Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sabon shirin da ke da nufin jawo dala biliyan 12 na zuba jari daga kasuwar tattalin arziƙin halal ta duniya da darajarta ta kai kusan dala tiriliyan 7. Gwamnatin ta ce tana son Nijeriya ta zama ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da ke samar da kayayyaki da ayyukan halal, tare da ƙirƙirar ayyukan yi da ƙara fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ne ya bayyana hakan a Legas yayin taron Lagos Halal Leadership Reception 2026, inda ƙaramin Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Dakta Doris Uzoka-Anite, ta wakilce shi. Ya ce Nijeriya ba za ta iya ci gaba da kasancewa mai sayen kayayyakin halal kawai ba yayin da wasu ƙasashe ke cin moriyar mafi yawan kuɗaɗen da ake samu daga wannan babbar kasuwa ba.
Shettima ya ce tattalin arziƙin halal ya wuce harkar abinci da abin sha, domin yanzu ya haɗa da kuɗaɗen Musulunci, da magunguna, da kayan kwalliya, da fannin yawon buɗe ido, da sufuri, da masana’antu da kasuwancin dijital.
Ya ce yawan al’ummar Nijeriya, da albarkatun noma da kiwo, da ƙarfin ‘yan kasuwa da kuma matsayinta a Afirka na ba ta damar samun babban kaso daga kasuwar. Ya bayyana cewa Kwamitin Aiwatar da Dabarun Tattalin Arziƙin Halal na Nijeriya da aka ƙaddamar a ranar 3 ga Maris, 2026, ya tsara wasu rukuni 13 na aiwatar da shirin tare da burin tara sama da dala biliyan 12 na zuba jari.
Gwamnatin ta kuma ce tana tattaunawa da Islamic Development Bank, BADEA, D8 Halal Forum da sauran ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa domin ƙarfafa shirin. Jihohin Osun, Katsina da Kano sun kuma nuna sha’awar aiwatar da dabarun a matakin jiha, yayin da ake shirin miƙa Tsarin Gudanarwa, Alamar Halal ta Ƙasa da dandalin tantancewa da tabbatar da halal ga Majalisar Zartarwa ta Tarayya domin amincewa.
Sai dai Shettima ya jaddada cewa manufofi da yarjejeniyoyi kaɗai ba za su isa ba idan ba su haifar da kasuwanci, da zuba jari, ko fitar da kayayyaki da ayyukan yi ba. Ya buƙaci masana’antu, da bankuna, da fannoni masu sufuri, da manoma da ‘yan kasuwar yawon buɗe ido da fasaha su ɗauki takardar shaidar halal da tsarin bin diddigi a matsayin hanyar shiga kasuwannin duniya, yayin da NACCIMA da sauran masu ruwa da tsaki suka buƙaci Nijeriya ta daina tsaya wa kan tattaunawa kawai, ta koma aiwatar da manufofin da za su bunƙasa sarrafa albarkatun ƙasa da kuma ƙara darajar kayayyakin da ake samarwa a cikin gida.














