ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka A Fannin Manyan Ababen More Rayuwa Ya Samu Babban Ci Gaba A 2025 

by CGTN Hausa and Sulaiman
8 months ago
Afirka

Lokacin da hasken rana na farko na shekara ta 2026 ya haskaka nahiyar Afirka, yanayin ci gaban Afirka yana bayyana a fili. Idan aka waiwayi shekara ta 2025 da ta gabata, sakamakon hadin gwiwar Sin da Afirka a fagen manyan ababen more rayuwa, ya kafa ingantaccen tushe ga taswirar ci gaban nahiyar Afirka a shekarar 2026.

A yankin hamadar Sahara, an kammala aikin shimfida layin dogo na Aljeriya wanda wani kamfanin Sin ya gina, kuma a tudun gabashin Afirka, layin dogo tsakanin Tanzania da Zambia wanda ake kira “Hanyar Abota” wanda tuni aka fara sabuntawa. Wadannan batutuwa ba kawai matakai ne na aikin gini ba, har ma sun zamo cikakkun misalan aiwatar da “Shawarar Tabbatar Da Cigaban Duniya”(GDI) da Sin ta gabatar. Yayin da har yanzu mutanen duniya ke tattaunawa kan yadda za a cike gibin ci gaban duniya, Kasar Sin da kasashen Afirka, ta hanyar shimfida layukan dogo masu inganci, suna tabbatar da ra’ayoyin da shawarar GDI ta kunsa, irin na “mayar da bukatun jama’a gaban komai”, da “daukar hakikanan matakai”. Matakin ya bullo da wata sabuwar hanyar hadin gwiwar kasashe masu tasowa, a kokarin raya ingantattun ayyuka da karfin dogaro da kai.

Shawarar GDI da Sin ta gabatar, ba magana ce mara tushe ba, kuma ka’idarta ta farko ita ce “karfafa ikon samun ci gaban kowace kasa”. Aikin sabunta layin dogo tsakanin Tanzania da Zambia ya zama misalin ka’idar. Inda bangaren Sin a wannan karo ba ma kawai ya sabunta layin da taragun ba ne, har ma ya samar da wani muhimman ci gaba, wato ba da taimako ga aikin gudanarwa da kulawa da aikin a nan gaba. Cibiyar horaswa dangane da wannan layin dogo da Sin ta kafa, da zummar horar da ma’aikata ’yan kasar Tanzaniya da Zambia, mataki ne dake bayyana cewa ba wai kawai ana gudanar da hadin gwiwa wajen baiwa wannan tsohuwar hanya ta kusan rabin karni sabon kuzari ba ne, har ma da nufin taimakawa wadannan kasashe biyu wajen samun karfin dogaro da kansu, a fannin gudanar da harkokin layin dogo, da samun riba daga jerin sana’o’i dake da nasaba da layin dogo. Wannan ya dace da bukatun shawarar GDI, wato habaka karfin samun ci gaba mai dorewa.

ADVERTISEMENT

Hakazalika, a Aljeriya, ba kawai layin dogo da jiragen kasa aka samar ba, har ma da cikakkun ma’aunai na Sin na layin dogo da suka dace da yanayin hamada, har ma da taimaka wa bangaren Aljeriya wajen gina tsarin fasaha mai dacewa da halayen kasar. Layin dogo, a nan ya zama “dakin koyar da fasaha”, ba wai kawai hanyar jigilar kaya ko fasinjoji ba ne, wato har ma ya daga matsayin fasahohi da masana’antu na kasar.

Ban da haka, Sin ta tsara layin dogo na yammacin Aljeriya bisa ainihin bukatun kasar, duba da cewa Aljeriya tana matukar bukatar hada babban ma’adinin karfe dake cikin kasa da tashar jiragen ruwa ta Bahar Rum, ta yadda Aljeriya ke iya samun wata hanyar ci gaban masana’antar karfe, da habaka karin sana’o’i masu alaka da albarkatu.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

A Gabashin Afirka, aikin layin tashar jiragen ruwa ta Lamu yana nufin baiwa kasasr Sudan ta Kudu, da Habasha damammakin ci gabansu, matakin da ya bayyana ruhin shawarar GDI a fili, wato “kar a bar wata kasa, ko wani mutum a baya”.

A hakika, salon hadin gwiwar Sin da Afirka na sauyawa daga “Abubuwan da Sin ke ginawa a Afirka”, zuwa “Karfin wasu fannoni da Sin da Afirka suke ginawa tare”. Ruhin shawarar GDI ta samar da daidaito, da daukar hakikanan matakai, da tabbatar da dorewar ci gaba, sun bayyana a fili cikin wadannan layukan dogo, da tashoshin jiragen ruwa, da tashoshin wutar lantarki, da aka gina. Wannan ba habaka kayan more rayuwa ne kadai ba, har ma misali ne na daidaitacciyar hanyar samun ci gaba: A yi hadin gwiwa wajen gina ababan more rayuwa, gami da karfafa karfin samun ci gaba ta hanyar dogaro da kai. (Mai rubuta: MINA)

Afirka
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Afirka
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
2023: Gwarazan Jam’iyyu A Karon Battar Zaben Shugaban Kasa

Manyan ‘Yan Siyasar Nijeriya Da Taurarunsu Za Su Haska A 2026

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.