ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, June 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matsalar Ɓacewar Gandun Dazukan Nijeriya

by Ra'ayinmu
3 months ago
Nijeriya

Gandun dazukan ƙasar nan, na buƙatar a samar masu da ɗaukin gaggawa, na kula da su, yadda ya kamata

Misali, gidauniyar da ke kula da gandun daji ta ƙasa, wato NCF ta yi gargaɗin cewa, Nijeriya ta yi asarar aƙalla kaso 90 na gangun dazukan da ke a ƙasar, a cikin ƙarni uku kacal, da suka wuce

Wannan asarar, ta sanya an rasa ƙasa da kaso 10 na faɗin ƙasar da ake da shi, a gandun dazukan ƙasar.

ADVERTISEMENT

Kazalika, wannan adadin, ya nuna yadda ake ci gaba da samun, ƙaruwar sare Bishiyoyin, da ke a cikin dazukan ƙasar, wanda ya haura, na adadin duniya.

  • Wata Ƙungiya Ta Mara Wa Ganduje Baya Don Zama Daraktan Kamfen Ɗin Tinubu A 2027
  • Gwamnan Sakkwato Ya Nada Manyann Mukaman Gwamnati A Jihar

A ɓangare ɗaya, batun ƙalubalen rashin tsaro, hauwan farashin kaya da rashin nuna damuwa, daga gun masu riƙe da madafun iko na siyasa a ƙasar, na ci gaba da zama barazana, ga gandun dazukan ƙasar.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kama Ɗan Fashi Da Makami A Taraba

An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

Ana ci gaba da samun ƙaruwar sare Bishiyoyi, a dazukan, ta haramtacciyar hanya, saboda buƙatar da ake da ita, ta Gawayi da kuma Katakon, da ake fasaƙwarinsa, zuwa kasuwannin duniya.

Bugu da ƙari, biyo bayan ci gaba da samun yawan alumma a ƙasar, hakan ya sanya, ana ci gaba da buƙatar Itacen yin girki da kuma sauran buƙatar da ake da ita, ta Itacen.

Bisa wasu alƙaluma da ƙungiyar ƙasa da ƙasa da ke sanya ido kan gandun daji wato Global Forest Watch, ta sanar da cewa, a tsakain 2001 zuwa 2024, Nijeriya ta yi asarar hecktar da ta kai miliyan 1.4, tare da kuma wasu hekta aƙalla dubu 250, 000 da suka ɓace, a 2024.

Hakazalika, hukumar ta NCF, ta ƙiyasta cewa, a duk shekara, Nijeriya na yin asarar hekta 400,000 da ke a cikin gandun dazukan ƙasar.

Wannan matsalar na ƙara janyo sare Bishiyoyi, da ke gandun dazukan ƙasar, musamman a yankin Sahele, na Arewaci ƙasar da kuma ci gaba da samun aukuwar ambaliyar ruwan sama a kudancin Sahel.

Kazalika, matsalar na kuma janyo zaizayar ƙasa da samun raguwar ruwa, musamman a Kainji da Shiroro, inda hakan ke haiyar da ambaliyar ruwan da ke kwararowa, zuwa cikin birane.

Misali, a johohin da ke a cikin Sahel, kamar irinsu, Borno, Yobe, Jigawa, Bauchi da Katsina, matsalar sare Bishiyoyi, na shafar ƙasar noma da ƙara aukuwar ambaliyar ruwa tare da kuma ƙara haddasa, talauci, ga mazauna karkara.

Akasarin alumomin da ke a Arewa da wanda suke a yankin Tsakiyar Nijeriya, wato Middle Belt, sun jima, suna dogaro da albarkatun da suke samu, daga cikin gandun zazukan ƙasar, inda suke samun saiwoyin Itace, da suke sarrafa sum zuwa magunguna da yin farauta da sauransu.

Sai dai, ɓacewar waɗannan kadarorin, na ci gaba da tarwatsa iyalansu da kuma gaba da aukuwar rikice-rikice.

Misali, matsalar rikice-rikice, a tsakanin Fulani makiyaya da manoma, tuni, ta ƙara ta’azzara, ƙalubalen rashin tsaro, wanda hakan ya haifar da ɓacewar Burtali, da dabbobin Fulanin ke yin kiwo a kansu.

Wannan, na ƙara haifar da matsalar yin balagoron mazuna karkara, zuwa cikin birane, tare da kuma haifar da rashin aikin yi. Inda hakan kuma ke sanya, ƴan ta’adda, yin hayar matasa, domin gudanar da ayyukan ta’adanci

Waɗannan matsalolin, sun nuna a zahiri, na rashin iya gudanar da shugabanci, a tsakanin ƴan siyasa, masu riƙe da madafun iko.

Kundin tsarin mulkin ƙasar na 1999 da aka sabunta, ya ɗorawa gwamnonin jihohin ƙasar, nauyin kare rayuka da dukiyoyin ƴan ƙasar

Duk da tsare-tsaren ƙasa da aka samar domin kare gandun dazukan ƙasar, amma abin takaici, tun daga matakin jihohi har zuwa na tarayya, babu wani ƙoƙari da suka yi, na bayar da kariyar.

Ƙwararu a fannin kare muhalli a ƙasar, na ci gaba da bayar da shawarar ɗaukar matakan da suka kamata, domin a bai wa gandun dazukan ƙasar, kariyar da ta kamata.

Kazalika, akwai kuma buƙatar tun a matakin jiha, da na tarayya, a tabbatar da sun ɗauki matakin gaggauawa, musaman domin a magance, sare Bishiyoyin da ke a cikin gandun dazaukan ƙasar.

Ya kuma zama wajbi, a yi koyi da irin salon yin gangami na ƙasar Ethiopia, na kare gandun dazuka tare da kuma bai wa alumomin ragamar ci gaba da bai wa gandun dazukan kulawar da ta kamata.

Kazalika, akwai buƙatar a samar da Jirage, marsa matuƙa, da za su rinƙa bayar da tsaro, a gandun dazukan ƙasar da kuma tura dakarun kula da gandun dazukan ƙasar, musamman domin yaƙar, masu sarar Bishiyoyi, ta haramtacciyar hanya.

Bugu da ƙari, ya kamata a tanadi hunkunci mai tsauri, kamar dai yanke hukuncin zama gidan yari, ga masu sarar Bishishiyin da ke a gandun dazukan ƙasar ƙasar.

Ya waja, a samar da wani tsari, na yin amfani da makamashi, wanda hakan zai daƙile yawan sarar Bishiyoyin domin samar da Gwayin yin girki.

Matuƙar gandun dazukan ƙasar nan suna ɓace ɓata, Nijeriya za ta yi asarar ba wai ruwa ba kawai, har da ma, gaza samar da wadataccen abinci, inda kuma kwararowar mazauna karkara da aukuwar rikice-rikice za su ƙara ƙaruwa, a ƙasar.

Nijeriya
Ra'ayinmu
+ postsBio
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Shin Nijeriya Ta Shirya Tunkarar Dawowar Annobar Ebola?
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Buƙatar Samar Da Alƙibla Ta Musamman Ga Gidajen Gyaran Hali Na Ƙasar Nan
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Ce-ce-ku-ce Kan Batun Biyan Bashin Naira Tiriliyan 3.3 Na Kuɗin Lantarki
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Buƙatar Magance Matsalar Ƙarancin Abinci Mai Gina Jiki A Tsakanin Ƙananan Yara

MASU ALAKA

Sojoji Sun Kama Ɗan Fashi Da Makami A Taraba
Labarai

Sojoji Sun Kama Ɗan Fashi Da Makami A Taraba

June 24, 2026
An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi
Labarai

An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

June 24, 2026
Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga
Manyan Labarai

Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

June 24, 2026
Next Post
Fadar Shugaban Ƙasa Ta Gargaɗi Peter Obi Kan Zargin Tinubu Na Haddasa Rikici A ADC

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Gargaɗi Peter Obi Kan Zargin Tinubu Na Haddasa Rikici A ADC

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kama Ɗan Fashi Da Makami A Taraba

Sojoji Sun Kama Ɗan Fashi Da Makami A Taraba

June 24, 2026
An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

June 24, 2026
Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

June 24, 2026
Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu

Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu

June 23, 2026
Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani

Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani

June 23, 2026
Gombe Ta Zabge Farashin Taki Da Kashi 50 Cikin 100

Gombe Ta Zabge Farashin Taki Da Kashi 50 Cikin 100

June 23, 2026
Wang Yi Ya Gana Da Babban Sakataren Majalisar Tsaron Masar Da Ministan Fadar Gwamnatin Afirka Ta Kudu A Indiya

Wang Yi Ya Gana Da Babban Sakataren Majalisar Tsaron Masar Da Ministan Fadar Gwamnatin Afirka Ta Kudu A Indiya

June 23, 2026
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

’Yansanda Sun Kama Mutane 57 Da Ake Zargi Da Ayyukan Ta’addanci A Adamawa

June 23, 2026
Li Qiang Ya Gana Da Firaministan Kasar Guinea

Li Qiang Ya Gana Da Firaministan Kasar Guinea

June 23, 2026
Maniyyatan Nijeriya

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Jigilar Alhazan Nijeriya Daga Saudiyya

June 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.