ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hukumar Kula Da Abuja Ta Haramta Amfani Da Tayoyi Wajen Gasa Sassan Dabbobi

by Sulaiman and Rabi'u Ali Indabawa
4 months ago
Abuja

Hukumar Kula da Babban Tarayya Abuja ta aiwatar da haramcin amfani da tsofaffin tayoyi wajen gasa sassan dabba a wajen mahauta na Kubwa, da ke Karamar Hukumar Bwari, bayan wani rahoto ya nuna irin hadarin lafiyar da wannan dabi’a ke haifarwa.

Bayan wani bincike da aka gudanar, an gano cewa wasu mahauta na amfani da tayoyi da aka kone wajen cire gashin dabbobi, lamarin da ke haifar da damuwa kan lafiyar jama’a da kuma ingancin abinci.

A ziyarar da aka sake kaiwa wurin, an ga cewa mahautan sun daina amfani da tayoyi, inda suka koma amfani da itacen wuta. An kuma ga manyan tarin itace a wuraren gasshin domin ci gaba da aikinsu.

ADVERTISEMENT

Wasu daga cikin mahautan sun bayyana cewa jami’an Sashen Aikin Gona da Raya Karkara na FCT sun kai samame bayan rahoton ya fito, sannan suka tilasta aiwatar da haramcin.

“Bayan rahoton ne suka zo suka hana mu amfani da tayoyi. Yanzu ba mu da wani zabi illa mu koma amfani da itacen wuta,” in ji daya daga cikin mahautan, yana nuna damuwa kan karin kudin aiki.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Wani likitan dabbobi da ke aiki a wurin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da cewa an aiwatar da matakin hana amfani da tayoyi. Ya ce hukumomi sun sha gargadi kafin daukar matakin tilas.

“Mun dade muna wayar da kai kan illolin lafiya, amma ba a cika bin umarni ba. Bayan rahoton, sai muka tilasta aiwatar da haramcin,” in ji shi.

Ya kuma kara da cewa an shawarci mahauta da su daidaita farashin aikinsu saboda karin kudin da amfani da hanyoyin da ba su da illa ke jawowa, yayin da ake kuma kira ga masu saye su fi mayar da hankali kan lafiya maimakon arha.

“Ya kamata mutane su fi mayar da hankali wajen sayen nama mai inganci ko da zai dan yi tsada, maimakon su jefa kansu cikin hadarin rashin lafiya,” in ji shi.

Abuja
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato
  • Sulaiman
    Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya
  • Sulaiman
    Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta
  • Sulaiman
    Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen
Abuja
Rabi'u Ali Indabawa
+ posts Bio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato
Manyan Labarai

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci
Manyan Labarai

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Abuja
Labarai

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Next Post
EFCC Na Neman Tsohuwar Ministar Buhari, Sadiya Farouq Ruwa A Jallo

EFCC Na Neman Tsohuwar Ministar Buhari, Sadiya Farouq Ruwa A Jallo

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
Abuja

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Abuja

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.