Dukkan Godiya ta tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad SAW, da Sahabbansa da ƴaƴan gidan sa da dukkanin waɗanda suka bi hanyar su, har izuwa ga ranar Alƙiyama.
Da farko, bayan murna ga wannan ƙwarya-ƙwaryan zama da yara manyan gobe a ƙarƙashin shugaban cin Malamin su, Malam Ahmad suka shirya.
Wannan Rana (ranar ƴanci), rana ce da ya dace a bata mahimmanci sosai, musamman Malaman Addini. Rana ce da ya dace su riƙe ta da kyau, da zasu dinga bayani a addinan ce, Meye ƴan ci? Ƴan ci shine tushen komai, hatta Ibada – bin Allah, in baka da ƴan ci bazaka Iya ta ba.
Don haka rabbul izzati, shi ne Wanda ya fara nuna girman ƴan ci, shine Wanda ya fara bawa bayin sa ƴanci (Subhanaka wa ta’ala), izan ƴanci sai yazama shi ne asali Wanda ake tafiyar da komai.
Allah yaba wa ɗan Adam ƙudirar sa (Shi Ubangiji), ya bawa ɗan Adam iradar sa, jin sa, ilimin sa ya bawa ɗan Adam dukkansu guda bakwai. Sabida waɗannan abubuwan da yabashi sai ya canza masa sunan sa, sai Ubangiji ya kirashi da Khalifah (“…inni ja’ilun fil Ardi Khalifah” Ma’ana: zan sanya Kalifa na akan ƙasa).
Kafin Allah yaba wa ɗan Adam waɗan can sunayen guda bakwai, sunan shi Halitta (“…inni kaliƙun basharan min ɗin” Ma’ana: Ni zan halicci Mutum daga taɓo).
Yanzu Allah ya sanya mu Khalifofi a ƙasa, me Allah yake nema a wajen mu ya san yamu kalifofi akan ƙasa? Sama ba wurin mu ba ne, wajen Mala’iku ne, Tasbihi da tsarkake wa suke yi amma mukuma ƴaƴan Adam sai muka haɗa duka, mukayi aikin Mala’iku kuma mukayi aikin mu.
Muna tasbihi, Sallah da duk ibada sannan kuma mukayi aikin da aka kawo mu – gina ƙasa, gina ɗan Adam sannan bauta wa Allah, Sai yabamu ƴan ci don muyi wannan abubuwa Uku da aka ɗaura mana (gina ƙasa da ɗan Adam sannan bauta wa Allah).
Don haka, Wanda ya gina dimokaraɗiyya yace “in aka lalata bautar Allah, aka lalata gina ƙasa da ƴan ƙasa to dimokaraɗiyya ta lalace”.
Sabida haka, duk in munyi maganar ƴan ci muna magana ne kan baiwar da Allah yayi mana ne, sannan Allah ya ajiye mu yaga me zamu aikata da wannan baiwa da yabamu. Allah yabamu ƙudra da irada (ya baka ji, gani da hankali) sannan ya naɗa ka a matsayin Kalifan sa.
Haka Annabi Muhammad SAW, Allah ne ya karantar da shi, ya nuna mana meye ƴan ci, meye zaman ƴan ci, ya zaman bauta yake da zaman ƴan ci.
Zaman Makkah, zaman bauta ne, Babu ƴanci, ba bu damar gudanar da shirye-shiryen ibada, Annabi Muhammad SAW ya nuna mana yadda ake zama a irin wannan yanayi sannan kuma ya sake nuna mana yadda ake zama a garin da bana ka ba, ba kuma irin Addinin ka ake yi ba amma mutan garin suna da hankali da kirki, sun yarda kayi irin Addinin ka azauna lafiya, zaman sahabban Annabi a Afirka, Ethiopia suka koya mana yadda ake wannan zaman, Sahabbai larabawa ne amma mutanen Najashi Afirka ne, Amma wayewar sahabbai tasa sun zauna lafiya sabida su sahabbai ƴan makatantar Annabi Muhammad SAW ne.
Haka kuma, ya koya mana yadda zaka zauna da ƙasar da ta yadda kai ɗanta ne, ta yarda kayi Addinin ka amma ƙasar tana da Addina tai da yawa, wannan shine farkon zaman Madina, Mutanen Madina sun karɓi Annabi da sahabban sa a matsayin ƴan ƙasa. Hakan tasa aka rubuta kundun tsarin mulki, kan yadda za a kare ƙasa, kowa yayi Addinin sa cikin ni’ima da kwanciyar hankali.
Haka aka tafi, har kuma Allah yabawa Annabi Muhammad SAW da sahabban sa ƴan ci ya zama shine sarkin ƙasa kuma shugaban ƙasa, Wazirorin ƙasa da hakimanta duk nasa ne. Hakan taba wa Annabi Muhammad SAW damar shimfiɗa dukkan wannan alkairi, ba don ƴan ci ba da duk Hakan bata faru ba.
Duk ɗan Adam, inda zai samu ƴan ci yake nema, Manzon Allah SAW ya halarci jana’izar wani daga cikin sahabban sa mutumin Madina a maƙabartar baƙi’a, sai Annabi yace “ina ma a baƙunta ya mutu”, sai sahabbai suka ce Ya Rasulullahi Meye Banbancin Mutuwar gida da ta baƙunta? Sai yace “za a auna tun daga garin su zuwa inda yake baƙunta a bashi a Aljannah”.
Wannan magana ce da zata nuna wani abu. Duk ɗan Adam ƙalla ne zakaga a garin su aka haifeshi kuma ya ɗau kaka a garin su. Ana samu amma ƙalla, zakaga In arziƙi ne sai yatafi wani gari ko karatu ne sai ya tafi wani gari. Meyesa haka? Sabida a can garin zai sami ƴan ci. Amma in a gida ne, zakaji ana cewa, ba ɗan wane ba ne.
Don haka, ƴan ci abune mai kyau, mun samu ƴan ci a Nijeriya yau shekara Sittin da ɗaya (61). Ya dace malamai suyi tayin maganar ƴan ci su San ma’anar sa, kuma me ake nufi da shi, shine asalin komai, kuma don mu aikata wannan ƴan cin, don alkairin sa ya dawo mana.
Allah yaba wa ƙasar mu lafiya da arziki, Allah ya yaye mana dukkan abinda ya da me mu ya bamu dukkan alkairai, Allah yasa muyi aikin kafa wannan ƴanci da yabamu, Allah yasa muyi aiki da wannan ƴanci da Annabi Muhammad SAW ya koya mana.
Muna godiya ga Malam Ahmadu da wannan taro da kuka shirya, Allah yayi wa rayuwa albarka yayi buɗi na arziƙi yaja da rayuwa.
Muna godiya ga Wanda albarkar sa duk wannan alkairan suke faruwa, Allah yasaka masa da alkairi, ya ja kwana yayi albarka ga rayuwa ya nuna masa abinda zai ta farin ciki a rayuwa albarkar manzon Allah SAW.
Shehu Ibrahim Inyas yana cewa in mutum ya muku alkairi Ku rama, in baza ku iya ramawa ba to ku rama masa da addu’a.














