ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 17, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manoma Da Makiyaya 200 Sun Amfana Daga Shirin SPAR Na Noma A Katsina

by Abubakar Sulaiman
5 months ago
Manoma

Aƙalla manoma da masu kiwon dabbobi 200 ne suka amfana da shirin Sustainable Peace and Resilience (SPAR) a jihar Katsina, wani tsari da aka ƙaddamar domin inganta zaman lafiya da ƙarfafa hanyoyin samun abin dogaro ta hanyar noma mai dacewa da sauyin yanayi.

Manajan aikin na Women Environmental Programme, Damaris Uja, ta bayyana hakan yayin taron rufe aikin da bitar darussa, inda ta yi bayani kan tasirin shirin a al’ummomin da suka ci gajiyarsa.

Ta ce shirin, wanda Foreign, Commonwealth and Development Office ke tallafawa tare da haɗin gwuiwar ActionAid da Tetra Tech, an ƙirƙire shi ne domin magance tushen rikice-rikicen manoma da makiyaya tare da inganta juriya ta tattalin arziki.

ADVERTISEMENT

A cewarta, an zaɓi masu cin gajiyar kai tsaye 200 daga jihohin Katsina da Binuwe, inda kowace jiha ta bayar da manoma 50 da makiyaya 50, yayin da wasu da dama suka amfana a daga gefe.

Shirin ya haɗa da horo kan kiwon dabbobi mai ɗorewa da noma mai jure sauyin yanayi, tare da samar da ƙaramar Ruga da aquaponics domin ƙara hanyoyin samun kuɗi da inganta wadatar abinci.

LABARAI MASU NASABA

Lalong Da Uwargidan Shugaban Ƙasa Sun Goyi Bayan Ci Gaban Sauye-Sauyen Tinubu

2027: Za Mu Kawo Wa Tinubu Kano Duk Da Tasirin Kwankwaso – Kofa

Haka kuma, an jaddada muhimmancin haɗa mata da masu nakasa cikin shirin, yayin da aka gudanar da wayar da kai da ziyarce-ziyarcen shawarwari ga gwamnati da sarakunan gargajiya domin tabbatar da dorewar shirin.

A nasa ɓangaren, jagoran shirin SPRING, Ukona Ukiwo, ya bayyana cewa haɗa batun sauyin yanayi da rikicin manoma da makiyaya yana da muhimmanci, yana mai cewa shirin ya taimaka wajen ƙarfafa hanyoyin warware rikici da gina juriya a tsakanin al’umma.

Ya ƙara da cewa tun fara shirin a 2024, an yi aiki da hukumomi da al’umma domin ƙarfafa tsarin gargaɗi da matakan magance rikice-rikice, tare da tallafa wa manufofi da dokoki da ke inganta sarrafa albarkatu da zaman lafiya.

Manoma
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Babu Dalilin Da Zai Sa Nijeriya Yin Talauci – Obasanjo
  • Abubakar Sulaiman
    Air Peace Da United Nigeria, Jirage 2 Masu Latti Sosai Watan Agusta — NCAA
  • Abubakar Sulaiman
    Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Hannun Jarin Matatar Dangote
  • Abubakar Sulaiman
    Ka Kyale Ni Nayi Wa Mutanen Binuwai Aiki – Gwamna Alia Ga Ortom

MASU ALAKA

Lalong Da Uwargidan Shugaban Ƙasa Sun Goyi Bayan Ci Gaban Sauye-Sauyen Tinubu
Labarai

Lalong Da Uwargidan Shugaban Ƙasa Sun Goyi Bayan Ci Gaban Sauye-Sauyen Tinubu

September 17, 2026
2027: Za Mu Kawo Wa Tinubu Kano Duk Da Tasirin Kwankwaso – Kofa
Manyan Labarai

2027: Za Mu Kawo Wa Tinubu Kano Duk Da Tasirin Kwankwaso – Kofa

September 17, 2026
Marafa Ya Yi Alƙawarin Murabus Idan Ya Kasa Magance Tsaro Cikin Shekaru Biyu
Labarai

Marafa Ya Yi Alƙawarin Murabus Idan Ya Kasa Magance Tsaro Cikin Shekaru Biyu

September 17, 2026
Next Post
JAMB Ta Ƙara Wa’adin Sayar Da Fom Ɗin Shiga Jami’a Kai Tsaye Zuwa 8 Ga Watan Mayu

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Sayar Da Fom Ɗin Shiga Jami'a Kai Tsaye Zuwa 8 Ga Watan Mayu

LABARAI MASU NASABA

Lalong Da Uwargidan Shugaban Ƙasa Sun Goyi Bayan Ci Gaban Sauye-Sauyen Tinubu

Lalong Da Uwargidan Shugaban Ƙasa Sun Goyi Bayan Ci Gaban Sauye-Sauyen Tinubu

September 17, 2026
Fitar Da Shirin Shekaru 5 Ya Bude Sabo Babi Na Tsarin Ci Gaban Yankin HK

Fitar Da Shirin Shekaru 5 Ya Bude Sabo Babi Na Tsarin Ci Gaban Yankin HK

September 17, 2026
 Xi Ya Yi Kira Da A Wanzar Da Kokarin Fadada Da Karfafa Ci Gaban Fannin Kere-kere

 Xi Ya Yi Kira Da A Wanzar Da Kokarin Fadada Da Karfafa Ci Gaban Fannin Kere-kere

September 17, 2026
2027: Za Mu Kawo Wa Tinubu Kano Duk Da Tasirin Kwankwaso – Kofa

2027: Za Mu Kawo Wa Tinubu Kano Duk Da Tasirin Kwankwaso – Kofa

September 17, 2026
Marafa Ya Yi Alƙawarin Murabus Idan Ya Kasa Magance Tsaro Cikin Shekaru Biyu

Marafa Ya Yi Alƙawarin Murabus Idan Ya Kasa Magance Tsaro Cikin Shekaru Biyu

September 17, 2026
An Ci TikTok Tarar Fam Miliyan £12.7 Kan Karya Dokar Kananan Yara A Burtaniya

Hisbah Ta Cika Hannu Da Fitaccen Ɗan TikTok A Kano Kan Bidiyoyin Rashin Da’a

September 17, 2026
Tinubu Zai Shiga Tsakani A Rikicin Wike Da Gwamnonin APC

Tinubu Zai Shiga Tsakani A Rikicin Wike Da Gwamnonin APC

September 17, 2026
Kawayen amarya

’Yansanda Sun Ceto Mutane, Sun Daƙile Harin ’Yan Bindiga A Katsina

September 17, 2026
Aisha Buhari Ta Ziyarci Atiku

Aisha Buhari Ta Ziyarci Atiku

September 17, 2026
Nazarin CGTN: Dole Ne Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Samar Da Tsaro Mai Dorewa

Nazarin CGTN: Dole Ne Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Samar Da Tsaro Mai Dorewa

September 16, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.