ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Laifukan Intanet: Kotun Abuja Ta Karɓi Rahoton DSS, Ta Ba Da Belin Wani Ɗan Gwagwarmaya

by Rabi'u Ali Indabawa
2 months ago

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa ɗan gwagwarmaya kuma mai sharhi a kafofin sada zumunta, Justice Chidiebere, wanda aka fi sani da Justice Crack, beli kan zargin aikata laifukan intanet.

Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta bayar da belin ne kan kuɗi Naira miliyan 5 tare da mutum ɗaya da zai tsaya masa da makamancin wannan adadi.

Kotun ta ce wanda zai tsaya masa dole ne ya kasance yana zaune a yankin da kotun ke da iko a kai tsawon aƙalla shekaru huɗu tare da tabbataccen adireshi, sannan ya gabatar da shaidar zama kamar yarjejeniyar haya ko takardar mallakar gida ga ma’ajiyar kotu.

ADVERTISEMENT

Mai shari’ar ta kuma bayyana cewa wanda zai tsaya masa dole ne ya kasance ma’aikacin gwamnatin tarayya mai mataki na 15 ko sama da haka, tare da shaidar albashin aƙalla watanni uku, wasiƙar tabbatarwa daga shugaban sashensa da kuma shaidar fansho.

Wani shaida ya bayyana wa kotu cewa wanda ake tuhuma ya bayar da bayaninsa da kansa a gaban lauyoyinsa.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan

Lalata Da Ƙaramar Yarinya: Kotu Ta Yanke Wa Tsoho Mai Shekara 75 Hukuncin Ɗaurin Shekara 10 A Ribas

A cewarsa, wasu sojoji ne suka aika wa wanda ake tuhuma hotuna, sannan ya yi bidiyo daga hotunan tare da wallafa su a kafofin sada zumunta ba tare da tabbatar da sahihancinsu daga hukumomin soja ba.

Ya kuma shaida wa kotu cewa masu bincike sun cire bayanai daga wayar wanda ake tuhuma, ciki har da bidiyoyin da ake zargin ya wallafa a intanet, tattaunawarsa da wasu sojoji, saƙonnin da ya yi da wanda ya kira “uban gidansa” kan zanga-zanga, da kuma bayanai daga shafukansa na sada zumunta.

Shaidar ya ƙara da cewa an fitar da takardar tabbatar da bin ƙa’ida kuma wani babban jami’i ya sanya wa hannu bayan kammala binciken fasaha.

A yayin zaman kotun, lauyan kariya, Sam Amadi, ya sanar da kotun cewa ba a ba su rahoton binciken da sauran takardun da masu gabatar da ƙara ke son gabatarwa ba.

Sai dai masu gabatar da ƙarar sun bayyana hakan a matsayin kuskure tare da bayar da haƙuri a gaban kotu.

Daga nan ne Mai shari’a Abdulmalik ta amince da rahoton binciken DSS a matsayin hujja ta Eɗhibit A.

Masu gabatar da ƙarar sun kuma gabatar da wayar iPhone da ake zargin an ƙwato daga hannun wanda ake tuhuma, da flash driɓe da aka ce na ɗauke da bidiyoyin da aka wallafa a kafofin sada zumunta, tattaunawar da aka cire daga wayar, da kuma takardar tabbatar da bin ƙa’ida.

Lauyoyin kariya sun ƙi amincewa da karɓar flash driɓe ɗin a matsayin hujja, suna masu cewa ba a bayyana abin da ke cikinsa ba kuma ba a kunna shi a gaban kotu ba.

An ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 25 ga Mayu domin ci gaba da shari’ar, yayin da har yanzu ba a sallami shaidar farko ta masu gabatar da ƙara ba.

Jaridar PUNCH Metro ta rawaito cewa sauraron neman belin ya tsaya a ranar 14 ga Mayu bayan saɓani ya ɓarke tsakanin lauyoyin wanda ake tuhuma kan wanda zai jagoranci tawagar kariya.

Saɓanin ya janyo janye wata tsohuwar buƙatar beli da aka gabatar a madadin ɗan gwagwarmayar, lamarin da ya tilasta wa kotun ɗage shari’ar zuwa ranar Litinin domin sauraron sabuwar buƙatar beli.

Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Wasu Fusatattun Mutane Sun Lakaɗa Wa Mutum Biyu Duka Har Lahira A Kaduna
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Mun Ɗauki Nauyin Karatun Masu Digiri Ta Hanyar Sayar Da Ƙosai Da Ƙuli-ƙuli —Wasu Ƴan Kasuwa
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Adadin Mutanen Da Tsananin Zafi Ya Kashe A Turai Ya Haura Dubu 1,300 —WHO
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Pakistan Ta Kashe Mutum 36 A Hare-haren Da Ta Kai Kan Iyakarta Da Afghanistan

MASU ALAKA

‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan
Manyan Labarai

‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan

July 15, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga
Manyan Labarai

Lalata Da Ƙaramar Yarinya: Kotu Ta Yanke Wa Tsoho Mai Shekara 75 Hukuncin Ɗaurin Shekara 10 A Ribas

July 15, 2026
‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi
Manyan Labarai

‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

July 15, 2026
Next Post
Laifukan Intanet: Kotun Abuja Ta Karɓi Rahoton DSS, Ta Ba Da Belin Wani Ɗan Gwagwarmaya

Ya Kamata Mawaƙa Su Guji Munafunci Da Hassada Su Rungumi Juna —Fati UK

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

July 15, 2026
Sabbin Ministoci

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

July 15, 2026
GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

July 15, 2026
Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

July 15, 2026
‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan

‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan

July 15, 2026
Majalisa Ta Ba da Tallafin ₦50m Ga Iyalan Malamai Da Jami’an Tsaro Da Aka Kashe A Aikin Ceto A Oyo

Majalisa Ta Ba da Tallafin ₦50m Ga Iyalan Malamai Da Jami’an Tsaro Da Aka Kashe A Aikin Ceto A Oyo

July 15, 2026
Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

July 15, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Lalata Da Ƙaramar Yarinya: Kotu Ta Yanke Wa Tsoho Mai Shekara 75 Hukuncin Ɗaurin Shekara 10 A Ribas

July 15, 2026
Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

July 15, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.