Ƙungiyar Reset Nigeria Movement ta taya Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, murna bisa nasarar lashe zaɓen Osun na 2026, tana mai cewa sakamakon ya nuna cewa ikon masu kaɗa ƙuri’a na iya yin nasara duk da matsin lamba da ƙalubalen siyasa.
A cikin wata sanarwa da Ko’odinetan Ƙungiyar na Ƙasa, Osi Iwenekhai, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta yaba wa al’ummar Osun bisa abin da ta bayyana a matsayin jajircewa da ƙarfin hali a lokacin fafutukar siyasar da ta kai ga zaɓen. Ta ce sakamakon ya tunatar da ’yan Nijeriya cewa dimokuraɗiyya mallakin jama’a ce, kuma ƙuri’a ita ce mafi muhimmiyar hanyar da za su yi amfani da ita wajen zaɓar shugabanninsu.
Ƙungiyar ta kuma yaba wa Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, bisa tsayawa tare da Adeleke a lokacin da ta bayyana a matsayin tafiya mai cike da ƙalubale. A cewarta, matakin Makinde ya nuna cewa ƙarfin hali a siyasa ba wai kawai samun nasara a zaɓe ba ne, har ma da kare ƙa’idojin dimokuraɗiyya a lokacin da hakan ke da wahala. Ta kuma tuna da kalamansa cewa zaɓen 2027 ba zai kasance tsakanin PDP da APC kawai ba, sai dai tsakanin ƴan Nijeriya da APC.
Reset Nigeria Movement ta ce sakamakon Osun ya wuce iyakar jihar, domin ya nuna cewa masu zaɓe na iya tsayawa tsayin daka wajen kare zaɓinsu duk da matsin lambar siyasa. Ta buƙaci ƴan Nijeriya su koyi darasi daga Osun gabanin zaɓen 2027, su yi amfani da ƴancinsu na zaɓe ba tare da tsoro, ko barazana ko magudi ba, tare da zaɓar shugabannin da ke da nagarta, da ƙwarewa da kishin yi wa jama’a hidima.
Sai dai ƙungiyar ta kuma yi jimamin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon rikicin siyasa yayin zaɓen, tana mai cewa rasa rayuwar ko mutum ɗaya saboda neman mulki abu ne da bai kamata ya faru ba.
Ta yi kira da a tabbatar da yin bincike da ɗaukar mataki kan masu hannu cikin tashin hankalin, tare da jaddada cewa zaɓe bai kamata ya zama filin daga ba. Ta kuma yi kira ga ƴan Nijeriya su kasance masu faɗaka da jajircewa a 2027.














