ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Na Bar Harƙoƙin Siyasa Gaba Ɗaya – Ɗan Takarar Gwamnan Bauchi, Air Marshal Saddique Baba

by Khalid Idris Doya
4 months ago

Ɗan takarar gwamnan jihar Bauchi wa jam’iyyar APC a zaɓen 2023, Air Marshal Saddique Baba Abubakar (mai ritaya) ya sanar da barin harƙoƙin siyasa daga yanzu sakamakon wasu dalilai da bai bayyana su ba.

Saddique tsohon shugaban sojojin saman Nijeriya (CAS) ne ya shiga harƙoƙin siyasa a 2021 bayan kammala aikin sojan sama.

A zaɓen 2023 ya yi tashe sosai har an sanya masa ran zama gwamnan jihar Bauchi amma Bala Mohammed na jam’iyyar PDP ya kayar da shi.

ADVERTISEMENT

Hakazalika, Saddique Baba Abubakar yana daga cikin waɗanda ake sa ran za su sake fitowa takarar gwamnan jihar Bauchi a zaɓen 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar Action Democratic Party (ADP) kwatsam sai ya fito ya sanar da yin murabus daga harƙoƙin siyasa.

Wannan lamarin ya zo da abun mamaki musamman ga magoya bayansa, inda ya shaida cewar matsayar da ya ɗauka ta kasance masa mai wuyan gaske, sai ya bai wa masoya da magoya bayansa hakuri bisa wannan matsayar nasa.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

A wani gajeren saƙon bidiyo da ya fitar wa al’ummar jihar Bauchi a ranar Asabar 16 ga watan Maris 2027, Saddique Baba ya ce duk da ya daina harƙoƙin siyasa, amma zai ci gaba da bayar da gudunmawarsa wajen ci gaban al’umman jihar Bauchi musamman ta ɓangaren kiwon lafiya da ilimi ƙarƙashin gidauniyarsa ta ‘Marshal Care Foundation’.

A saƙon na cewa: “Dukkanin godiya da yabo sun tabbata ga Allah Subhanahu wata’ala; Allah shi kaɗansa ke tabbatar da al’amura.

Abun da Allah ya tabbatar ba mai iya gusar da shi, haka kuma abun da Allah ya gusar ba mai iya tabbatar da shi. “Bayan godiya wa Allah subhanahu wata’ala.

A yau, ina cike da zuciya mai nauyi na yanke mawuyacin shawara barin al’amuran siyasa saboda wasu dalilai nawa.

“Wannan mawuyacin shawarar bai zo mini da sauƙi ba, ganin mutane masu ɗumbin yawa da suka nuna min so da ƙauna a jihar Bauchi da ma ƙasa baki ɗaya tun shigowata siyasa a shekara 2021 har ya zuwa yau,” ya shaida.

“Ina matuƙar godiya marar iyaka. Ina bada haƙuri ga dukkanin masoya da magoya baya game da wannan mawuyacin shawarar da na ɗauka; ina kuma musu fatan alkairi baki ɗaya.

“Ina roƙon Allah Subhanahu wata’ala ya saka wa kowa da mafificin alkairi.

“Ya ci gaba da cewa a kowani lokaci a shirya yake wajen ci gaba da taimaka wa al’umma musamman a ɓangaren ilimin da kiwon lafiya.

“Kasancewar na bar siyasa ba zai hanani ci gaba da taimaka wa al’umma ba ta gidauniyata ta Marshal Care Foundation musamman a fannonin ilimi, da kiwon lafiya.”

“A ƙarshe ina sake miƙa godiya ta ga dukkanin al’umma; Allah saka wa kowa da alkairi. Allah ya zaunar da kasa lafiya, Allah ya shiga cikin al’amuranmu baki daya.”

Khalid Idris Doya
+ postsBio
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Yaro Ya Harbe Kansa Har Lahira Bayan Mafarauci Ya Yi Sakaci Da Bindigarsa A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    An Kama Mutane 5 Da Sassan Jikin Ɗan’Adam Za Su Yi Tsafi A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Tsohon Mai Neman Takarar Gwamnan Bauchi, Bala Jibrin, Ya Fice Daga APC Kan Zargin Ɗoki-ɗora
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    ‘Yansanda Sun Cafke Tsoho Mai Shekara 70 Kan Zargin Yi Wa ‘Yar Shekara 8 Fyaɗe A Bauchi

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Tawagogin Sin Da Amurka Masu Tattauna Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya Sun Cimma Sakamako Mai Gamsarwa

Tawagogin Sin Da Amurka Masu Tattauna Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya Sun Cimma Sakamako Mai Gamsarwa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.