ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manoma Da Dama Za Su Yi Watsi Da Fannin Noma A Taraba A 2026 -AFAN

by Abubakar Abba
3 months ago
Manoma

Shugaban ƙungiyar manoma ta ƙasa reshen Jihar Taraba AFAN), Mista Saliu Adamu Kumba, ya zayyana manyan dalilan da za su tilasta ɗimbin manoman jihar yin watsi da noma a kakar noma ta 2026.

Ya sanar da cewa, akasarin manoman da ke jihar, ba za su yi noma ba, saboda saukar farashin kayan abinci da kuma tsadar farashin kayan feshi a jihar.

  • Manufar Kawar Da Harajin Kwastam Ta Sin Ta Haifar Da Sabbin Damammakin Hadin Gwiwar Noma Tsakanin Sin Da Zimbabwe
  • Jakadan Sin a Najeriya Ya Gana Da Shugaban Kwamitin Kula Da Makarantun Noma Da Cibiyoyin Bincike Na Majalisar Dattawa Ta Najeriya

Mitsa Kumba, wanda ya sanar da haka a hirarsa da jaridarmu ta LEADERSHIP a Jalingo, babban birinin jihar.

ADVERTISEMENT

Sai dai, ya kuma yi kira ga manoman da ke jihar, da kada su sake su yi ƙasa a gwaiwa, a kan yanayin da suka samu kansu, a kakar noma ta bara.

A cewar shugaban ƙungiyar, samun raguwar farashin amfanin gona a jihar, ya zame wa manoman jihar wani babban ƙalubale, musamman duba da irin ɗimbin kuɗaɗen da suka kashe, wajen yin noma a bara, wanda hakan ya jefa su cikin halin ni ‘yasu.

LABARAI MASU NASABA

Badaƙalar PFIPC: Ban Taɓa Haɗuwa Da Gbajabiamila Ba – Adeyemi

NNGF Ta Kaddamar Da Kwamitin Amintattu Na Gidauniyar Asusun Tsaro Ta Yankin

Kazalika, ya buƙaci manoman jihar, da su ci gaba da yin amfani da ƴan kuɗaɗen da suke da su, domin yin noma a kakar ta bana, musamman domin samar da wadataccen abinci a jihar da kuma a ƙasa baki-ɗaya.

Bugu da ƙari, Mista Kumba ya nanata cewa; manoma da dama a jihar a kakar noman bana, ba za su iya sayen takin zamani da taraktocin noma da kuma sauran kayan aikin yin noma ba, musamman saboda tsadar da waɗannan kayan suke da shi.

Ya nanata cewa, manoman jihar na buƙatar matuƙar tallafi da ƙara musu ƙwarin gwiwa, tare da kuma mayar da hankali daga ɓangaren gwamnati, musamman domin daƙile afkuwar yunwa a jihar.

Haka zalika, shugaban ya nuna ɓacin ransa, a kan yadda aka samu gagarumar raguwa a kakar noman rani ta bana, musaman idan aka kwatanta da ƙaruwar da aka samu mai ɗimbin yawa a kakar bara.

Har wa yau, ya sanar da cewa; matuƙar mahukunta a jihar ba su ɗauki matakan da suka dace na lalubo da mafita a kan wannan matsala ta yiwuwar yin watsi da aikin noma a tsakanin manoman jihar ba, akwai matsala.

Da yake yin tsokaci a kan taimaka wa manoman jihar da Gwamnan Jihar na Taraba Agbu Kefas, ya yi a kakar noma ta bara, shugaban ya jinjina masa matuƙa.

Mista Kumba ya kuma sake yin kira ga gwamnan, kan kada ya gajiya wajen ci gaba da taimaka musu, musamman a ɓangaren rage masu farashin kayan aikin noma, domin manoman jihar su ci gaba da samar da wadataccen abinci a jihar.

Kazalika, shugaban ya kuma yi kira ga matakan gwamnati uku na ƙasar nan da sauran ɗaiɗaikun mutane, musamman waɗanda ke jihar, da su taimaka wa manoman jihar kai tsaye, mai makon taimaka wa waɗanda ba manoman na haƙiƙa ba.

Manoma
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Ɗaura Ɗamarar Magance Matsalolin Kasuwanci Da Ƙasashen Waje
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Me Ya Sa Har Yanzu Manoma A Arewa Suka Gwammace Yin Noma Da Galmar Shanu
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Dalilin Masu Kiwon Kajin Gidan Gona Na Sukar Haɗakar Gwamnatin Tarayya Da Chana
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Abin Da Ya Sa Matatar Ɗangote Ta Ƙaryata Iƙirarin Dillalan Man Fetur 

MASU ALAKA

Badaƙalar PFIPC: Ban Taɓa Haɗuwa Da Gbajabiamila Ba – Adeyemi
Manyan Labarai

Badaƙalar PFIPC: Ban Taɓa Haɗuwa Da Gbajabiamila Ba – Adeyemi

July 8, 2026
NNGF Ta Kaddamar Da Kwamitin Amintattu Na Gidauniyar Asusun Tsaro Ta Yankin
Labarai

NNGF Ta Kaddamar Da Kwamitin Amintattu Na Gidauniyar Asusun Tsaro Ta Yankin

July 8, 2026
Yadda Na Sayar Da Kadarori Na Don Ɗaukar Nauyin Ɗalibai A Ƙasashen Waje – Kwankwaso
Labarai

Kwankwaso Ya Mayar wa Ali Modu Sheriff Martani, Ya Ce Peter Obi Na da Gagarumin Goyon Baya a Arewa

July 8, 2026
Next Post
Kofin Duniya

Ko Ka San Manyan Ƴanwasa Da Ƙasashen Da Ba Za Su Je Gasar Cin Kofin Duniya Ba?

LABARAI MASU NASABA

Badaƙalar PFIPC: Ban Taɓa Haɗuwa Da Gbajabiamila Ba – Adeyemi

Badaƙalar PFIPC: Ban Taɓa Haɗuwa Da Gbajabiamila Ba – Adeyemi

July 8, 2026
NNGF Ta Kaddamar Da Kwamitin Amintattu Na Gidauniyar Asusun Tsaro Ta Yankin

NNGF Ta Kaddamar Da Kwamitin Amintattu Na Gidauniyar Asusun Tsaro Ta Yankin

July 8, 2026
Yadda Na Sayar Da Kadarori Na Don Ɗaukar Nauyin Ɗalibai A Ƙasashen Waje – Kwankwaso

Kwankwaso Ya Mayar wa Ali Modu Sheriff Martani, Ya Ce Peter Obi Na da Gagarumin Goyon Baya a Arewa

July 8, 2026
Sojoji Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Waɗanda Aka Sace A Taraba

Sojoji Da NDLEA Sun Kama Mutanen Da Ake Zargi Da Kai wa ’Yan Ta’adda Miyagun Ƙwayoyi A Katsina

July 8, 2026
An Gudanar Da Manyan Tarurruka 3 Game Da Kimiyya Da Fasaha A Beijing

An Gudanar Da Manyan Tarurruka 3 Game Da Kimiyya Da Fasaha A Beijing

July 8, 2026
Majalisar Zartarwa Ta Jihar Kaduna Ta Amince Da Manufofin Haɓaka Walwalar Al’ummar Jihar

Majalisar Zartarwa Ta Jihar Kaduna Ta Amince Da Manufofin Haɓaka Walwalar Al’ummar Jihar

July 8, 2026
Dole Ne Mace Ta Gaya Wa Mijinta Gaskiya Domin Ranar Hisabi – Matar Gwamnan Jigawa

Gwamnatin Jigawa Ta Ɗaga Mafi Ƙarancin Fansho Zuwa Naira 20,000

July 8, 2026
Rahoton Bankin Duniya: Ci Gaban Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Dore

Rahoton Bankin Duniya: Ci Gaban Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Dore

July 7, 2026
Binciken CGTN Ya Shaida Kiraye-kirayen Jama’a Game Da Bukatar Hada Karfi Da Karfe Wajen Shawo Kan Kalubalen Tsanantar Yanayi

Binciken CGTN Ya Shaida Kiraye-kirayen Jama’a Game Da Bukatar Hada Karfi Da Karfe Wajen Shawo Kan Kalubalen Tsanantar Yanayi

July 7, 2026
Gwamnatin Tarayya Na Biyan Tallafin Man Fetur A Asirce – El-Rufai

Ɗan Takarar Gwamnan Kaduna Na ADC, Ya Gana da El-Rufai, Ya Sha Alwashin Kawo Karshen Mulkin APC

July 7, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.