Rundunar Sojin Nijeriya ta tura jami’anta 86 zuwa ƙasar Guinea-Bissau domin shiga aikin samar da zaman lafiya ƙarƙashin ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS).
A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce sojojin sun tashi daga filin jirgin sama na Abuja kuma sun isa Guinea-Bissau lafiya, inda za su fara aikinsu.
Ta ce tura sojojin na nuna yadda Nijeriya ke ci gaba da ba da gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a ƙasashen Yammacin Afirka.
Rundunar ta ƙara da cewa Nijeriya na daga cikin ƙasashen Afirka da suka fi bayar da gudunmawa a ayyukan wanzar da zaman lafiya na ECOWAS, Tarayyar Afirka da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya.
A cewarta, wannan aiki zai taimaka wajen ƙarfafa tsaro, inganta zaman lafiya da kuma tabbatar da kwanciyar hankali a Guinea-Bissau, ƙasar da ta sha fama da rikicin siyasa da juyin mulkin soja.
Nijeriya ta daɗe tana tura sojoji zuwa irin waɗannan ayyuka a ƙasashe kamar Liberiya, Saliyo, Gambiya da Guinea-Bissau.
Tura sabbin sojojin na zuwa ne yayin da Nijeriya ke ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro a wasu sassan ƙasar, ciki har da hare-haren ‘yan bindiga da sace mutane domin neman kuɗin fansa.














