ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ko Kin San…Maganin Wanke Dattin Ciki Da Mara Na Maza Da Mata?

by Bilkisu Tijjani and Sulaiman
7 months ago
Ciwon ciki

Ta hanyar amfani da abubuwa guda 10 ga su kamar haka:

A nemi wadannan abubuwa da zan Lissafo su guda 10 wadanda duka ba za su yi wahalar samowa ba ga su kamar Haka:

1. Asamu asalin Ganyen Zaitun a daka shi ya dawo gari sosai, a kalla ana son cikin babban cokali uku 2. Tsohuwar Tsamiya ba danyar ba, in an ce tsohuwar tsamiya ita ce wacce za ka ga ta yi Brown ko ja kuma tana da danko sosai ita ce tsohuwar tsamiya guda bakwai 3. Jan Gauta wanda ya bushe kuma wanda bai Dagargaje ba guda 7 4. Lemon tsami guda 7 shi ma mai kyau ba busashshe ba.

ADVERTISEMENT

5. Garin Sanamaki/Fulasko ana samunsa a shagon sai da magani na Islamic, A kalla ya kai kimanin cokali uku 3 babba.

6. Tafarnuwa mekyau kwallo uku, kuma a bare busashshen bawonta a yayyanka ta kanana-kanana. 7. Albasa fara babba mai kyau guda daya babba

LABARAI MASU NASABA

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

7. Dabino Mai kyau a kalla guda 20 a bare su a cire kwallon, a kuma cire dattin ciki har wannan Leda-ledar farin a cire shi. 9. Ganyen Zogale busashshe, kuma garin a kalla ya kai cikin cokali uku babba. 10. Zobo, Zobo dai da aka sani wanda ake jikawa ya yi ja a sa sukari a sha shi nake nufi, a daka garinsa shima a kalla ya kai cikin babban cokalin uku

Sai a nemi ruwa mai kyau a kalla ya kai kimanin Litre biyu, ko uku, Sai a juye wadannan abubuwan da aka lissafo guda 10 din a cikin wani abu mai dan girma wanda zai dauke su, sai a barshi sai ya kwana tukunna a ciki sannan sai a juye a tukunya a dafa su, su tafasa sai a tace a zuba shi a cikin wani abu mai kyau wanda ba zai lalata shi ba, sai a dinga sha bayan an ci abinci kullum sau biyu a yini

Ana son in aka ci abinci aka sha a tsaye sai a zauna a bubbude kafafuwa a saki jiki ana Numfashi ta yadda mara da ciki za su sakata su wala maganin ya ratsa su sosai tsawon mintuna goma sai a ci gaba da harkokin da aka saba, da yamma ma a kara yin haka, in ana Azumi ne kuma ana sha lokacin Sahur da lokacin buda baki ana daukar kwana bakwai ne a cikin kowanne wata ana yi.

In sha Allahu dukkan Dattin dake cikin Mara ko ciki ko tsutsar ciki, wannan Maganin zai wanko su gabadaya, zai dinga Pitar da su, sai dai idan Mutum yana da Olsa ana son in ya sha sai ya kara da ruwan sanyi in sha Allahu Olsa din ba za ta tashi ba.

Wannan maganin ba iya dattin ciki da mara kadai yake magancewa ba, yana wanko har dattin da kan zama barazana ga huhu ko hanta ko koda, sannan yana wanko mahaifa ga mata kuma yana wanke jijiyoyi, mace me ciki za ta iya amfani da shi matsala in sha Allahu, kuma ana iya ba wa yara kanana amma yadda za su sha daidai yadda zai dauki cikinsu ne, ya danganta da shekaru ko girman yaron, mata za su fi ni fahimtar me nake nufi a nan,

Idan namiji ko mace babba ko zai sha cikin karamin kofi to wanda bai girma ba in dai yana iya cin abinci zai sha rabin karamin kofi kenan, amma in yaro bai fara cin abinci ba, ba a bashi, domin ana sha ne bayan an ci abinci an koshi. Allah ya sa mu dace.

Ciki
Bilkisu Tijjani
+ posts Bio
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Tuwon Alkama Da Miyar Taushe
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa
Ciki
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

MASU ALAKA

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)
Uwargida Sarautar Mata

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)

July 5, 2026
Ciki
Uwargida Sarautar Mata

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

June 27, 2026
Wasu Abubuwa Da Ke Sa Maza Hana Mata Fita Unguwa (Uwargida)
Uwargida Sarautar Mata

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

June 21, 2026
Next Post
Yaudara

Yawaitar Yaudara Tsakanin Masoya A Wannan Zamanin

LABARAI MASU NASABA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.