ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci Matasa Su Riƙa Tantance Sahihancin Labari Kafin Su Yaɗa Shi

by Shehu Yahaya and Sulaiman
6 months ago
Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya gargaɗi cewa yaɗa labaran ƙarya yana haifar da babbar barazana ga ɗabi’a da haɗin kan ƙasa, inda ya yi kira ga matasan Nijeriya da su riƙa tabbatar da sahihancin duk wani labari kafin su yaɗa shi.

 

Ministan ya bayyana hakan ne yayin Laccar Ramadana ta Haɗin Gwiwa karo na 20 wadda Hukumar Talbijin ta Nijeriya (NTA), Hukumar Rediyon Tarayyar Nijeriya (FRCN) da gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON) suka shirya a Kaduna.

ADVERTISEMENT
  • Jami’ar Osun Ta Buƙaci Wani Kamfani Ya Janye Kalamansa Kan Batun Ma’aikatan Bogi A Jami’ar
  • Ban Fuskanci Matsala Ba A Gwagwarmayar Shiga Harkar Fim —Asiya Muhammad

Ya yi gargaɗin cewa amfani da kafafen sadarwa ta hanyar da ba ta dace ba yana iya ƙara rarrabuwar kawuna da raunana haɗin kan ƙasa.

 

LABARAI MASU NASABA

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

A cewar sa, duk da cewa fasahar zamani ta kawo damammaki masu yawa, tana kuma zuwa da ƙalubalen ɗabi’a da ke buƙatar ladabi da ɗaukar alhaki.

 

Idris ya ce tantance sahihancin labari ya zama wajibi na ɗan ƙasa da kuma nauyin ɗabi’a a wannan zamani, yana mai cewa, “Sanin yadda kafofin watsa labarai suke aiki shi ne rigakafin yaɗuwar labaran ƙarya.”

 

Ministan ya buƙaci matasa da su yi amfani da kafafen dijital wajen neman ilimi, ƙirƙire-ƙirƙire da bunƙasa ƙasa, maimakon haifar da rarrabuwa.

 

Ya ƙara da cewa: “Ku tantance kafin ku yaɗa. Ku dakata. Ku binciki tushe,” yana mai jaddada cewa wajibi ne a yi amfani da fasahar zamani wajen ƙarfafa haɗin kai da cigaba.

 

Ya jaddada cewa yawan matasan Nijeriya na daga cikin manyan ƙarfin ta, amma makomar ƙasa tana dogara da yadda ake jagorantar su da tallafa masu.

 

Ya ce: “Ƙasar da ta kasa kula da matasan ta ba ta da makoma. Muna saka hannun jari a tsarin da zai mayar da fasahar dijital matattakalar samun damarmaki.”

 

Ministan ya bayyana cewa gwamnati tana aiwatar da shirye-shiryen tallafa wa matasa da dama a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ciki har da shirin 3MTT, Lamunin Ilimi na Nijeriya (NELFUND), da kuma kafa cibiyar farko a Afrika ta koyar da ilimin kafofin watsa labarai.

 

Haka kuma, Ministan ya ambaci amincewar da UNESCO ta bai wa Nijeriya ta karɓar baƙuncin cibiyar farko a Afrika ta Ilimin Kafofin Watsa Labarai (IMILI), yana mai cewa wannan wani muhimmin mataki ne wanda zai taimaka wajen horar da jama’a kan tunani mai zurfi domin guje wa ruɗin labarai.

 

Ya nanata cewa kare ɗabi’a da sararin labarai ba aikin gwamnati kaɗai ba ne, yana kira ga iyaye, malamai, shugabannin addini, ‘yan jarida da matasa da su haɗa kai wajen gina al’umma mai fasaha da ɗabi’a tagari.

 

Laccar ta bana ta samu halartar gwamnonin jihohi da manyan jami’an gwamnati da sarakunan gargajiya da shugabannin kafafen yaɗa labarai daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Minista
Shehu Yahaya
+ posts Bio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamna Uba Sani Ya Yi Jimamin Rasuwar Dan Jarida Jafaru Yakubu Maitama
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamnatin Kaduna Ta Fara Rabon Takin Zamani Kyauta Ga Manoma 150,000
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Zaka Iya Sayar da Takin Gwamnati Ka Sayawa Iyalinka Kaji — Imam Nuradden
Minista
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina Kasa

MASU ALAKA

Minista
Labarai

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Minista
Labarai

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
Next Post
Shawarwari 40 Zuwa Ga Uwargida   (1)

Shawarwari 40 Zuwa Ga Uwargida (1)

LABARAI MASU NASABA

Minista

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Minista

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.