ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jadawalin Zaɓen 2027: Masana Da Ƴan Siyasa Na Tafka Muhawara

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto, Sulaiman and CGTN Hausa
1 month ago
Siyasa

A yayin da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta fitar da jawadalin Babban Zaɓen 2027, masu ruwa da tsaki da masana na ci gaba da bayyana ra’ayoyin su kan jadawalin zaɓen wanda zai jagoranci sababbin shugabanni a mabambantan kujeru.

Fitar da sanarwar jadawalin zaɓen 2027 ya bai wa mabambantan jam’iyyun siyasa damar gudanar da tsare- tsaren yadda za su gudanar da yekuwar neman zaɓe da yadda za su fafata a zaɓen wanda ake da tabbacin zai ɗauki hankalin al’ummar ciki da wajen ƙasa.A sanarwar da Hukumar Zaɓe ta fitar ta bayyana cewar za a fara gudanar da yekuwar neman zaɓen Shugaban Ƙasa da na Ƴan Majalisar Dokoki ta Ƙasa a ranar 19 ga Agusta, 2026 kuma za a kammala yekuwar a ranar Juma’a, 15 ga Janairu, 2027, sa’o’i 24 kafin gudanar da zaɓen da za a yi a ranar Asabar, 16 ga Janairu, 2027.

Hukumar ta kuma bayyana cewa yekuwar neman zaɓen Gwamna da na Ƴan Majalisar Dokokin Jihohi zai fara ne a ranar Laraba, 9 ga Satumba, 2026, za a kammala a ranar Juma’a, 5 ga Fabrairu, 2027, gabanin zaɓen da za a gudanar a ranar Asabar, 6 ga Fabrairu, 2027.

ADVERTISEMENT

A cewar Hukumar Zaɓen, ta bayyana cewar an tsara jadawalin ne bisa tanadin Dokar Zabe ta 2026 wadda ta tanadi cewa ba a yarda jam’iyyun siyasa su fara yekuwar neman zaɓe fiye da kwanaki 150 kafin ranar zaɓe ba, kuma dole ne su dakatar da duk wani gangamin neman ƙuri’a aƙalla sa’o’i 24 kafin ranar jefa ƙuri’a.

Haka kuma sashe na 98 (2) na dokar zaɓe ya bayyana cewar duk wata jam’iyyar siyasa da ta yi yekuwar neman zaɓe ko ta bari aka yi mata, talla ko kamfen ta kowace irin hanya cikin sa’o’i 24 kafin ranar zaɓe, ko ta hanyar gidan rediyo da talabijin ko kuma ta hanyar jaridu, da nufin tallata ko yaƙi da wani ɗan takara, ta aikata laifi a ƙarƙashin dokar kuma za ta fuskanci hukunci a kotu.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

A kan wannan Hukumar Zaɓe ta tunatar da jam’iyyun siyasa, ƴan takara da magoya bayansu cewa ba su da hurumin fara yekuwar neman zaɓe kafin ranakun da aka amince da su tare da gargaɗin cewa duk wanda ya karya dokar zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada.

Hukumar ta ƙara da cewa sabon jadawalin ya maye gurbin duk wani jadawalin da ta fitar a baya, kuma shi ne zai kasance jagoran gudanar da dukkanin ayyukan yekuwar neman zaɓe gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

LEADERSHIP Hausa ta labarto cewar duk da yake an fitar da jadawalin ne kwanan nan, tuni masu ruwa da tsaki suka fara sukar yadda wasu jam’iyyun siyasa, ƴan takara da magoya bayansu suka fara yaƙin neman zabe gabanin lokaci ta hanyar liƙa fastoci, baje kolin allunan talla da sauran nau’ukan kamfen tun kafin lokacin da doka ta amince.

A cewarsu, irin waɗannan matakan sun saɓawa tanade-tanaden dokar zaɓe kuma hakan ne ke haifar da saɓani da rikita- rikita a tsakanin jam’iyyun siyasa don haka suke da ra’ayin wajibi ne Hukumar Zaɓe ta riƙa aiwatar da hukuncin da dokar ta tanada domin waɗanda abin ya shafa su shiga taitayin su.

Jam’iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki sun yi maraba da sabon jadawalin tare da cewar ya kawo ƙarshen cece-ku-cen da ya biyo bayan jadawalin farko wanda hakan zai ba su cikakkiyar damar tsara ayyukansu bisa ga ranakun da INEC ta ayyana.

Sai dai wasu ƴan siyasa sun dage cewa abin da suke yi tun kafin ranar fara kamfen ba yekuwar neman zaɓe ba ne, illa tuntuɓar al’umma, bayyana manufofi da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki, saboda haka ba su karya dokar zaɓe ba wanda matsayi ne da ke ci- gaba da haifar da muhawara tsakanin ƴan siyasa da masu sa ido kan harkokin zaɓe a ƙasar nan.

Fitar da sanarwar, ya nuna cewar da zarar lokaci ya yi an buɗe ƙofa ga jam’iyyun siyasa da ƴan siyasa domin fara yekuwar neman zaɓe a hukumance wanda ya haɗa da gangamin yaƙin neman zaɓe, tallace-tallace a kafafen yaɗa labarai, wayar da kan masu zaɓe da tarukan tattaunawa da al’umma.

Domin kiyaye doka Hukumar Zaɓe ta buƙaci dukkanin masu ruwa da tsaki da su bi sabon jadawalin da kuma tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026 domin kaucewa duk wata matsala tare da tabbatar da gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali, lumana, gaskiya, adalci da bin doka.

Sai dai wasu masu ruwa da tsaki sun bayyana cewar tun kafin lokacin da doka ta amince da fara yakewar neman zaɓen 2027, alamu sun nuna jam’iyyu da dama sun riga sun fara kamfen a sassa da dama a Nijeriya, lamarin da ya ci karo da tanade-tanaden Dokar Zaɓe.

Tuni manyan jam’iyyun siyasa suka fara neman goyon bayan jama’a ta ƙarƙashin ƙasa domin samun amincewa da cikakken goyon su gabanin lokacin da doka ta ƙayyade fara yekuwar neman zaɓe.

A kan wannan ƴan siyasa da dama na amfani da giɓin da ke cikin dokar wajen gudanar da abin da ake kallo a matsayin kamfen na ƙarƙashin ƙasa ta hanyar amfani da wasu sunaye, taruka ko ayyuka daban-daban ba tare da fuskantar hukunci ba.

Lamarin ya fi ɗaukar hankali a yankin Kudu- maso- Yamma inda fafatawar siyasa ta ƙara zafi bayan fitowar manyan masu neman kujerar Shugaban Ƙasa uku daga yankin, wato Shugaba Bola Tinubu na jam’iyyar APC, Gwamna Seyi Makinde na jam’iyyar APM da Adewole Adebayo na jam’iyyar SDP.

Yawaitar ayyana goyon baya ga waɗannan ƴan siyasa ta jawo suka daga ƙungiyoyin fararen hula waɗanda suka buƙaci Hukumar Zaɓe da ta tabbatar da aiwatar da Dokar Zaɓe. A cewarsu aiwatar da gangamin tattara magoya baya da bayyana goyon baya a bainar jama’a sun yi kama da yaƙin neman zaɓe kafin lokacin da doka ta amince.

Sai dai magoya bayan Shugaba Tinubu sun musanta zargin, suna cewa abin da suke yi ba kamfen ba ne, illa bayyana gamsuwarsu da nasarorin gwamnatin da kuma nuna goyon baya ga manufofinta.

Sai dai kuma masana sun koka da cewar, duk da irin waɗannan koke-koke, INEC ba ta da cikakken ikon hukunta ƴan siyasa ko jam’iyyun da ke fara kamfen kafin wa’adin doka, sakamakon giɓin da ke cikin Dokar Zaɓe da kuma ƙarancin ikon aiwatar da hukunci da aka ba hukumar.

Ko da yake Sashe na 98 (1) na Dokar Zaɓe ta 2026 ya haramta fara yaƙin neman zaɓe kafin kwanaki 150 zuwa ranar zaɓe, dokar ba ta tanadi wani taƙamaiman hukunci ko tara ga waɗanda suka karya wannan tanadi ba.

A maimakon haka, dokar ta tanadi hukunci ne kawai ga duk wanda ya ci- gaba da kamfen cikin sa’o’i 24 kafin ranar zaɓe, inda aka tanadi tarar da ta kai naira miliyan biyu amma ba ta fayyace hukuncin kan waɗanda suka fara kamfen watanni ko shekaru kafin lokacin da doka ta amince ba.

LEADERSHIP HAUSA ta ruwaito cewar a sassa daban-daban na ƙasar nan daga Arewa zuwa Kudu, ƴan siyasa na amfani da bukukuwan al’adu, tarukan addini, allunan talla da kuma kafafen sada zumunta wajen gudanar da abin da ake zargin kamfen ne a ɓoye kamar yadda masu ruwa da tsaki suka bayyana.

Sai dai ƴan siyasa da dama na kare kansu da cewa gangamin da suke yi ba kamfen ba ne, illa bayyana ra’ayi, tuntuɓar al’umma da kuma gudanar da harkokin siyasa na yau da kullum, don haka ba su karya doka ba.

A cewar masana ci- gaba da irin wannan gangamin da ba sh da cikakken tsari da goyon bayan doka na ƙara tsadar gudanar da zaɓe tare da karkatar da hankalin gwamnati daga gudanar da mulki zuwa fara kamfen gabanin kaɗa gangar siyasa.A kan wannan masu ruwa da tsaki a harkokin zaɓe, ciki har da tsofaffin shugabannin INEC, sun sha yin kira ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta yi gyaran fuska ga dokar zaɓe domin kafa Hukumar Kula da Jam’iyyun Siyasa mai cikakken ikon hukunta duk wanda ya karya dokokin yaƙin neman zaɓe, musamman waɗanda ke fara kamfen kafin lokacin da doka ta tanade.

Masana harkokin zaɓe sun bayyana cewa sabon jadawalin da Hukuma Zaɓe ta fitar zai baiwa jam’iyyun siyasa da ƴan takara isasshen lokacin gudanar da yekuwar neman zaɓe cikin tsarin da doka ta tanada, tare da kawar da cece-kucen da ya biyo bayan jadawalin farko. A cewarsu sauyin ya nuna yadda hukumar ke iya daidaita shirye-shiryenta idan buƙatar hakan ta kama.

Sai dai wasu masana sun yi gargaɗin cewa sauya jadawalin kaɗai ba zai wadatar ba idan ba a magance matsalar kamfen kafin lokacin da doka ta tanada ba. A cewarsu, tuni wasu ƴan siyasa suka fara gangamin neman goyon baya ta hanyar taruka, allunan talla da kafafen sada zumunta, alhali Dokar Zaɓe ta tanadi taƙamaiman lokacin fara kamfen.

Haka ma ƙungiyoyin fararen hula da ke sa ido kan zaɓe sun yi kira ga INEC da hukumomin tsaro su tabbatar da cewa dukkan jam’iyyu sun bi sabon jadawalin ba tare da nuna bambanci ba. A ra’ayin su, rashin ɗaukar mataki kan masu fara kamfen da wuri na iya haifar da rashin adalci tsakanin ƴan takara.

Sai dai masu sa ido kan harkokin zaɓe a Nijeriya da ƙungiyoyin fararen hula sun bayyana cewar Hukumar Zaɓe ba ta da iko a kundin tsarin mulki na hana ɗan takara ko jam’iyya shiga zaɓe saboda fara kamfen kafin lokaci.

Wannan mataki na INEC ya zo ne kimanin watanni huɗu bayan da hukumar ta fitar da jadawalin zaɓen farko, wanda ya jawo muhawara da suka daga sassa daban-daban na ƙasar saboda ranakun da aka tsara gudanar da zaɓen sun yi daidai da watan azumin Ramadana na shekarar 2027.

Sakamakon ce-ce-ku-cen da jadawalin ya haifar, Majalisar Dokokin Ƙasa ta duba tanade-tanaden dokar zaɓe tare da yin gyara kan mafi ƙarancin wa’adin da ya kamata hukumar zaɓe ta sanar da ranar gudanar da babban zaɓe.

A jadawalin farko da INEC ta sanar, an ware ranar 20 ga Fabrairu, 2027 domin gudanar da zaɓen Shugaban Ƙasa da na ƴan Majalisar Dokoki ta Ƙasa, yayin da aka sanya ranar 6 ga Maris, 2027 domin zaɓen Gwamnoni da na Ƴan Majalisun Dokokin Jihohi.Sai dai sabon jadawalin da hukumar ta fitar ya sauya waɗannan ranaku, matakin da ake ganin an ɗauka ne domin kaucewa matsalolin da suka taso kan yiwuwar cin karo da watan Ramadana da kuma tabbatar da gudanar da zaɓe cikin yanayi mai sauƙi ga masu kaɗa ƙuri’a da sauran masu ruwa da tsaki.

Siyasa
Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
+ posts Bio
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    2027:Cece-kuce Ta Barke Tsakanin Tinubu Da Atiku
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Yadda Rikici Ya Tsananta Tsakanin Dan Daba Da Malaman Addini A Sakkwato
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Dalilin Yawaitar Haduran Kwale-kwale A Yankin Sakkwato
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Atiku Ya Koka Kan Ƙaruwar Ta’addanci A Sakkwato
Siyasa
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Siyasa
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Siyasa

Shugaban Pi-CNG Ya Nemi Zuba Jari Domin Haɓaka Sufuri

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.