ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugaban Pi-CNG Ya Nemi Zuba Jari Domin Haɓaka Sufuri

by Abubakar Sulaiman
1 month ago

Babban Darakta Gudanarwa na Shirin gwamnatin tarayya kan Iskar Gas ta CNG da Motocin Wutar Lantarki (Pi-CNG & EV), Ismaeel Ahmed, ya jaddada cewa ɗorewar haɗin kai da zuba jari su ne ƙashin bayan cimma muradin Nijeriya na komawa amfani da hanyoyin sufuri masu tsafta. Ya bayyana hakan ne ta bakin Babban Jami’in Bin Dokoki na tsarin, Zayyanu Tamberi, a yayin Taron Masana’antar Ƙera Motoci na Nijeriya karo na 3 (3rd Nigeria Auto Industry Summit) da aka gudanar ranar Alhamis, 30 ga Yuli, 2026 a jihar Lagos.

Taron, wanda Ƙungiyar Manema Labaran Masana’antar Motoci (NAJA) tare da Haɗin Gwuiwar Hukumar Haɓaka Ƙera Motoci ta Ƙasa (NADDC) suka shirya, ya mai da hankali ne kan hanyar Nijeriya ta komawa amfani da wutar lantarki da CNG a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Malam Ahmed ya bayyana cewa wannan shiri na shugaban ƙasa yana ɗaukar matakai masu mahimmanci wajen haɓaka adadin cibiyoyin sauya tsarin motoci zuwa CNG, da faɗaɗa tashoshin mai na iskar gas, da haɓaka motocin wutar lantarki, da gina koyar da ma’aikata. Ya ƙara da cewa a cikin shekaru biyu da suka gabata, shirin ya samu nasarori wajen horar da dubban ma’aikatan sauya wa zuwa tsarin, da kuma ƙaddamar da tsarin sa ido na ‘Nigeria Gas Vehicle Monitoring System’ domin tabbatar da tsaro da kiyaye ƙa’idoji.

ADVERTISEMENT

Sai dai ya bayyana ƙarancin kayan aiki, da ƙarancin tsarin tallafin kuɗi ga masu saya, da raunin masana’antun gida a matsayin ƙalubalen da ke buƙatar haɗin gwiwar dukkan masu ruwa da tsaki.

Haka zalika, ya yabawa kafafen labarai a matsayin abokan tarayya masu muhimmanci a wannan tafiya, inda ya buƙaci mambobin ƙungiyar NAJA da su riƙa wallafa ingantattun labarai domin wayar da kan jama’a, ƙalubalantar labaran ƙarya, da jawo hankalin masu zuba jari. Ahmed ya jaddada aniyar shirin na rage kuɗaɗen sufuri ga ‘yan Nijeriya, da ƙirƙirar damar samar da ayyuka, da tabbatar da tsaron makamashi, da kuma samar da kyakkyawar rayuwa ta hanyar haɗin gwiwa mai ƙarfi da sanya jari a ɓangaren sufuri mai tsafta.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

A nasa ɓangaren, Darakta Janar na Hukumar NADDC, Joseph Osanipin, wanda Darakta mai kula da Yaɗa Labarai na hukumar, Susan Bisong-Taiwo ta wakilta, ya yi kira ga masu zuba jari da su faɗaɗa zuba jarinsu a gidajen mai na CNG da sansanonin caji motocin lantarki.

Osanipin ya bayyana cewa ko da yake Nijeriya tana da cibiyoyin sauya tsarin motoci zuwa CNG guda 345 da aka amince da su a faɗin ƙasar, ana buƙatar ƙarin zuba jari daga ɓangaren masu zaman kansu domin rage dogayen layuka a gidajen mai da kuma sauƙaƙa amfani da motocin wutar lantarki a tafiye-tafiye masu nisa.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Mazauna Yankin Sun Tsere Bayan Gano Wasiƙar Kawo Hare-haren Ta’addanci a FCT

Ƴan Bindiga Sun Farmaki Jami’an INEC Tare Da Sace Kayayyakin Zaɓe A Jihar Osun

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.