ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matsalar Tsaro: Yadda Tinubu Ya Dauki Matakin Dakile Tasirin Nuhu Ribadu

by Sani Anwar
4 months ago
Tinubu

Nadin Adeyinka Famadewa, Manjo-Janar mai ritaya, a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin tsaron cikin gida, ya haifar da cece-kuce kan wani sabon salo na tsarin tsaro na Nijeriya, karkashin Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Tinubu, wanda a halin yanzu yana wajen kasar, ya sanar da nadin ne ta wata takardar sanarwa a ranar Litinin, mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, wadda kuma babban sakatare na ofishin kula da ayyuka Ibrahim Kana ya bayar.

A cewar Akume, nadin ya kara jaddada kudirin gwamnatin Tinubu, na karfafa hadin kan tsaro a cikin gida da inganta ayyukan sirri da zurfafa hadin gwiwar hukumomin tsaro, wajen magance matsalolin na tsaro da suka kunno kai a fadin kasar nan.

ADVERTISEMENT

Daily trust ta ruwaito cewa, a ‘yan kwanakin nan, Nijeriya ta fuskanci kalubalen tsaro, inda sojoji da ‘yansanda da sauran jami’an tsaro, suka suka fuskanci babban kalubale daga ‘yan ta’adda tare kuma da kona na’urorin tsaro na zamani.

Yayin da wasu ‘yan Nijeriya ke ganin cewa, matakin da shugaban kasar ya dauka na kan hanya mai kyau, wasu kuma na ganin cewa; nadin na da nasaba da siyasa, kuma zai iya zama wani yunkuri na rage wa mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, karfin iko.

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

Manyan Janar guda biyu da suka yi ritaya, sun ba da ra’ayoyi daban-daban kan dalilin da ya sa Shugaba Tinubu ya kirkiro ofishin mai ba da shawara na musamman kan harkokin tsaron cikin gida.

“Bana tunanin zai tsige Ribadu, na yi imani yana kokarin tabbatar da kafa ‘yansandan jiha ne, zai yi amfani da shi (sabon mai ba shi shawara) da Sufeto-Janar na ‘yan sanda (IGP), wajen kafa ‘yansandan,” daya daga cikin Janar din ya shaida wa Daily trust.

Wani Janar ya ce, “Ba zai sallami Ribadu da wuri ba, domin shi ne ke tsara tsare-tsaren hukumar leken asiri ta kasa, shi kuma Janar din zai kula da tsaron cikin gida.

“Duk da haka, idan aka yi la’akari da siyasar kabilanci da ake gani tun lokacin da gwamnati mai ci ta hau mulki, ba zan yi mamaki ba idan Ribadu ya koma gefe, watakila a kan kuri’un Arewa-maso-gabas, yana iya barin sa, duk da haka, kada wani ya gaya min cewa; wannan nadin an yi shi ne bisa cancanta, wace cancanta?”

Wani masani kan harkokin tsaro, wanda ba ya so a bayyana sunansa, ya ce; za a iya samun matsala.

A cewarsa, “Akwai ayyuka masu alaka da juna, babu shakka game da hakan. A Amurka, an raba su gida biyu, NSA mai ba da shawara ne, sannan kuma Sakataren Tsaron Cikin Gida, daidai yake da minista.

“Amma a ce Ribadu da wannan mutumin duk masu ba da shawara ne, hakika wannan wani abu ne daban. Watakila Ribadu ba zai sake jin dadin amincewa da Tinubu ba,” in ji shi. Majiyar ta ce, ra’ayin bai goyi bayan Ribadu ba.

“A haka ne sannu a hankali, Tinubu ya bata wa Wale Edun rai, har sai da ya fita (Edun), na farko, duk wani muhimmin aiki da Edun ya kamata ya yi, an karbe an bai wa wani karamin minista daban ya yi.

Tinubu
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki
Labarai

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
Tinubu
Labarai

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Tinubu
Labarai

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Next Post
Zan Bai Wa Al’ummar Filato Fifiko – Mai Neman Takarar Gwamna A PDP

Zan Bai Wa Al’ummar Filato Fifiko - Mai Neman Takarar Gwamna A PDP

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
Tinubu

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Tinubu

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.