ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ni Yanzu Ɗan Siyasa Ne Mai Zaman Kansa, Ina Damar Alaƙa Da Kowace Jam’iyya – Gwamnan Bauchi

by Khalid Idris Doya
5 months ago

Daga Khalid Idris Doya Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana cewar yanzu haka shi ɗan siyasa ne mai zaman kansa wanda ke da damar alaƙa da kowace jam’iyyar siyasa a faɗin ƙasar nan domin ganin an ceto Nijeriya daga halin da ta ke ciki.

Bala, wanda ya shaida hakan a lokacin da ya amshi baƙwancinsa jigo a jam’iyyar ADC, Mista Peter Obi a gidan gwamnatin jihar Bauchi ranar Alhamis, bayan sun yi ganawar sirri, inda ya wa ‘yan jarida cewa, jam’iyyarsa ta PDP a halin yanzu tana cikin wani hali da suke zaman jiran hukuncin kotun domin sanin matsayarsu.

Don haka ya ce, a shirye yake ya hada kai da kowace jam’iyya domin ganin an ceto Nijeriya. Gwamna Bala Mohammed ya ce magance manyan ƙalubalen Najeriya na buƙatar haɗin kai.Ya bayyana cewa ganawar da suka yi da Obi ta mayar da hankali ne kan haɗin kan ƙasa da kuma aiki tare, yana mai jaddada cewa ba a gudanar da ita bisa son rai na jam’iyya ba.”Tabbas, dukkanmu muna cikin ɓangaren adawa, shi ya sa na kira wannan tattaunawa ta siyasa.

ADVERTISEMENT

Amma ba za mu bayyana muku duk abin da aka tattauna ba,” in ji shi.Ya kara da cewa tattaunawar tana da nufin neman haɗa kai domin samar da tsarin da za su tunƙari zaɓen 2027.”Dole sai da jam’iyyar siyasa za mu hada ƙarfi waje guda,” don haka ne ya ce suna ci gaba da tattauna yanayin siyasar da kuma inda za su haɗu wato jam’iyya guda da nufin ceto Nijeriya daga halin ni’yasu.

Bala Mohammed ya bayyana ziyarar Obi a matsayin wata alama ta ƙoƙarin kyautata alaka tsakanin yankuna, yana mai cewa, “Wannan ziyara ta shafi haɗin gwiwa, aiki tare, da sake gina ƙasa domin dawo da daidaiton iko da magabatanmu suka kafa, wanda daga baya aka yi watsi da shi.

LABARAI MASU NASABA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

“Ya kuma lura cewa jam’iyyun adawa na duba yiwuwar ƙulla kawance na dabaru.Tun da farko, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023 kuma tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki daga yankin Kudu maso Gabas, Arewa maso Gabas, da sauran yankuna da su haɗa kai domin sake gina Nijeriya.

Obi ya roƙi Bala da sauran masu ruwa da tsaki da su yi aiki tare domin ci gaban ƙasa da kuma ceto ta daga rugujewa.Ya bayyana cewa ziyarar na da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa da zumunci tsakanin shugabanni daga yankuna daban-daban, musamman a Arewa maso Gabas.

“Munaso mu gina ƙasa mai haɗin kai domin makomar ‘ya’yanmu. Nijeriya ba za ta iya ci gaba da tafiya a wannan yanayin ba; muna kan hanyar da ba ta dace ba kuma dole mu gyara hakan domin amfanuwar kowannenmu” in ji shi.Ya jaddada cewa kishin ƙasa ya kamata ya fi fifiko a kan alaƙar jam’iyya, yana mai cewa matsaloli kamar rashin tsaro da tashin farashin abinci na shafar dukkan ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da jam’iyya, ƙabila ko addini ba.

“Babu wata jam’iyya da ke sa abinci ya yi araha a kasuwa. Babu wata ƙabila ko addini da ke sayen burodi a farashi mai sauƙi fiye da wasu. Abin da ya fi muhimmanci shi ne tabbatar da tsaro da inganta rayuwar ‘yan Nijeriya,” ya ƙara da cewa.Obi, wanda jigo ne a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya jaddada cewa idan rashin tsaro ya afku, ko ta hanyar garkuwa da mutane ko tashin hankali, ba a bambanta waɗanda abin ya shafa da jam’iyya ko ƙabila, yana mai nuna gaggawar ɗaukar matakin gama-gari.

Obi ya je ziyarar tare da wasu fitattun ‘yan siyasa daga Kudu maso Gabas, ciki har da tsohon gwamnan Jihar Imo, Achike Udenwa, Ben Obi, Sanata Enyinnaya Abaribe, Sanata Victor Umeh, Farfesa Udenta O. Udenta, da Tanko Yunusa, da sauransu.

Khalid Idris Doya
+ postsBio
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Yaro Ya Harbe Kansa Har Lahira Bayan Mafarauci Ya Yi Sakaci Da Bindigarsa A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    An Kama Mutane 5 Da Sassan Jikin Ɗan’Adam Za Su Yi Tsafi A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Tsohon Mai Neman Takarar Gwamnan Bauchi, Bala Jibrin, Ya Fice Daga APC Kan Zargin Ɗoki-ɗora

MASU ALAKA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna
Siyasa

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

September 9, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Next Post
Yadda Fasahar Mutum-Mutumin Inji Ke Kara Shiga Fannonin Rayuwa A Kasar Sin

Yadda Fasahar Mutum-Mutumin Inji Ke Kara Shiga Fannonin Rayuwa A Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.