ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Samu Karuwar Hada-hadar Jiragen Ruwa A Zangon Farko Na 2026 —Shugaban NPA

by Abubakar Abba
2 months ago
NPA

A zango na farko na shekarar 2026, fannin sufurin Jiragen Ruwa na kasar nan, ya fara da kafar dama, musamman duba da yadda aka samu zirga-zirgar Jiragen Ruwa da suka karu zuwa  jimlar, metric tan miliyan 32.38, tare da kuma samun karuwar kaso,  67 na hada-hadar shigo da ababen hawa.

A cikin rahoton nazari, na kokarin da aka samu a hukumar a zango na daya na 2026 wanda NPA ta fitar ya nuna cewa, hada-hadar shiga da fitar da kaya daga Tashoshin Jiragen Ruwan kasar, cikin kayan ban da Danyen Mai, sun karu zuwa jimlar kaso 11.6 daga kaso metric tan miliyan 29.02.

Kazalika, rahoton ya nuna cewa, an samu karuwa a tsarin yiwa Jiragen Ruwa rijista wato GRT, wanda ya daga kai kaso 19.5 zuwa kaso niliyan  46.75.

ADVERTISEMENT

A cewar NPA sauye-sauyen da a aka ci gaba da samar wa da kuma karin bukatar da ake da ita a bangren shige da ficen Jiragen Ruwa na kasashen waje zuwa cikin kasar da kuma aikin kananan Tashoshin Jiragen Ruwa na Lekki, sun kara taimaka wa, wajen samun wadannan nasarorin.

Bugu da kari, ci gaba da namjin kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na sayen kayan aiki na zamani a Tashoshin Jiragen Ruwan kasar, hakan ya kara daga darajar kasar nan a hada-hadar kasuwanci na Afirka.

LABARAI MASU NASABA

Ɗantsoho Ya Jinjina Wa Hukumar FCC Kan Sabbin Sauye-Sauyen Da Ta Samar

Rage Farashin Mai Na Ɗangote: Dillalan Man Fetur Sun Yi Burus Da Sauya Nasu Farashin

A kwanan  baya, an ruwaito Shugaban Hukumar NPA Abubakar Dantsoho ya bayyana cewa, ya zama wajibi, Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar su ci gaba da gudanar da gasa, a harkar sufurin Jiragen Ruwa a nahiyar Afirka.

Dantsoho ya bayyana haka ne a wani taro kungiyar masu masana’antu, da aka gudanar a jihar Legas.

“Irin tsarin da muka samar a fannin sufurin Jiragen Ruwa na kasar nan, hakan na ci gaba da taimaka wa matuka, wajen kara habaka fannin tattalin arzikin kasar,” Inji Dantsoho.

Kazalika, rahoton ya nuna cewa, an samu karin da ya kai daga kaso 23.7 zuwa kaso 14.13 na   metric tan miliyan na hinTa-hadar kasuwanci na yanki.

Kazalika, hada-hadar shige da ficen Jiragen da suna yo jigilar kwantaina, ya karu daga kaso zuwa 67.6 zuwa kaso 102,803.

Hakazalika, an kuma samu nasara wajen shigo da ababen hawa, inda suka karu daga kaso 67 zuwa kaso 58,870, musamman idan aka kwatanta da wanda aka samu a bara, da suka kai kaso 35,262 .

Sauye-sauyen da a kirkiro da su a karkashin gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, musamman na zamantakewar da Tashoshin Jiragen Ruwan kasar hakan ya kara taimaka wa fannin.

Manyan sauye-sauyen su ne na aikin sabunta ginin Tashoshin Jiragen Ruwa na Legas da na Tin Can Island, musamman bayan amincewa tare da kuma sanya hannun yarjejeniyar ta dala biliyan daya.

Ministan Bunkasa Fannin Tattalin Arziki na Teku Adegboyega Oyetola ya bayyana cewa,  ana kan shirye-shiyen sayo wasu kayan aiki domin a daga darajar Tashoshin Jiragen Ruwa na Warri da ta, Onne da kuma ta Kalaba.

Samar da tsare-tsaren kara daga daraja da kuma kimar kayan aiki a Tashoshin Jiragen Ruwan kasar, wadanda suka kasance na zamani ta hanyar amfani da NSW da kuma PCS, sun kara taimaka wa wajen magance jinkiri da kuma kara tabbatar da ana bin ka’ida.

 Masu ruwa da tsaki a fannin masana’antu, suma ba a bar su a baya ba, wajen bayyana yakinin su na cewa, nasarorin da aka samu, sun kara taimaka wa, wajen samar da saukin hada-hadar kasuwanci a Tashoshin Jiragen Ruwan kasar.

Bugu da kari, gwamnatin tarayya ta kara fadada fannin zuba jari a Tashoshin kan tudu wanda hakan ya sanya fannin, ke ci gaba da habaka tare da kuma rage yawan yadda a baya, ake samun cunkoso Jiragen Ruwa a Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar.

Hakazalika, karfafa tsaro da aka yi a hanyoyin Ruwan kasar hakan ya kara tabbatar da kwarin guwai, ga fannin.

Babbar hujja kan wannan batun shi ne, ganin yadda yau Nijeriya ta shafe shekaru hudu, ba samu masu fashin Teku ba.

Sai dai, duk da irin wannan dimbin nasarorin da aka samu a fannin, shugaban hukumar ta NPA, har yanzu, akwai sauran aiki, da ya kai kaso 25 na cunkoson Jiragen Ruwa da ake ci gaba da fuskanta a Afirka ta Yamma.

Ya kara da cewa, duk da wadannan nasarorin, da suka kai na sama da kaso 60 na tattalin arzikin yankin, ya zama wajibi Nijeriya ta ci gaba da samar da sauye-sauyen da kara habaka fannin sufurin Jiragen Ruwan kasar.

NPA
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari A Kan Wasu Cututtuka Da Ke Shafar Dabbobi Lokacin Damina
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Ɗantsoho Ya Jinjina Wa Hukumar FCC Kan Sabbin Sauye-Sauyen Da Ta Samar
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    “Mutunta Ƴancin Addinai Ita Ce Hanyar Wanzar Da Zaman Lafiya A Kaduna”

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Tattalin Arziki

Ɗantsoho Ya Jinjina Wa Hukumar FCC Kan Sabbin Sauye-Sauyen Da Ta Samar

July 11, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN
Tattalin Arziki

Rage Farashin Mai Na Ɗangote: Dillalan Man Fetur Sun Yi Burus Da Sauya Nasu Farashin

June 27, 2026
Gwamnatin Tarayya, Bankin Duniya Da Cibiyar IITA Za Su Bunkasa Noma Ta Fasahar Zamani
Tattalin Arziki

Bankin Duniya Ya Ɗora Tashoshin Apapa Da Tincan Kan Sikelin Maki Na 20 A Duniya

June 26, 2026
Next Post
Yadda Na Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU Cikin Kwana Daya – Jonathan

Kotu Za Ta Saurari Ƙarar Da Ke Ƙalubalantar Cancantar Tsayawar Jonathan Takarar Shugaban Ƙasa A 2027

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

July 15, 2026
Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

‘Yansanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kano

July 15, 2026
Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.