Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) reshen Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), ta tayar da jijiyar wuya kan yadda furofesoshi da sauran kwararrun malaman jami’ar sama da 200 suka yi murabus sakamakon taɓarɓarewar yanayin aiki da kuma ƙin aiwatar da yarjejeniyar shekarar 2025 tsakanin gwamnatin tarayya da ASUU.
Biyo bayan wannan mummunan lamari, ƙungiyar ta ba da wa’adin makonni biyu kacal ga mahukuntan jami’ar, da gwamnatin jihar Kaduna, da sauran masu ruwa da tsaki da su gaggauta fara aiwatar da wannan yarjejeniya. ASUU ta yi tsauraran kashedin cewa idan wa’adin ya cika ba tare da an biya musu buƙatunsu ba, za su tsunduma yajin aikin gama-gari kuma na sai-baba-ta-gani.
Shugaban ƙungiyar ASUU na reshen KASU, Kwamared Abubakar Abdullahi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin wani taron manema labarai a sakatariyar ƙungiyar da ke cikin jami’ar. Ya koka da cewa koda yake yarjejeniyar da ta tanadi kyautata rayuwar malaman ta fara aiki ne tun a watan Janairun 2026, har yanzu KASU ba ta nuna wata alama ta aiwatar da ita ba, lamarin da ya mayar da malaman jami’ar daga cikin waɗanda suka fi ƙarancin albashi a ƙasar nan.
Kwamared Abdullahi ya jaddada cewa yawancin malaman da suka raba gari da jami’ar sun koma wasu sababbin jami’o’i ne don neman sauƙin rayuwa, inda ya yi gargaɗin cewa asarar irin waɗannan gogaggun malamai zai ɗauki jami’ar shekaru masu yawa kafin ta farfaɗo.
Daga ƙarshe, ya roƙi iyaye da sauran al’ummar Nijeriya masu kishin ƙasa da su shiga tsakani don ganin gwamnati ta ɗauki matakin da ya dace don ceto ilimi.














