubuwa huɗu: mutum ya san abinda ke damun sa, yadda zai iya tafiyar da kan sa, iya hulɗa da mutane, ya zama yana da ilimi, mai son harkar kasuwanci, iya yin wani abu mai taimakawa, ga kuma sanin abubuwan da suke faruwa a duniya na daga cikin abubuwan da Malami ya kamata ya mallake su ko kuma wasu daga ciki,”.

Ta ce su gyare- gyaren da ake son yi ba a nufin a kawo naƙasu kan yadda za a gane kwalejojin ilimi ba ne,amma ana son bunƙasa su ne.

“Wannan ya nuna ke nan ɗalibin da ya nuna ya na son zuwa kwalejin ilimi ba wai ya bi ta hanya mai sauƙi ba ne kamar yadda bayanin nata ya nuna,”.

Hakanan ma ta bayyana tsare- tsaren da aka shirya na ɓangaren yadda ake koyarwa,ana kan shiryasu domin su taimakawa Malamin makaranta ya riƙa tafiya da zamani idan yana koyar da ɗaliban shi,sun haɗa da kafar sadarwa ta zamani da bata daɗe da shigowa ba, ko ba  a daɗe da samar da ita ba, lamarin da ya shafi kasuwanci, ilimin sauyin yanayi, da kuma kare yaro.

Kamar yadda ta ce, shi sabon tsarin na koyarwa zai sa Malaman makaranta su shirya wat sarin koyarwa na musamman ba ayi ta amfani da hanyoyin koyarwa  ada aka yi amfani da su a shekarun da suka gabata.

“Fasaha ba za ta maye gurbin Malaman makaranta ba. Amma kuma Malaman da suka gane fasaha za su kasance masu amfani sosai, masu bada gudunmawa sosai za kuma su kasance cikin shirin abinda ka iya faruwa ko ake buƙata a gaba kamar dai yadda jawabin nata ya nuna,”.

Idris Aliyu Daudawa
+ postsBio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tarihin Rayuwar Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim (2)
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kyamar Baƙi: An Sake Kwaso Ƴan Nijeriya 83 Daga Afirka Ta Kudu
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Manoma 60 Da Kayan Aiki A Edo
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tsohon Shugaban Ƙasa Jonathan Ya Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Ƙasa 18 A Jihar Bauchi

MASU ALAKA

Ilimi

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

August 31, 2026
Ilimi

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

August 29, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Ilimi

Kano Ta Yi Zarra Wajen Kashe Kuɗi Don Raya Ilimi A Yammacin Afirka

July 11, 2026
Next Post
Uzodimma: Babu Dimokraɗiyya Idan Babu Hamayya

Uzodimma: Babu Dimokraɗiyya Idan Babu Hamayya

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.