ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Kashim Imam Ke Yi A Yanzu?

by Sulaiman
3 months ago
Imam

Kashim Ibrahim Imam, fitaccen dan siyasa kuma abokin kasuwancin Shugaba Bola Tinubu, ya shiga sahun ’yan adawar da ke neman kifar da gwamnatin shugaban kasa daga mulki a babban zaɓen shekarar 2027.

A cewarsa da kansa, Imam ya yanke shawarar kawo karshen shekaru 36 na abota tsakaninsa da Shugaba Tinubu domin mara wa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, baya a takarar shugaban kasa ta shekara mai zuwa.

Babu wani rahoto da ya nuna cewa akwai saɓani na siyasa ko kasuwanci tsakanin Shugaba Tinubu da Kashim Imam.Abin da aka sani kawai shi ne wani ɗan gajeren rahoto da dan siyasar na Borno ya wallafa a shafinsa na sada zumunta watanni da suka gabata, inda ya yi watsi da goyon bayansa ga Tinubu saboda abin da ya kira “rashin adalci”, tare da cewa akwai “ɗimbin arziki a Nijeriya, na ɓoye ko na fili.”

ADVERTISEMENT

Rahotannin kafafen yada labarai da bayanan fadar shugaban kasa sun nuna cewa Tinubu da Imam na ci gaba da kyakkyawar alaka har zuwa farkon wannan gwamnati.Watanni biyar bayan shugaban kasa ya hau mulki, ya yi wani naɗin muƙami da ya yi, ya haifar da cece-kuce a tsakanin jama’a.

Imam Kashim Imam, matashi mai shekaru 24 da ya kammala karatun injiniyanci kuma dan wani abokin siyasar shugaban kasa, an nada shi shugaban hukumar kula da gyaran hanyoyi ta tarayya (FERMA), sanadiyyar wannan naɗin ne ya haifar da cece-kuce tsakanin jama’a.

LABARAI MASU NASABA

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

Kafafen yada labarai sun ruwaito cewa mahaifinsa, Kashim Ibrahim Imam, ya taka muhimmiyar rawa sosai wajen yakin neman zaben Tinubu da kuma nasararsa a zaben shugaban kasa.

Nadin na daya daga cikin na farko da shugaban kasa ya yi, duk da cewa ya dauki kusan watanni uku kafin ya nada ministoci 45 da suka shiga majalisar ministocinsa.

Har watanni 12 kafin karewar zangon mulkinsa na farko, mukaman jakadun Nijeriya da dama ba a cike su ba. Wannan ya nuna irin muhimmancin da Tinubu ya bai wa nadin matashin Imam a matsayin shugaban FERMA da kuma irin kusancin da ya sa aka yi la’akari da shi a watan Oktoban 2023.Sai dai, cece-kucen da jama’a suka yi, ya yi tasiri sosai har shugaban kasa ya janye nadin bayan mako guda.

Baban Imam, wanda ya taba kasancewa babban abokin hamayyar Ali Modu Sheriff a siyasar Borno kuma ya yi takara sau biyu da tsohon gwamnan, ya kasance daya daga cikin jiga-jigan taron jam’iyyun adawa da aka gudanar a Ibadan, jihar Oyo, a karshen watan Afrilu.

Jam’iyyun siyasar sun nemi samar da hadin kai tare da tsayar da dan takarar shugaban kasa guda daya domin kalubalantar Shugaba Tinubu a watan Janairu mai zuwa, har ma suka fitar da sanarwar hadin kai.

Sai dai hadakar ta watse bayan mako guda bayan tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, sun fice daga jam’iyyar ADC zuwa NDC domin tsayawa takara tare a karkashin tikiti guda.

Imam
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

MASU ALAKA

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Rahotonni

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

September 5, 2026
Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
Rahotonni

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

September 5, 2026
Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
Rahotonni

Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki

September 5, 2026
Next Post
Yari Ya Dace Da Rayuwar Mulki Da Kasuwanci

Yari Ya Dace Da Rayuwar Mulki Da Kasuwanci

LABARAI MASU NASABA

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.