ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NDLEA Ta Cafke Wani Dan Kasuwa Mai Shirin Tafiya China A Filin Jirgin Saman Kano Dauke Da Muggan Kwayoyi

by Rabi'u Ali Indabawa and Sulaiman
7 months ago
NDLEA

Jami’an Hukumar Hana Sha da Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) sun kama wani dan kasuwa mai shekaru 62, mai zama a Legas, Nwabueze Izueke, a Filin Jirgin Saman kasa da kasa na Mallam Aminu Kano, bisa zargin cewa ya hadiye Kwallan kwayar Hodar Iblis domin safarar miyagun kwayoyi zuwa China.

An ce Izueke ya hadiye kwallon Hodar Iblis 95 masu girman jumbo da nauyin kilogiram 1.589, wanda ake zargin ya yi domin samun kudin kammala ginin gida a garinsu.

Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa, inda ya kara da cewa wanda ake tuhuma an kama shi ne a ranar Asabar, 31 ga Janairu, 2026, yayin da ake gudanar da bincike kan fasinjoji masu tafiya China ta hanyar Addis Ababa a jirgin Ethiopian Airlines ET940.

ADVERTISEMENT

Babafemi ya ce jami’an NDLEA sun ja hankalin Izueke domin dubawa, suka yi masa body scan, wanda ya nuna cewa ya hadiye miyagun kwayoyi.

“Yayin da ake sa ido a kansa, wanda ke ikirarin cewa yana harkar tufafi da kayan motoci a Legas, ya fitar da kwallen kwayoyi 95 na Class A cikin sau 7,” in ji sanarwar.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

“A cikin bayaninsa, ya ce ya yanke shawarar shiga harkar safarar miyagun kwayoyi ne domin samun kudin kammala gidan kauye da yake ginawa a garinsu, Iwollo, Jihar Enugu.”

Kamar yadda NDLEA ta bayyana, wannan kama shi ya kasance wani bangare ne na jerin ayyukan tsaro na kasa baki daya, wanda ya kai ga kwato miyagun kwayoyi da kamawa a jihohi da dama.

A Abuja, jami’an NDLEA sun kwato kilogiram 627.7 na skunk, wani nau’in tabar wiwi, daga wani wuri a Fums Plaza, Kubwa.

Hakanan an hana yunkurin safarar methamphetamine da aka boye a cikin lasifikar MP3 daga Enugu zuwa Abuja da Kaduna.

An kama mutane hudu Ebube Okeke, Ebans Ugwu, Mohammed Eze Arinze da Friday Michael a kan wannan safarar miyagun kwayoyi. Babafemi ya ce, daga bisani an sake kama Okeke a Zuba, yayin da sauran ukun suka bayyana a Kaduna domin karbar kayan miyagun kwayoyi.

A Jihar Taraba, jami’an sun kama wani wanda ake zargi yana safarar methamphetamine da aka boye a cikin kwalin yogurt.

A Jihar Oyo, an kama wasu mutane da dama, ciki har da wani babban mai safarar miyagun kwayoyi da ake zargin yana gudanar da wani wurin samar da Colorado, wani nau’in tabar wiwi na roba.

A Ibadan, an kwato abubuwa da dama, ciki har da: Ampoules 10,820 na pentazocine injection Capsules 117,820 na tramadol. Sinadaran hada kwayoyi, skunk da sauran kayan aiki na samar da kwayoyi, Naira miliyan 7.4 a hannu da motoci 2.

A Jihar Imo, an kama ma’aurata Izuchukwu Azubuike, mai shakara 37, da Ifunaya Mmadueke, 32, tare da kilogiram 203 na skunk, yayin da jami’an NDLEA a Jihar Ondo suka kwato kilogiram 420 na wannan kayan daga wani daji a Ikun Akoko.

Babafemi ya jaddada cewa NDLEA za ta ci gaba da yaki da harkokin safarar miyagun kwayoyi a fadin kasa.

A takaice, jami’an NDLEA sun samu nasarar hana safarar miyagun kwayoyi da dama, sun kuma ci gaba da gudanar da ayyukan sintiri da gano masu safarar kwayoyi a jihohi daban-daban.

A Jihar Taraba, jami’an sun kama wani wanda ake zargin yana safarar methamphetamine da aka boye a cikin paket na yogurt.

A Jihar Oyo, jami’an sun kama mutane da dama, ciki har da wani babban mai miyagun kwayoyi da ake zargin yana gudanar da wani wurin samar da Colorado, wani nau’in tabar wiwi na roba.

NDLEA
Rabi'u Ali Indabawa
+ posts Bio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas
NDLEA
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
An Gabatar Da Bikin Share Fagen Shirin Talibijin Na Murnar Sabuwar Shekarar Sinawa A Masar 

An Gabatar Da Bikin Share Fagen Shirin Talibijin Na Murnar Sabuwar Shekarar Sinawa A Masar 

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.