ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Remi Tinubu Ta Kaddamar Da Raba Tireloli 100 Na Shinkafa da Tallafin Naira Biliyan 1.2 Ga Jihohin Arewa

by Sulaiman and Shehu Yahaya
4 months ago
Remi

Uwargidar shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta kaddamar da shirin rabon tireloli 100 na shinkafa tare da tallafin kudi na naira biliyan 1.2 ga Malaman addini da marasa karfi a jihohi 19 na Arewacin Nijeriya domin hidimar Babbar Sallah.

Shirin Wanda ofishinsa uwargidar shugaban Kasa Oluremi Tinubu da ofishin Mataimaki na musamman ga shugaban Kasa akan harkokin siyasa suka jagoranta ya samu halarcin dubban Malaman addini da kungiyoyi daga jihohi 19 na Arewacin kasar nan da birnin tarayya Abuja Wanda ya guda a dakin taro na gidan gwanatin Kaduna.

Da yake jawabi yayi taron Mataimaki Na musamman ga shugaban kasa kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabiru Masari, ya bayyana cewa shirin ya kunshi raba tallafi ga limamai da na’ibansu da malaman Islamiyya da na tsangayu da kungiyoyin nakassu da marayu da sauran marasa galihu a yankin Arewa.

ADVERTISEMENT
Remi

Masari ya kara da cewa an tsara tsarin rabon yadda zai tabbatar da cewa kowa ya amfana cikin adalci, inda kowace jiha za ta samu tirelan shinkafa guda hudu domin rabawa mabukata.A nasa jawabin Shugaban shirye-shiryen shirin bayar da tallafin Aminu Sani Jaji, ya jaddada muhimmancin taimakon juna, yana mai ambato hadisin Manzon Allah (SAW) da ke karfafa rabon abin da mutum ke so wa kansa ga ‘yan uwansa.

Yace uwargidar shugaban Kasa Oluremi Tinubu mai kishin ci gaba Arewa ce inda yace lokaci yayi da al’ummar yankin Arewa zasu sake marawa shugaban Kasa Bola Tinubu domin ganin ya dawo Kato biyu a zaben 227.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Shi ma Sheikh Halliru Maraya wanda yake wakiltar Malaman addini a taron,ya bayyana cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta kawo gagarumin ci gaba a yankin Arewa, wanda ya sa al’ummar yankin ke shirin ci gaba da mara masa baya a zaben 2027.

Ya kara da cewa ‘yan Arewa ne za su taka rawar gani wajen tabbatar da sake tsayawar Tinubu takara, yana mai cewa za su bashi goyon bayan da ya kamata domin dawowarsa mulki a zabe mai zuwa.

A cewarsa, gwamnatin Tinubu ta bai wa yankin Arewa muhimmanci ta hanyar raba mukamai da dama, ciki har da mukamin Ministan tsaro da Ministan Noma da Ministan Kasafi, wadanda duk ‘yan Arewa ne.Haka kuma, ya ce cikin kasa da shekaru uku gwamnatin ta samar da sabbin jami’o’i har guda 23, tare da rage kudin aikin hajji domin saukaka wa al’umma.

Shirin rabon tallafin na daga cikin kokarin gwamnati na rage radadin talauci da tallafa wa al’ummar da ke cikin bukata musamman a yankin Arewa.

Remi
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
Remi
Shehu Yahaya
+ posts Bio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamna Uba Sani Ya Yi Jimamin Rasuwar Dan Jarida Jafaru Yakubu Maitama
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamnatin Kaduna Ta Fara Rabon Takin Zamani Kyauta Ga Manoma 150,000
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Zaka Iya Sayar da Takin Gwamnati Ka Sayawa Iyalinka Kaji — Imam Nuradden
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Rashin Tsaro: ACI Zata Kira Taron Gaggawa Na Masu Ruwa Da Tsaki A Kaduna

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
Wakilin Sin Ya Bayyana Matsayin Kasa A Yayin Taron Nazarin Yarjejeniyar Hana Yaduwar Makaman Nukiliya Karo Na 11

Wakilin Sin Ya Bayyana Matsayin Kasa A Yayin Taron Nazarin Yarjejeniyar Hana Yaduwar Makaman Nukiliya Karo Na 11

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.