ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hanyoyi 5 Na Sace Zuciyar Maigida A Zamantakewar Aure

by Sulaiman and Bilkisu Tijjani
4 months ago
Aure

Zamantakewar aure wata hanya ce ta hadin kai da soyayya tsakanin namiji da mace. Duk da cewa aure yana cike da albarka da farin ciki, hakan baya nufin babu kalubale. Akwai lokutan da za a samu sabani, amma abu mafi muhimmanci shi ne hakuri da fahimtar juna.

Idan mace tana so ta sace zuciyar mijinta ta yadda zai kara kaunarta kuma ya fi jin dadin zama da ita, akwai wasu hanyoyi da za tabi domin tabbatar da hakan. Ga hanyoyi biyar da suka fi muhimmanci:

1. Ki so iyayensa da dangi: Namiji yana matukar jin dadin mace wacce ke girmama iyayensa da ‘yan uwansa.

ADVERTISEMENT

Idan kika nuna kauna ga danginsa, hakan yana karfafa soyayyarsa a gare ki.

Kada ki rika ganin danginsa a matsayin abokan gaba, sai dai ki zamanto mai lallashi da sulhu a duk lokacin da aka samu matsala.

LABARAI MASU NASABA

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

Yana da kyau ki rika zama da su da mutunta su, kuma ki guji fada da su ko yin gunaguni akansu.

2. Ki guji yi masa binciken Kwokkaf:

Duk da cewa mace tana da ‘yancin sanin halin mijinta, kwakkwaf da bincike fiye da kima na iya lalata zaman aure. Kada ki rika binciken wayarsa ko jin dadin bincike kan inda yake. Idan akwai damuwa, ki tambaye shi cikin nutsuwa da salo mai kyau.

Yin bincike yana kara matsin lamba a zamantakewa, wanda kan iya sa namiji ya fara nema ko’ina domin samun nutsuwa.

Idan kika zama mace mai aminta da mijinta, zai kara kaunarki kuma ba zai boye miki sirrinsa ba.

3. Ki darajanta Shi tare da bashi girma: Namiji yana son mace mai girmamawa da biyayya, ba mai fada da gardama ba.

Yana da muhimmanci mace ta girmama mijinta a gaban mutane da a sirrance.

Kada ki rika kushe shi ko rage masa daraja, musamman idan kuna tare da dangi ko abokai.

Ki rika jin tausayinsa, ki yi mishi maganganu masu dadi, kuma ki rika yi masa godiya idan yayi miki abu mai kyau.

4. Ki kula tare da tattala masa dukiyarsa:

Wata mace na ganin cewa dukiyar mijinta ba ta da mahimmanci, amma mazaje na son mace mai kula da tattalin arzikinsu. Idan yana da hali, kada ki rika bata kudi a banza.

Idan ba shi da hali sosai, ki taya shi neman na halal ko kuma ki koyi sana’a don rage masa nauyi. Kada ki rika neman abubuwan da yafi karfinsa, hakan na iya sa shi jin takaici.

5. Ki taimaka masa lokacin da bashi da hali:

Akwai lokutan da namiji zai iya shiga cikin wahalar rayuwa, musamman idan ya rasa aiki ko yana fama da matsin tattalin arziki.

Mace mai hankali za ta tsaya da shi, ba wai ta guje shi ba.

Ki kasance mace mai goyon baya, ki yi amfani da hikima wajen faranta masa rai.

Idan kina da sana’a ko aiki, ki taimaka da abinda kika samu har sai ya fita daga matsalarsa.

Idan kika bi wadannan hanyoyi, mijinki zai kara sonki kuma soyayyarku za taci gaba da karfafa har abada.

Aure
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
Aure
Bilkisu Tijjani
+ posts Bio
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Tuwon Alkama Da Miyar Taushe
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa

MASU ALAKA

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)
Uwargida Sarautar Mata

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)

July 5, 2026
Aure
Uwargida Sarautar Mata

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

June 27, 2026
Wasu Abubuwa Da Ke Sa Maza Hana Mata Fita Unguwa (Uwargida)
Uwargida Sarautar Mata

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

June 21, 2026
Next Post
Lokacin Da Duniya Ke Kira Ga Zaman Lafiya, Japan Ta Zabi “Sake Daukar Makamai”!

Lokacin Da Duniya Ke Kira Ga Zaman Lafiya, Japan Ta Zabi "Sake Daukar Makamai"!

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.