Zamani a yanzu ya zo da canje-canje musamman yadda kasarmu ke yin tafiyar hawainiya ta fuskar tattalin arziki, hakan ya sanya a halin yanzu sana’o’i ana tafiya kafada da kafada tsakanin maza da mata.
KHADIJA ABBDULLAHI matashiya ce wacce ta shawarci mata kan su kama sana’a domin dogaro da kansu domin biya wa kansu bukata a wannan zamani da kowa ta kansa yake yi. Khadija ta bayyana hakan ne a tattaunawarsu da wakiliyarmu BILKISU TIJJANI ALKASSIM. Ga dai yadda hirar ta kasance:
Da fari za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki…
Suna na Khadija Abdullahi Muhammad iyaye na haifaffiyar Hadeja ce Jihar Jigawa, ni an haife ni a Garin Kano na yi makaranta a Kano wannan shi ne takaitaccan tarihina.
Shin Khadija matar aure ce?
A’a ni ba matar aure bace, amma dai ana niyya in sha Allahu.
Malama Khadija ‘yar kasuwa ce ko kuma ma’aikaciya ce?
Eh to ina taba kasuwanci dai kadan-kadan saboda yanzu sai a hankali wallahi mutane ba kudi a hannunsu ana dai kasuwancin Alhamdu lillah.
Wanne irin kasuwanci kike yi?
Ina saida atamfofi da leshi da kayan kicin da takalma da jakankuna.
Me yaja hankalinki har kika shiga wannan kasuwancin?
Eh to abin da ya ja hankalina har na shiga wannan kasuwancin ni mutum ce mai son na ganni da kudi a hannuna ba na son zama babu kudi ko ban kashe ba ni dai na gan su ina jin dadi.
Mene ne matakin karatunki?
Ina da (NCE).
Wanne irin kalubale kika taba fuskanta a cikin sana’arki?
Akwai kalubale kala-kala ta wajan idan mutum ya sayi kaya ko ya ce zai turo kudi ka bashi kaya daga baya kuma kudi ya zo ya zama bai fito ba, to wannan duk suna daya daga cikin irin kalubale da muke fuskanta.
Zuwa yanzu wadan ne irin nasarori kika cimma?
Alhamdu lillah mun cimma nasarori daban-daban ka kalli kanka ka ga ka fi karfin bukatunka ma wannan babbar nasara ce Alhamdu lillah.
Wanne abu ne ya fi faranta miki rai game da sana’arki?
Idan na duba na ga na fi karfin bukatuna har zan iya taimakawa wani to Alhamdu lillah ina jin dadi.
Ta wacce hanya kike bi wajen tallata sana’arki?
Ta kafofin sada zumunta wato social media Facebook, Instagram, Whatsapp
Da me kike so mutane su rika tunawa da ke?
Ta halaye masu kyau.
Ga karatu, ga kuma hidimomin sana’a, shin ta yaya kike samun damar gudanar da hutunki?
Eh to gaskiya lokacin da na fara sana’a na kammala karatu na gaskiya ban samu wani kalubale ba ta wannan fannin ban hada karatu da sana’a ba sai da na gama karatu na fara sana’a.
Wace irin addu’a ce idan aka yi miki kike jin dadi?
Ina so na ji an yi min addu’ar fatan alkhairi ina jin dadi sosai.
Wanne irin goyon baya kike samu daga wajen iyaye da ‘yan uwanki?
Na samu goyon baya dari bisa dari gaskiya babu abin da za mu ce daidai Alhamdu lillah.
Kawaye fa?
Gaskiya na samu goyon bayan kawaye na sosai suna taya ni tallata kayana kuma suma suna saya.
Me kika fi so cikin kayan sawa da kayan kwalliya?
Ni gaskiya kwalliya ba ta dame ni ba, kayan sawa ina son abaya da duguwar rigar atamfa su ne kayan da na fi sawa.
A karshe wanne irin shawara za ki ba ‘yan uwanki mata?
Shawarar da zan ba wa ‘yan uwana mata ita ce a rike sana’a, dogaro da kai, Allah ya rufa mana asiri baki daya na gode.