ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya Sun Shiga Rudani A Yayin Da Wa’adin Mika Sunayen Mambobi Ya Shude

by Yusuf Shuaibu
4 months ago
Adawa

Jam’iyyun siyasa a Nijeriya sun shiga rudani a yayin da wa’adin mika jerin sunayen mambobin jam’iyyun ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ya kare.

Wa’adin ranar karshe ga jam’iyyun siyasa don mika rajistar mambobinsu ga hukumar zabe ta kare da tsakar daren ranar 10 ga watan Mayu.

Jam’iyyar APC da jam’iyyar ADC da jam’iyyar NDC na iya fafatawa da ‘yan takarar shugaban kasa iri daya da na zaben 2023, amma a jam’iyyu daban-daban.

ADVERTISEMENT

A zaben shugaban kasa na 2023, ya kasance fafatawa ne tsakanin mutane uku, inda shugaba Bola Tinubu ya kasance dan takarar APC, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP da kuma tsohon gwamnan Jihar Anambra, Mista Peter Obi a matsayin dan takarar jam’iyyar LP.

Bayan shekaru hudu, PDP da LP na daga cikin manyan jam’iyyun adawa guda uku a 2023, duka sun shiga cikin rikice-rikicen wanda ya janyo har sai da manyan mutane a cikinsu sun tilasta musu barin jam’iyyun. Atiku ya koma ADC yayin da Obi ya koma NDC.

LABARAI MASU NASABA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

Obi ya bayyana a bainar jama’a cewa dole ne ya kasance a kan takardar zabe a shekarar 2027, kuma ya kara nuna aniyyarsa ta yin wa’adi guda idan an zabe shi a matsayin shugaban Nijeriya, tare da yanke shawarar NDC na kai mukamin shugaban kasa a yankin kudu, fitowarsa a matsayin dan takarar shugaban kasa na NDC ya kusan tabbata. A karkashin wannan tsarin, NDC ta ce za a juya tikitin zuwa arewa a shekarar 2031, kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, wanda ake tsammanin zai zama mataimakin Obi, ya amince da hakan.

‘Yan takara guda uku sun nuna sha’awar takara a zaben shugaban kasa a karkashin jam’iyyar ADC kuma su ne Atiku, tsohon ministan sufuri, Chibuike Amaechi da Mohamed Hayatu-Deen kuma jam’iyyar ba ta fayyace ko za ta bi tsarin karba-karba wajen raba tikitinta ba.

Ga PDP, yiwuwar tsohuwar jam’iyyar gwamnati wadda rikici mai tsawo na shugabanci ya raba ta gida biyu wajen fitar da dan takarar shugaban kasa, ya bayyana a matsayin abin shakka yayin da wa’adin da jam’iyyun ke da shi don mika jerin mambobinsu ga hukumar zabe ya wuce a ranar 10 ga Mayu.

PDP ta rabu kashi biyu. Daya na karkashin kulawar ministan Babban Birnin Tarayya Abuja kuma tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, yayin da daya bangaren ke karkashin kulawar Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde. Dukkanin bangarorin biyu suna cikin dogon rikici kan wanda ke wakiltar sahihin shugabancin kasa na jam’iyyar.

A cikin hukuncin kotun koli na baya-bayan nan, hukuncin ya nuna cewa kotu ta tabbatar da dakatar da abokin Wike, Sam Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar na kasa, amma har yanzu shafin yanar gizo na hukumar INEC na nuna cewa, Abdul Rahman Mohamed a matsayin shugaban jam’iyyar da Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar PDP. Dukkanin wadannan mutane suna cikin bangaren Wike, kuma ci gaba da kasancewarsu a shafin INEC na nuni da cewa hukumar zabe ba ta aiwatar da wani umarnin kotu da zai iya canza shugabancin da aka amince da shi a jam’iyyar ba.

Matakin INEC na ci gaba da sanya abokan Wike a matsayin shugaban jam’iyyar da sakatare, yana da bambanci da gaggawar cire sunan tsohon shugaban majalisar dattawa, Dabid Mark da tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola a matsayin shugaban da sakataren jam’iyyar ADC.

Lokacin da kotun koli ta yanke hukunci cewa shugabancin ADC ya kamata ya koma yadda yake a baya, INEC ta dauki mataki cikin sauri ta fassara hukuncin a matsayin cewa an dawo da Mark da Aregbesola. Duka shugabannin an dawo da sunayansu daga shafin yanar gizon INEC.

Wata majiya daga PDP ya shaida cewa INEC ba ta yi wani canji a shugabancin jam’iyyar duk da hukuncin kotun koli, wanda ana fassara shi a matsayin cewa hukumar na jiran karin bayani.

Siyasa
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
Tambarin Dimokuradiyya

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

September 5, 2026
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

September 4, 2026
Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?
Tambarin Dimokuradiyya

INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027

August 28, 2026
Next Post
Masanin Angola: Manufar Soke Harajin Kwastam Za Ta Bude Sabon Babi Na Raya Dangantakar Sin Da Afirka

An Samu Karuwar Hada-hadar Jiragen Ruwa A Zangon Farko Na 2026 —Shugaban NPA

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.