ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manyan ‘Yan Siyasar Nijeriya Da Taurarunsu Za Su Haska A 2026

by Yusuf Shuaibu, Sulaiman and Sani Anwar
6 months ago
Siyasa

shekarar 2027 ne Nijeriya za ta gudanar da babban zabenta, wanda a 2026 ita ce shekarar da ake gudanar da yakin neman zabe da jawo hankalin masu jefa kuri’a da kuma sake zana taswirar siyasa. Bisa ga yadda abubuwa suke tafiya a yanzu, dukkan idanu za su kasance a kan wasu manyan ‘yan siyasa da tauraransu za ta haskaka a wannan sabuwar shekara.

 

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu

ADVERTISEMENT

Bayan ya samu tikitin kai tsaye na jam’iyyarsa ta APC, don ya sake tsayawa takarar shugaban kasa karo na biyu, shekarar 2026 za ta kasance shekara mai matukar muhimmanci ga Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu. Lokacin mulkinsa na farko ya kasance an bayyana shi da gyare-gyaren tattalin arziki masu karfi irin su daga darajar naira da cire tallafin man fetur wanda ya janyo matsin tattalin arziki.

Mutane za su so ganin yadda zai sarrafa sakamakon wadannan manufofi masu tsauri ta hayar yaki nema zabe. Zuwa farkon shekarar 2026, matsin tattalin arziki da ake fuskanta za su zama makamin siyasa mafi karfi a kasar nan. A al’ada, ‘yan Nijeriya suna kada kuri’asu ne bisa lura da  asalin kabila da yanki, amma 2026 na iya nuna wani sauyi zuwa zaben da ake yin sa bisa gwazon gwamnati wajen samar da ababen more rayuwa.

LABARAI MASU NASABA

Amurka Ta Yi Alƙawarin Sa Ido Sosai A Zaɓen Nijeriya Na 2027

Sautin Muryar Da Aka Fallasa Kan El-Rufai Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara

 

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio

A yayin da majalisar dattawa ta 10 ke shiga mataki na karshe na kalandar majalisa ta 2025, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya samu kansa a sarkakakiya na sake sauya kundin tsarin mulki. Kafin shekarar 2026, akwai wasu muhimman batutuwa da ke kan tebur. Mafi muhimmanci daga ciki su ne, kirkirar ‘yansandar jihohi don magance matsalar tsaro da ke karuwa a kasar.

Majalisar Dattawa na kokarin sanya gyara a kundin tsarin mulki domin bai wa jihohi izinin kafa nasu ‘yansanda. Wannan yana nufin bai wa gwamnonin jihohi da shugabannin kananan hukumomi ikon samar da tsaro a yankunansu. Wani abu da ya shafi wannan shi ne, bukatar kirkirar sabbin jihohi. A yanzu, wannan kokari ya kai kololuwa tare da gabatar da daruruwan shawarwari ga kwamitin sake kundin tsarin mulki na majalisa. Rahotanni sun nuna cewa majalisar dattawa ta samu bukatu fiye da 30 na kirkirar sabbin jihohi.

A kwanakin baya ne, Akpabio ya sake tayar da sabon fata kan kirkirar Jihar Ibadan, yana bayyana hakan a matsayin bukata ta jama’a yayin ziyararsa ga Olubadan na Ibadanland. A tarihi, kirkirar jiha abu ne mai wahala sosai, yana bukatar samun rinjaye kashi biyu bisa uku a cikin duka majalisar tarayya da majalisun jihohi guda 36. Masu ruwa da tsaki za su kasance cikin fatan ganin yadda wadannan al’amura za su wakana a shekarar 2026.

Hazalika, ana gudanar da manyan sauye-sauye a tsarin zabe don magance kura-kuren da aka gani a zabukan 2023. Don samun ingancin tsarin, akwai kudirin da aka gabatar kan yin zabukan shugaban kasa da gwamnoni a watan Nuwamba 2026 maimakon 2027. Muhimmin gyara da ake tattaunawa shi ne, warware dukkan shara’o’in a kotu kafin a rantsar da wanda ya ci zabe.

A matsayinsa na shugaban majalisar dattawa, ana kallon Akpabio a matsayin garkuwar dokoki ga fadar shugaban kasa. Tasirinsa a kudu maso kudu da ikon da yake da shi na tabbatar da cewa ajandar dokoki ta kasance mai amfani ga Tinubu ya sa ya shiga ciki wadanda taurarosu za ta haska a 2026.

 

Peter Obi

Yayin da Peter Obi ya bayyana komawarsa jam’iyyar ADC, a matsayin jam’iyyar hadin gwiwar jam’iyyun adawa, don cimma burin siyasarsa a 2027. Har yanzu yana daga cikin wadanda taurarosu za ta haska a ciki siyasar Nijeriya. Ba kamar Atiku Abubakar ba, wanda ya a hukumance ya yi murabus daga PDP kuma ya karbi katin ADC a wani taron da aka gudanar, Obi ya sauya sheka ne daga jam’iyyar LP.

Babban abin mamaki shi ne, ko Obi zai amice ya zama mataimakin takarar Atiku. Ya bayyana cewa zai yi takarar shugaba kasa ne kawai, duk da haka yana ci gaba da zama a tebur daya da Atiku a tarurrukan jam’iyyar ADC. Akwai jita-jita cewa Obi yana jiran sakamakon gyaran tsarin mulki, musamman sabon jadawalin dokar zabe ta 2025, kafin ya tsai da shawara.

A lokuta da dama Obi ya ambata cewa zai kasance zai yi wa’adi mulki guda ne na shekara hudu wajen farfado da kasar. Duk da haka, bai fayyace ko wannan tayin wani bangare ne na yarjejeniya don samun goyon bayan Atiku ko kuwa alkawari ne na musamman ga masu zabe ba. Shirin Obi zai tabata ne a lokacin babban taron ADC da ake sa ran za a yi a farkon shekarar 2026.

 

Rabiu Kwankwaso

Rabiu Kwankwaso yana ci gaba da tallata burinsa na siyasa, yana taka rawar gani a cikin siyasar Nijeriya wanda ke sa shi watakila ya yi rashin tabbas a siyasar 2027.

Yayin da Atiku da Obi suka sauya sheka zuwa ADC, Kwankwaso ya ci gaba da zama jam’iyyar NNPP a matsayin tsani mai karfi, ya ki shiga kowace hadakar jam’iyyun adawa.

A makon jiya, a ranar 20 ga Disamba, 2025, ya shirya babban taron NNPP a Abuja, inda ya yi alfahari cewa NNPP ita ce jam’iyyar mafi daidaito da tsara a Nijeriya, yana barrata ta da rikice-rikicen cikin gida na APC da PDP. Ya jaddada cewa burinsa na lashe zaben shugaban kasa a 2027, ba tare da zama dan takarar mataimakin shugaban kasa ga Atiku ko wani ba.

 

Rotimi Amaechi

Amaechi ya shafe ‘yan watannin karshe na 2025 yana kokarin dawo da kansa cikin siyasar Nijeriya ta hanyar haduwa da kungiyoyin kawance. A watan Yulin 2025, a hukumace ya sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC kuma ya yi alkawarin fuskantar Shugaba Tinubu kai tsaye a 2027.

A halin yanzu, yana sanya kansa a matsayin daya daga ciki ‘yan takarar shugana kasa guda uku a jam’iyyar ADC. A kwanakin baya, an ga hotunan tallansa a biranen Arewa kamar Kaduna, inda ake bayyana shi a matsayin mutum daya da zai iya yi aikin. Duk da haka, masu nazarin siyasa suna ganin wannan yana kama da wani babban wasa, domin ba tare da samun goyon baya daga Jihar Ribas da zai kawo ba, karfinsa na tare da Atiku da Obi zai ragu sosai. Idan har sakamakon zaben kananan hukumomi na 30 ga Agusta, 2025 zai iya zama misali, tasirin Amaechi a matakin kasa yana cikin rauni tun daga 1999. Muhimmancinsa yanzu ya dogara kusan gaba daya ga nasarar hadin jam’iyyun adawa na kasa.

Rahotani su bayyana cewa yawancin tsoffin kwamishinansa da shugabannin kananan hukumominsa ko dai sun koma bagaren Wike ko kuma sun yi hadin kai da Gwamna Siminalayi Fubara. Ba tare da samun gagarumin goyan baya a gida ba, Amaechi ba zai yi tasiri ba. Sai dai kuma burinsa na zama shugaban kasa na tattare ne a shekarar 2026.

 

Nyesom Wike

Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya kasance babban jarumin siyasa. Duk da yake yana aiki a cikin majalisar Tinubu, yana ci gaba da rike iko a wani babban bangare na PDP. A shekarar 2026, rawar da yake takawa mai nauyi wacce ta hada yin aiki ga shugaba kasa yayin da yake rike da kafar ‘yan adawa, za ta kasance daya daga cikin mafi rikitarwa a ayyukan da za a kalla.

 

Rauf Aregbesola

Rauf Aregbesola yana cikin manyan ‘yan siyasar kasar nan da tauraronsu za ta haska a wannan shekarar. Bayan an kore shi daga APC, ya kasance babban abokin Tinubu tare da wata shakka ba, ya karya dukkan alakarsa da gwamnatin Tinubu domin jagorantar siyasarsa. Rayuwarsa da muhimmancinsa a siyasar kasar nan suna dogara ne a kan Jiharsa ta Osun da sabon rawar da yake takawa a hadin gwiwar adawa.

A matsayinsa na sakataren jam’iyyar ADC na wucin gadi, yanzu yana kan gaba a cikin ‘yan adawa. Muhimmancin Aregbesola ya dogara gaba daya ne kan ko har yanzu zai iya kawo nasara a Osun. Yanzu haka yana yaki a bangare biyu. Na farko, hadin gwiwar dabaru da Aregbesola ya yi da Gwamna Ademola Adeleke a 2022 ya rushe. Adeleke wanda kwanan nan ya koma Jam’iyyar Accord ya bayyana cewa mulkin Aregbesola shi ne mafi muni a tarihin Osun.

Idan ADC ta kasa yin tasiri sosai a zaben gwamnan Osun na 2026, tasirin Aregbesola a siyasa zai ragu a matakin kasa. Zai shiga shekarar 2027 a matsayin shugaba mara tasiri a ciki gidasa.

 

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan

Ga shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, zabukan 2026 na jihohin Ekiti da Osun za su kasance zakaran gwajin dafi a jagorancinsa. A matsayinsa na  kararren masani, Amupitan ya shiga wannan matsayin da umarni na sake gina amincewar jama’a bayan rikice-rikicen zabukan 2023. Zabukan 2026 na jihohin Osun da Ekiti su ne manyan gwaje-gwaje na farko kafin babban zaben 2027. Za a mai da hankali kan amfani da fasaha ba tare da matsala ba da kuma rashin son zuciyar hukumomin tsaro.

A tarihin, Jihar Osun tana daga cikin jihohi masu samun rikicin zabe, a zaben Jihar Osun zai gwada iyawar hukumar wajen sarrafa yanayi mai matukar kwantar da hankali da warware rikice-rikicen sakamako zabe a kan lokacin. Ya yi alkawarin gyara matsalolin da suka shafi na’urar zabe.

Masu kada kuri’a jihohin Osun da Ekiti za su kasance a shirye don ganin ko sakamakon za a dora shi nan take ta na’urar zabe. Idan Farfesa Amupitan bai samu damar gudanar da wata tsari mai inganci a wadannan jihohi biyu ba, ko shakku babu zai yi wahala ya samu nasara a zaben 2027. Akasin haka, gudanar da tsari a fili a Ekiti da Osun zai tabbatar da nadinsa a matsayin shugaba mai gyara kuma zai ba shi kima a siyasa da ake bukata don kula da zabukan kasa.

Siyasa
Yusuf Shuaibu
+ posts Bio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Amurka Ta Yi Alƙawarin Sa Ido Sosai A Zaɓen Nijeriya Na 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Sautin Muryar Da Aka Fallasa Kan El-Rufai Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Ci-ma-zaunen Ƴan Siyasa Ne Ke Tunanin Yin Maguɗi A Zaɓen 2027 – Makarfi
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    An Samu Ruɗani Kan Rashin Bayyana Jerin Ƴan Takarar Jam’iyyun Siyasa Na Zaɓen 2027
Siyasa
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai
  • Sulaiman
    Lalata Da Ƙaramar Yarinya: Kotu Ta Yanke Wa Tsoho Mai Shekara 75 Hukuncin Ɗaurin Shekara 10 A Ribas
  • Sulaiman
    Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin
  • Sulaiman
    Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya
Siyasa
Sani Anwar
+ posts Bio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Shugaban Rundunar Sojojin Nijeriya Ya Nemi Haɗin Kan Fararen Hula
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ƴan Ƙwadago Sun Buƙaci Naira 300,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    NiMet Ta Gargaɗi Jihohi 27 Kan Barazanar Ambaliyar Ruwa A Farkon Watan Yuli
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027: Masu Ruwa Da Tsaki Sun Amince Da Jamilu Gwamna A Matsayin Gwamnan Gombe

MASU ALAKA

Amurka Ta Yi Alƙawarin Sa Ido Sosai A Zaɓen Nijeriya Na 2027
Tambarin Dimokuradiyya

Amurka Ta Yi Alƙawarin Sa Ido Sosai A Zaɓen Nijeriya Na 2027

July 11, 2026
Sautin Muryar Da Aka Fallasa Kan El-Rufai Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara
Tambarin Dimokuradiyya

Sautin Muryar Da Aka Fallasa Kan El-Rufai Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara

July 11, 2026
makarfi
Tambarin Dimokuradiyya

Ci-ma-zaunen Ƴan Siyasa Ne Ke Tunanin Yin Maguɗi A Zaɓen 2027 – Makarfi

June 26, 2026
Next Post
Tsarin Dokoki Ne Kan Gaba Wajen Samar Da Kyakkyawan Muhallin Kasuwanci

Tsarin Dokoki Ne Kan Gaba Wajen Samar Da Kyakkyawan Muhallin Kasuwanci

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

July 15, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Lalata Da Ƙaramar Yarinya: Kotu Ta Yanke Wa Tsoho Mai Shekara 75 Hukuncin Ɗaurin Shekara 10 A Ribas

July 15, 2026
Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

July 15, 2026
‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

July 15, 2026
Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

July 15, 2026
Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

‘Yansanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kano

July 15, 2026
Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.