ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zaɓen Fidda Gwani Na Gwamna: Ba Za Mu Lamunci Kaƙaba Mana Ɗan Takara A Bauchi Ba – Mambobin APC

by Khalid Idris Doya and Sulaiman
4 months ago
Bauchi

Wasu magoya bayan jam’iyyar APC a jihar Bauchi sun ce ba za su taɓa lamuncewa da dukkanin wani yunƙuri na ƙaƙaba ɗan takara gabanin gwamna na jam’iyyar ba, inda suka ƙafe kai da fata kan cewa dole ne a gudanar da sahihin zaɓe fidda gwanin gwamnan cikin gaskiya da adalci.

Da ya ke magana a ranar Alhamis yayin da suka ziyarci otal ɗin da ake tunanin mambobin kwamitin zaɓen jam’iyyar suka sauƙa domin neman ƙarin haske kan yadda za a gudanar da zaɓen fidda gwanin zai gudana, wani jigo a APC, Musa Buba Mohammed wanda aka fi sani da “Civilian General,” ya ce mambobin jam’iyyar ba za su amince da duk wani yunƙuri daga wasu tsirarun mutane na musu ɗauki-ɗoran ɗan takara maimakon bai wa dimokuraɗiyya damar tafiya yadda ya kamata ba.

Ya jaddada cewa dimokuraɗiyya dole ne ta wakilci muradin mafi rinjayen mambobin jam’iyya, ba wai buƙatun wasu tsirarun mutane kaɗai ba.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, babban abin da magoya bayan APC a Bauchi ke nema shi ne gudanar da sahihin zaɓen fidda gwani cikin gaskiya da adalci wanda zai samar da ɗan takarar da mambobin jam’iyyar da al’ummar jihar za su amince da shi har a samu nasara a 2027.

Musa ya bayyana cewa duk da cewa an ɗage zaɓen fidda gwanin daga ranar Alhamis zuwa Juma’a, har yanzu mambobin jam’iyyar na da kyakkyawan fata cewa za a gudanar da zaɓen cikin gaskiya, adalci da sahihanci, inda ya yi gargaɗi kan yin wani abu saɓanin hakan. Ya ce abin da magoya bayan jam’iyyar ke nema kawai shi ne adalci da gaskiya, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa ɗan takara Nura Manu Soro zai yi nasarar zama ɗan takarar jam’iyyar APC muddin aka gudanar da sahihi kuma zaɓe cikin gaskiya da adalci.Haka kuma ya yi kira ga shugabannin APC da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da su tabbatar an yi wa mambobin jam’iyyar a Bauchi adalci da gaskiya.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

A cewarsa, an sanar da magoya bayan jam’iyyar cewa an ɗage zaɓen fidda gwani a jihohin Bauchi da Kwara, lamarin da ya haifar da fargaba kan ingancin zaben da za a gudanar ɗin.”Abin da muke so shi ne sahihin zaɓe cikin lumana, gaskiya da adalci. Ba ma son kakabawa. Wannan shi ne kawai buƙatarmu,” in ji shi.

Jigon APC ɗin ya kuma yi tambaya kan dalilin ɗage zaɓen fidda gwani a Bauchi, yana mai cewa hakan ya ƙara haifar da damuwa a tsakanin magoya bayan jam’iyyar.

“Me ya sa aka ɗage zaɓen? Dole akwai wani dalili a bayan hakan. Sauran jihohi sun gudanar da nasu zaɓukan, amma Bauchi da Kwara aka ɗage. Shi ya sa mutane da dama ke fara zargin akwai wata manufa a ciki,” in ji shi.

Ya buƙaci shugabannin jam’iyyar da su mutunta ƙa’idojin dimokuraɗiyya, yana mai tuna cewa Shugaba Tinubu ya samu nasara ne ta hanyar sahihin zaɓe ba ta hanyar yarjejeniya ko kakabawa ba.

“Shugaban ƙasa ya yi nasara ne ta hanyar ƙuri’a, ba ta hanyar yarjejeniya ba. Wannan irin tsarin dimokuraɗiyyar ne muke nema a nan Bauchi,” in ji shi.

Shi ma da yake magana, Kwamared Abdul’Aziz Nasrullah ya ce Jihar Bauchi na buƙatar sahihan ‘yan takara waɗanda za su wakilci muradun al’umma da gaske da adalci, ba waɗanda ake zargin wasu masu ƙarfin fada a ji suna ƙoƙarin kakaba su domin biyan buƙatun kansu ba.

Ya sake jaddada ƙudirin magoya bayan APC na tabbatar da adalci, gaskiya da sahihanci a tsarin zaɓen fidda gwani na gwamna a Jihar Bauchi.

Bauchi
Khalid Idris Doya
+ posts Bio
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Yaro Ya Harbe Kansa Har Lahira Bayan Mafarauci Ya Yi Sakaci Da Bindigarsa A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    An Kama Mutane 5 Da Sassan Jikin Ɗan’Adam Za Su Yi Tsafi A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Tsohon Mai Neman Takarar Gwamnan Bauchi, Bala Jibrin, Ya Fice Daga APC Kan Zargin Ɗoki-ɗora
Bauchi
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

MASU ALAKA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Bauchi
Siyasa

Muna Da Yan Takarar Gwamna A Jihohi 28 Don Shiga Zaben 2027

September 6, 2026
Next Post
Sin Za Ta Gudanar Da Babban Taron Kwamitin Sulhun MDD A Ranar 26 Ga Watan Mayu

Sin Za Ta Gudanar Da Babban Taron Kwamitin Sulhun MDD A Ranar 26 Ga Watan Mayu

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.