A cewar taron tattaunawa game da harkokin kwastam, da kasuwanci na kungiyar APEC na shekarar 2026, jimilar darajar hada-hadar shige da fice ta Sin da sauran membobin APEC ta kai yuan tiriliyan 18.03 a watanni bakwai na farkon bana, adadin da ya karu da kashi 21% bisa makamancin lokaci na bara.
A halin yanzu, jimilar darajar tattalin arzikin yankin Asiya da Pasifik ya kai fiye da kashi 60% na duniya, kuma yawan cinikinsa ya kai kusa da rabin jimillar na duniya baki daya.
A cikin watanni bakwai na farkon wannan shekara, saurin karuwar shige da fice na Sin da sauran membobin APEC ya zarta saurin karuwar cinikin kayayyaki na Sin baki daya cikin wannan wa’adi, wanda hakan ke nuna babbar dama da aka samu a bangaren hadin gwiwar tattalin arziki a yankin. (Safiyah Ma)














