ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III Ya Cika Shekaru 70 A Duniya

by Abubakar Sulaiman
2 weeks ago
Musulmi

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya cika shekaru 70 a duniya a ranar Litinin, 24 ga watan Agusta, inda kuma zai cika shekaru 20 a kan karagar mulki a ranar 2 ga watan Nuwamba.

A wata kasida da Babban Editan jaridar LEADERSHIP kuma marubucin littafin Writing for Media and Monetising it’, Azu Ishiekwene, ya rubuta wadda ta biyo bayan makamanciyarta da ya rubuta masa yana da shekaru 65 a shekarar 2021 ya bayyana cewa Sarkin shi ne soja na farko da ya hau gadon sarautar.

Musulmi

Ya zama Sarki ne bayan rasuwar wansa, Muhammadu Maccido, da ɗan wansa, Sanata Badamasi Maccido, a hatsarin jirgin sama na shekarar 2006 wanda ya kashe mutane 93 a lokacin yana matsayin Birgediya.

ADVERTISEMENT

Kafin hakan, Sarkin wanda ya yi Kwas na 18 na Makarantar Sojoji ta NDA tare da tsohon hafsan Soji, Laftanar Janar Azubuike Ihejirika, ya taɓa zama wakilin tsaro a Pakistan, mai lura da Iran, da Iraki, da Afghanistan, da Saudiyya, da ƙasashen Gulf.

Sarkin Musulmi, wanda kuma yake mataimakin shugaban Majalisar Addinai ta Ƙasa, ya shahara wajen faɗa wa gwamnati gaskiya da yaƙar ta’addanci ba tare da shayi ba. Yayin rikicin ƙabilanci a jihar Filato, ya tabbatar da cewa duk wanda ya tunzura al’umma zai fuskanci hukunci, sannan ya faɗawa ‘yan Boko Haram da masu ra’ayin irin nasu cewa za su “wuce kai tsaye zuwa wuta!” maimakon samun matan aljanna kamar yadda suke iƙirari, yana mai dogaro da Suratul Ma’idah (5:78-79).

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Haka zalika, a taron majalisar addinai a Abuja, ya caccaki gwamnatin Shugaba Buhari kan ƙin bin umarnin kotu na sakin Omoyele Sowore, yana mai cewa hakan “hanya ce ta kawo hargitsi da bala’i.” Ya kuma alaƙata rashin tsaro da talauci da hauhawar farashi, inda ya ce “yunwa ba ta san addini ba,” sannan ya jagoranci kwamitin sasantawa tare da Janar Abdulsalami Abubakar zuwa Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulkin 2023, koda yake hakan bai hana ƙasashen Nijar, da Mali da Burkina Faso kafa ƙungiyar tsaro ta AES ba.

Game da fahimtar juna tsakanin addinai, lokacin da aka kashe Deborah Samuel a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari a Sokoto kan zargin cin zarafi ko tozarta addini, Majalisar Masarautar ta yi Allah wadai tare da neman a hukunta masu laifin, koda yake Gwamna Waziri Tambuwal bai yi aiki da shawarar ba sannan Atiku Abubakar ya goge saƙonsa na yin Allah wadai.

Sarkin ya ci gaba da jaddada mahimmancin ilimin yara mata da maza, inda ya tunatar da masu ƙyamar talaka ilimi cewa an kafa Daular Musulunci ne kan ilimi; kamar yadda marubuta Fola Fagbule da Feyi Fawehinmi suka bayyana a littafinsu na ‘Formations’ cewa Nana Asmau, ƙanwar Sarki Mohammed Bello, tana jin harsuna huɗu.

Wannan yunƙuri nasa na tabbatar da zaman lafiya ya sa aka tsayar da shi tare da Kadinal John Onaiyekan takarar lambar yabo ta Nobel Peace Prize, bayan da suka lashe kyautar Mutanen Shekara na LEADERSHIP a 2012.

Duk da waɗannan kyawawan halaye da nasarori, Ishiekwene ya bayyana cewa babban abin takaici ga Sarkin yayin da yake cika shekaru 70 shi ne ɓullar ƙungiyar Lakurawa a jihohin Kebbi da Sokoto, baya ga cibiyar rikicin Boko Haram a jihar Borno, lamarin da ya jefa yankin Arewa maso Yamma cikin barazanar ta’addanci irin na yankin Sahel.

Wani babban ƙalubale da Masarautar ta fuskanta shekaru biyu da suka wuce shi ne yunƙurin Gwamna Ahmed Aliyu na cire wa Majalisar Masarautar ikon naɗa hakimai a ƙarƙashin Dokar Ƙananan Hukumomi ta Sokoto; matakin da ko da yake an dakatar da shi yanzu, an kwatanta shi da cin fuskar da Gwamnatin Kano ta yi wa Sarki Muhammadu Sanusi shekaru biyar da suka gabata.

Da yake karɓo kalaman marubuci Kipling don bayyana shekarun Sarkin da kusan 20 a kan karagar mulki, marubucin ya siffanta shi a matsayin wanda ya ga nasara da koma-baya, amma duk ya ɗauke su a matsayi ɗaya.

Musulmi
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja

NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja

LABARAI MASU NASABA

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026
Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

September 8, 2026
Ballon D'or

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.