ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Layin Dogon Da Zai Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Wajen Zamanantar Da Kansu

by CGTN Hausa and Sulaiman
10 months ago
Layin dogo

Kwanan nan, an kaddamar da aikin farfado da layin dogo tsakanin Tanzaniya da Zambiya, matakin da zai samar da kuzari ga layin dogon.

Layin dogo dake tsakanin Tanzaniya da Zambiya yana da tsawon kilomita 1860, wanda ya tashi daga tashar ruwa ta Dar es Salaam da ke Tanzania, sa’an nan ya ratsa tudun Tanzania har zuwa Kapiri Mposhi da ke tsakiyar kasar Zambiya, wanda ya taimaka ga hada dimbin kasashe masu arzikin albarkatun kasa da sauran sassan duniya. Kasar Sin ce ta bayar da gudummawar gina wannan layin dogon a kimanin shekarun 1970, don mara baya ga kasashen Tanzania da Zambiya wadanda suka samu ‘yancin kansu daga Turawa ’yan mulkin mallaka, wajen tsayawa da kafafuwansu a fannin tattalin arziki. A shekarar 1976, aka fara aiki da layin dogon, wanda ya samar da wata hanyar zuwa teku ga Zambiya da sauran wasu kasashen shiyyar da ba su da iyaka da teku, ta yadda albarkatun kasashen za su zama karfin bunkasa tattalin arzikinsu, matakin da ya sa kasashen suka yi watsi da tarnakin da aka yi musu ta fannin tattalin arziki tare da samun ‘yanci na gaske. Don haka, tsohon shugaban kasar Zambiya, marigayi Kenneth David Kaunda ya bayyana layin dogon a matsayin “’yancin kan Zambia a karo na biyu”.

A cikin kimanin shekaru 50 da suka wuce, layin dogon ya taka rawar gani wurin bunkasa tattalin arziki da zaman al’umma na Tanzaniya da Zambiya da ma sauran kasashen shiyyar. Sai dai layin dogon yana kuma fuskantar matsalar lalacewa sakamakon dadewarsa da aiki. Don haka, ana matukar bukatar inganta layin dogon don ci gaba da bunkasa tattalin arziki da zaman al’ummar shiyyar. A sabili da haka ne, a gun taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka da ya gudana a watan Satumban bara, shugabannin kasashen Sin da Tanzaniya da Zambiya suka rattaba hannu a kan takardar fahimtar juna game da farfado da layin dogo tsakanin Tanzaniya da Zambiya, inda suka amince da dora nauyin aikin a wuyan kasar Sin. An ce, bayan inganta layin dogon, za a kai ga ninka karfin sa na zirga-zirga har sau 12, a yayin da tsawon lokacin zirga-zirga zai ragu da kimanin kaso 2/3, wanda hakan tabbas zai sa kaimi ga bunkasar tattalin arzikin sassan da layin dogon ya ratsa.

ADVERTISEMENT

A hakika, layin dogo tsakanin Tanzaniya da Zambiya wani misali ne na hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka a fannin raya ababen more rayuwa. Ta la’akari da layin dogon dake tsakanin Mombasa da Nairobi da wanda ke tsakanin Abuja da Kaduna, da tashar samar da wutar lantarki ta karfin iska da ke garin De Aar na kasar Afirka ta Kudu da tashar samar da lantarki ta karfin ruwa ta Zungeru da ke Nijeriya, da ma sauran ababen more rayuwa da ba sa lisaftuwa da kamfanonin kasar Sin suka gina, za mu gano cewa, a cikin ’yan shekarun baya, kasar Sin ta gina jerin layukan dogo da hanyoyi da tashoshin ruwa da tashoshin samar da lantarki da asibitoci a wurare daban daban na nahiyar Afirka, wadanda suka kyautata tushen bunkasuwar tattalin arzikin nahiyar, tare da sa kaimi ga bunkasuwar masana’antu da zamanantar da kasashen Afirka.

Amma me ya sa kasar Sin ke iyakacin kokari wajen taimakawa kasashen Afirka raya ababen more rayuwa? Lallai a ganina, hakan ya faru ne sakamakon dadadden zumuncin dake tsakaninsu, da burinsu na neman tabbatar da moriyar juna, da ma yadda kasar Sin ke rungumar manufar gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Bisa ga yadda ta cimma nasarori ta fuskar samun ci gaban tattalin arziki, kasar Sin tana sane da cewa, manyan ababen more rayuwa su ne tushen bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al’umma, don haka ta gabatar da dabarunta ga kasashen Afirka, don inganta tushen bunkasa masana’antu a kasashen, da ma kwarewarsu ta raya kansu.

A sa’i daya, Sin da kasashen Afirka suna amfanin juna bisa hadin gwiwarsu ta gina ababen more rayuwa. Kasashen Afirka suna da yawan matasa da albarkatun kasa da ma manyan kasuwanni, sai dai dole ne su kyautata ababen more rayuwa don fifikonsu a fannonin ya taka rawar da ta kamata. Kasar Sin a nata bangaren, tana da fifiko ta fannonin kera na’urori da gine-gine da ma tara kudade, wanda hakan ke iya tallafa wa kasashen Afirka, kuma a wani bangare, hakan na iya samar da sabbin kasuwanni ga kamfanonin kasar Sin, ta yadda sassan biyu za su iya samun ci gaba na bai daya.

Ban da haka, a yayin da ake fuskantar matsalar rashin daidaiton bunkasuwar kasashen duniya, kasar Sin tana kokarin hada gwiwa da kasashen Afirka wajen gina ababen more rayuwa, domin aiwatar da manufarta ta gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga dukkanin bil Adam, sabo da farfadowar nahiyar Afirka ba alhairan da za su shafi al’ummar nahiyar kawai za ta samar ba, har ma da taimakawa wajen kafa tsarin kasa da kasa mai adalci da daidaito. (Lubabatu Lei)

Layin dogo
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Layin dogo
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta
  • Sulaiman
    Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen
  • Sulaiman
    Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci
  • Sulaiman
    Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Morocco: Kasar Da Ke Neman Zama Fuskar Kwallon Ƙafa A Duniya

Morocco: Kasar Da Ke Neman Zama Fuskar Kwallon Ƙafa A Duniya

LABARAI MASU NASABA

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
Layin dogo

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Layin dogo

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.