Yunkurin neman kujerar Sarkin Gumel ta fara daukar sabon salo bayan rasuwar marigayi Sarkin Gumel, Alhaji Dr Ahmed Muhammad Sani II, inda wasu daga cikin ’ya’yan gidan sarautar suka fara bayyana sha’awarsu ta maye gurbinsa.
Rahotanni sun ce a halin yanzu akwai wasu fitattun ’ya’yan gidan sarautar da ke takarar neman kujerar, yayin da ake jiran tsarin da za a bi wajen tantance wanda ya fi cancanta ya gaji marigayin.
Marigayi Ahmed Muhammad Sani II ya rasu ne a ranar 3 ga Satumba, 2026 a birnin Alkahira na kasar Masar, bayan ya shafe sama da shekaru 40 yana jagorantar Masarautar Gumel.
Rasuwarsa ta jefa al’ummar Gumel da Jihar Jigawa cikin jimami, tare da bude babbar kafa ta neman wanda zai gaji kujerar mai muhimmanci a tarihin masarautar. Masarautar Gumel na daga cikin tsoffin masarautun Arewacin Nijeriya, kuma marigayi Sani II shi ne sarki na 16 a jerin sarakunan Gumel.
Yayin da ake sa ran fara bin matakan a hukumance na zaben sabon sarki, hankalin al’umma ya koma kan ’ya’yan gidan sarautar da za su fafata da juna, da kuma yadda za a gudanar da tsarin gadon sarautar cikin lumana domin kare hadin kan masarautar.














