ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, June 14, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ko Ka San Manyan Ƴanwasa Da Ƙasashen Da Ba Za Su Je Gasar Cin Kofin Duniya Ba?

by Abba Ibrahim Wada and Abubakar Sulaiman
2 months ago
Kofin Duniya

Kawo yanzu dai an kammala duk wani shiri na zuwa gasar cin kofin duniya bayan kammala duk wasu wasanni na cike gurbi ko kuma wasannin neman cancanta inda a ƙarshen watan da ya gabata aka kammala buga wasannin kuma duk ƙasar da za ta buga gasar yanzu ta san kanta kuma ta san cikin rukunin da take.

Sai dai ɗaya daga cikin ƴan wasan gaba mafi shahara a duniyar ƙwallon ƙafa a tsawon shekara 15 da suka wuce – ɗan ƙasar Poland Robert Lewandowski – yana cikin manyan ƴanwasan ƙwallon ƙafa da ba za su je gasar kofin duniya ba da za a yi a Canada, Amurka da kuma Meɗico a wannan shekara da muke ciki.

Ɗan wasan mai shekara 37 da ke buga wa ƙungiyar Barcelona wasa, wanda ya zura ƙwallaye 89 a ƙasarsa, ya kasa taimaka mata zuwa gasar kofin duniya bayan da suka yi rashin nasara a hannun Sweden da ci 3-2 a birnin Stockholm ranar Talata, a wasan ƙarshe na neman gurbin ɗuwa gasar ta cin kofin duniya.

ADVERTISEMENT

Lewandowski, wanda ya lashe gasar Bundesliga ta Jamus har sau goma – biyu da Borussia Dortmund sai kuma guda takwas a jere da Bayern Munich, kafin cin La Liga biyu da Barca – za a iya cewa ya buga wasansa na ƙarshe a matakin ƙasa a ƙasar tasa kuma tuni ya bayyana cewa ya yi bankwana da wakiltar ƙasar tasa.

Rashin samun nasarar Poland a gasar cin kofin duniya na shekarar 2026 ya sare gwiwar fitattun ƴanwasanta sannan kuma wannan ce dama ta ƙarshe ga ɗanwasa Robert Lewandowski da zai buga wa ƙasar gasar kofin duniya.

LABARAI MASU NASABA

Ghana Za Ta Kai Ƙarar Canada Kotu Kan Hana Thomas Partey Shiga Ƙasar

Allah Kaɗai Zai Iya Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Nijeriya – Matawalle

 

Ga jerin ƴanwasan da suka gaza zuwa gasar ta kofin duniya.

Gianluigi Donnarumma (Man City da Italiya)

Mai tsaron raga Gianluigi Donnarumma ya kasance mai tsaron raga mafi ƙwazo a gasar Premier a bana tun bayan komawa Manchester City daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Paris St-Germain kan fam miliyan 26 a watan Satumba, bayan taimaka wa ƙungiyar ta Faransa lashe gasar kofi Zakarun Turai a bara.

Duk da kasancewa ɗan wasan da ya fi haskawa lokacin da Italiya ta lashe gasar Euro 2020, yanzu ƙasarsa ta gaza zuwa gasar kofin duniya bayan rashin nasara da ci 4-1 a hannun Bosnia-Herzegoɓina a bugun fenariti ranar Talata. Italiya wadda ta lashe kofin duniya har sau huɗu ta rasa damar fafatawa a gasar ta shekarar 2026 karo na uku a jere.

Babu wata tawaga da ta taɓa lashe kofin duniya kuma ta gaza zuwa gasar cin kofin duniya har sau uku a jere sai Italiya. Ƙasar ba ta samu damar buga gasar kofin duniya ba shekarar 2018 a Rasha, da kuma Ƙatar a shekarar 2022.

 

Serhou Guirassy (Dortmund da Guinea)

Ɗan wasa Serhou Guirassy ya assasa kansa a matsayin ɗaya daga cikin ƴan wasan gaba mafi hazaƙa a duniyar ƙwallon ƙafa, inda ya zura ƙwallaye 62 a Bundesliga a cikin kakar wasanni uku da suka gabata, sannan babu ɗan wasan da ya ci ƙwallo sama da 13 wanda ya zura a gasar Champions League na kakar 2024-25. Sai dai, ba zai samu damar zuwa gasar kofin duniya ba, saboda ƙasarsa ta Guinea ta fita tun a zagayen farko na neman gurbi a ɓangaren Afirka, inda suka ƙare a matsayi na huɗu a rukuninsu, nasara huɗu kacal da kuma canjaras guda uku a cikin wasanni goma.

 

Khvicha Kɓaratskhelia (PSG da Georgia)

Khvicha Kɓaratskhelia ya taimakawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Paris St-Germain zama Zakarun Turai a bara, inda ya zura ƙwallo a wasan ƙarshe da suka doke Inter Milan 5-0. Ya kuma zo na 12 cikin jerin ƴan wasan da suka fi haskawa na kyautar Ballon d’Or. Sai dai Georgia ba ta taɓuka wani abin kirki ba a wasannin neman gurbin zuwa gasar kofin duniya, saboda maki uku kaɗai suka samu a cikin rukunin da ya ƙunshi ƙasashen

Spain, Turkiyya da kuma Bulgaria.

 

Lewandowski (Barcelona da Poland)

Lewandowski ya jagoranci Poland zuwa gasar kofin duniya ta 2018 a Rasha, sai dai bai zura ko da ƙwallo ɗaya ba inda ƙasarsa ta ƙare a ƙarshen teburin rukuninsu. Ya samu haskawa a gasar kofin duniya da aka yi a Ƙatar a 2022, inda ya zura ƙallo biyu har da kai Poland zagayen ƴan 16, kafin Faransa ta doke su.

Ya ci ƙwallaye huɗu a wasan rukuni na neman gurbin zuwa gasar kofin duniya na 2026, inda ƙasarsa ta ƙare a ƙasan Netherlands wadda ta fi ta da maki uku – kafin su yi rashin nasara a hannun Sweden ranar Talata.

 

Victor Osimhen (Galatasaray da Nijeriya)

Kawo yanzu dai Nijeriya bata da ɗan wasa kamar Ɓictor Osimhen, a shekarun baya ya taimaka wa Napoli ta lashe Serie A a 2023 kafin ya koma Galatasaray, inda ya zura ƙwallaye 26 a cikin wasanni 30, abin da ya ba su nasarar lashe gasar Turkiyya a bara. Nijeriya ta yi canjaras biyar a cikin wasanni 10 na neman gurbin zuwa kofin duniya, inda ta ƙare maki ɗaya ƙasan Afirka ta Kudu, sai dai sun samu dama ta biyu a wasan neman gurbi da ya biyo.

Nijeriya ta yi rashin nasara a hannun Kongo a bugun fenariti wanda aka buga bayan sauya Osimhen, abin da ya sa ƙasar ta kasa zuwa gasar kofin duniya.

Nijeriya ce ta 26 a jerin hukumar FIFA, kuma wannan ne karo na biyu da ba za ta samu damar bugar gasar ba a jere. Nijeriya ba ta samu damar shiga gasar ba a 2022 da aka yi a Ƙatar, tun bayan rashin fafatawarta a shekarar 2006. Nijeriya na taka rawar gani a duniyar ƙwallon ƙafa, inda take da fitattun ƴanwasa irin su Ɓictor Osimhen, Ademola Lookman, Aleɗ Iwobi, Calɓin Bassey, da Samuel Chukwueze. Sai dai duk da haka sun kasa kai wa matakin nasara.

 

Dominik Szoboszlai (Liverpool da Hungary)

Ɗan wasan tsakiyar Liverpool da Hungary Dominik Szoboszlai yana haskawa sosai a bana kuma ya ci ƙwallaye masu ƙayatarwa da ban sha’awa. Sai dai ba zai samu damar zuwa gasar kofin duniya ba bayan da ƙasarsa ta sha kashi a hannun Jamhuriyar Ireland da ci 3-2.

Sauran ƴan wasan da ba za su je gasar ba sun haɗa da; mai tsaron raga Jan Oblak (Atletico Madrid da Sloɓenia).

Milos Kerkez (Liɓerpool da Hungary).

Nikola Milenkoɓic (Nottingham Forest da Serbia)

Willi Orban (RB Leipzig da Hungary).

Ola Aina (Nottingham Forest da Nigeria).

Sandro Tonali (Newcastle da Italiya)

Bryan Mbeumo (Manchester United da Kamaru).

 

Ƙasashe shida da suka rage sun kammala wasanninsu, abin da ke nuna cewa yanzu ƙasashe 48 ne za su fafata. Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo da Iraƙi su ne ƙasashe biyu na ƙarshe da suka samu nasarar shiga gasar. DR Congo ta doke Jamaica, yayin da Iraƙi ta doke Boliɓia. An tabbatar da sauran ƙasashen turai huɗu ne a ranar Talatar da ta gabata, inda Bosnia-Herzegoɓina da Jamhuriyar Czech da Turkiya da Sweden suka samu nasara. Cikin ƙungiyoyi 48 da za su fafata, ƙasashe ukun da za su karɓi baƙuncin gasar sun samu tikiti kai tsaye, yayin da 43 kuma suka fafata a wasannin neman cancantar shiga gasar, sai kuma biyu da suka samu gurbin ta hanyar wasannin kifa ɗaya ƙwala a nahiyoyinsu.

 

Kofin duniya
Abba Ibrahim Wada
Website |  + posts Bio
  • Abba Ibrahim Wada
    Su Waye Wakilan Afirka A Kofin Duniya?
  • Abba Ibrahim Wada
    Jiya Aka Fara Gasar Cin Kofin Duniya
  • Abba Ibrahim Wada
    Real Madrid Ce Tafi Kowacce Kungiya Daraja A Duniya
  • Abba Ibrahim Wada
    Kofin Duniya: Sababbin Dokokin Da FIFA Ta Kawo
Kofin duniya
Abubakar Sulaiman
Website |  + posts Bio
  • Abubakar Sulaiman
    Allah Kaɗai Zai Iya Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Nijeriya – Matawalle
  • Abubakar Sulaiman
    Tsohon Kakakin Ma’aikatar Tsaro Rabe Abubakar Ya Rasu A Hannun ‘Ƴan Bindiga
  • Abubakar Sulaiman
    Yadda Matata Ta Daina Girki, Ta Ke Lakaɗamin Duka — Miji Ya Koka
  • Abubakar Sulaiman
    Zan Saki Nnamdi Kanu Idan Na Zama Shugaban Ƙasa – Peter Obi

MASU ALAKA

Ghana Za Ta Kai Ƙarar Canada Kotu Kan Hana Thomas Partey Shiga Ƙasar
Manyan Labarai

Ghana Za Ta Kai Ƙarar Canada Kotu Kan Hana Thomas Partey Shiga Ƙasar

June 13, 2026
Allah Kaɗai Zai Iya Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Nijeriya – Matawalle
Manyan Labarai

Allah Kaɗai Zai Iya Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Nijeriya – Matawalle

June 13, 2026
Tsohon Kakakin Ma’aikatar Tsaro Rabe Abubakar Ya Rasu A Hannun ‘Ƴan Bindiga
Manyan Labarai

Tsohon Kakakin Ma’aikatar Tsaro Rabe Abubakar Ya Rasu A Hannun ‘Ƴan Bindiga

June 13, 2026
Next Post
inec

INEC Ta Gargaɗi Jam’iyyu Kan Gudanar Da Babban Taro Ba Tare Da Sanin Ta Ba

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su Lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu (1)

Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su Lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu (1)

June 13, 2026
Talauci Ya Sake Karuwa Da Kashi 63 Duk Da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Da Gwamnati Ta Yi – IMF

Talauci Ya Sake Karuwa Da Kashi 63 Duk Da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Da Gwamnati Ta Yi – IMF

June 13, 2026
Muhallin Halittu Da Aka Yi Gado A Kasar Sin Sun Samu Ci Gaba Ta Fuskar Ba Su Kariya

Muhallin Halittu Da Aka Yi Gado A Kasar Sin Sun Samu Ci Gaba Ta Fuskar Ba Su Kariya

June 13, 2026
Gwamnonin Arewa-maso-yamma Sun Kaddamar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Yankin

Gwamnonin Arewa-maso-yamma Sun Kaddamar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Yankin

June 13, 2026

Sake Jan Damarar Soja Da Japan Ke Yi Karin Alama Ce Mai Hadari

June 13, 2026
NANS Ta Kafa Kwamitin Ganin Yadda Ake Tafiyar Da Ayyukan TETFund

NANS Ta Kafa Kwamitin Ganin Yadda Ake Tafiyar Da Ayyukan TETFund

June 13, 2026
Shugaban Majalisar Bayar Da Shawara Kan Harkokin Siyasa Ta Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Raya Dangantakar Gabobi Biyu Na Mashigin Tekun Taiwan Cikin Lumana

Shugaban Majalisar Bayar Da Shawara Kan Harkokin Siyasa Ta Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Raya Dangantakar Gabobi Biyu Na Mashigin Tekun Taiwan Cikin Lumana

June 13, 2026
Ghana Za Ta Kai Ƙarar Canada Kotu Kan Hana Thomas Partey Shiga Ƙasar

Ghana Za Ta Kai Ƙarar Canada Kotu Kan Hana Thomas Partey Shiga Ƙasar

June 13, 2026
Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili

Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili

June 13, 2026
Garkuwa Da Mutane Na Barazana Ga Dalibai Miliyan 1.9 Masu Jarrabawar WAEC A Sassan Nijeriya

Garkuwa Da Mutane Na Barazana Ga Dalibai Miliyan 1.9 Masu Jarrabawar WAEC A Sassan Nijeriya

June 13, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.