ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rikicin Kabilanci A Jihar Ribas Ya Tayar Da Hankalin Al’umma

by Sani Anwar and Sulaiman
7 months ago
Ribas

An lalata kayayyaki na miliyoyin naira, biyo bayan zanga-zangar da ‘yan Arewa suka yi a garin Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas, kan kisan wani mazaunin garin Igwuruta da ke Karamar Hukumar Ikwerre da ake zargin wani dan AcaBa ya yi.

An tattaro cewa, Nchelem Samuel Festus, dan asalin Igwuruta ne, wanda aka samu da laifin satar babur a wani shago mallakin ‘yan Arewa. Yayin da ake kokarin kwato babur din, an ce an caka masa wuka, inda daga bisani kuma ya mutu.

  • Kisan Ƙare Dangi: Sojojin Amurka Sun Fara Aikin Samar Da Tsaro A Nijeriya
  • Makomar Nijeriya Na Hannun FIFA – Shehu Dikko

Lamarin, wanda ya faru a ranar 10 ga watan Fabrairu, ya haifar da zanga-zanga, inda masu zanga-zangar ke zargin cewa; ‘yan Arewa ne da ke sana’ar tuka babur (AcaBa) ke da alhakin mutuwar ta Festus.

ADVERTISEMENT

Har ila yau, masu zanga-zangar, sun ci gaba da zargin ’yan Arewar da hannu a wasu laifuka da suka hada da fyade da kuma garkuwa da mutane.

Rikicin dai, ya ta’azzara ne yayin da matasa suka tare titin filin jirgin sama na Fatakwal, inda suka bukaci da a gaggauta dakatar da zirga-zirgar ‘yan AcaBa daga Arewa a yankin.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Sun kuma yi kira da a rufe wuraren zubar da shara da ake zargin ’yan Arewan, a kuma kama tare da hukunta wadanda ke da hannu a kisan na Festus, da kuma hana makiyaya shiga gonakin mutane da suke yi.

Masu zanga-zangar, sun bayar da wa’adin sa’o’i 48 ga hukumomin tsaro, inda suka yi gargadin cewa; rashin biyan bukatunsu na iya tilastawa al’umma daukar matakan kare rayuka da dukiyoyi, tare da tabbatar da cewa; matakin nasu zai kasance a cikin tsarin doka da oda.

Tashin hankalin ya yi kamari ne a ranar Asabar da ta gabata, yayin da wani mai tura Baro, mai suna Zakara Afaaruwu ya daBa wa wani dan kasuwa mai suna Higightor Wenem daga Jihar Benuwe wuka har lahira, a lokacin da suke takaddama a Fatakwal.

Lamarin dai ya haifar da wani sabon rikici, wanda ya kai ga sake kai hare-hare a kan ‘yan kasuwar Arewacin kasar a Igwuruta, inda aka yi ta’adi a wasu kasuwanni tare da yin sace-sace.

“Kada ku danganta ’yan Arewa da wasu keBantattun laifuka.”

Shugaban al’ummar Hausawa a Jihar Ribas, Malam Musa Saidu, ya bayyana matukar bakin cikinsa, kan kashe-kashen da aka yi, ya kuma yi gargadin a guji alakanta aikata laifuka da al’ummar Hausawa ko wata kabila daban.

Ya ce, “An samu rashin fahimtar juna ne a tsakanin wani yaro dan Arewa da kuma wani dan garin Igwuruta, wanda abin takaici ya yi sanadin mutuwar wasu mutane, kamar yadda ni ma na samu bayani, saboda ni kaina ban je wurin ba, an ce; yaron Arewan ya daBa wa yaron garin wuka, har ya mutu, hakan ya sa aka yi wannan zanga-zanga, amma zanga-zangar ita ce; ta Hausawa su fita daga garin, idan wani ya yi laifi, hukuma ce ya kamata ta kama shi, jami’an tsaro su gurfanar da shi, amma mene ne dalilin yin zanga-zanga tare da neman Hausawa su bar garin?

“Rokona ga ’yan’uwanmu maza da mata a Jihar Ribas, ‘yan asalin jihar da wadanda ba ‘yan asalin jihar ba shi ne, mu yi hakuri da abin da ya faru, mu ba masu tayar da hankali ba ne, duk wanda ya aikata laifi doka ta dauki mataki akansa, yin zanga-zangar adawa da al’umma gaba-daya tamkar kiyayya ce, kuma kiyayya na iya haifar da karin tashin hankali,” in ji shi.

Ribas
Sani Anwar
+ posts Bio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta
Ribas
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya Da Gwamnonin APC Sun Ba Da Gudummawar Naira Biliyan 8 Ga ‘Yan Kasuwar Singa

Gwamnatin Tarayya Da Gwamnonin APC Sun Ba Da Gudummawar Naira Biliyan 8 Ga ‘Yan Kasuwar Singa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.