Sakataren Yaɗa Labaran Jam’iyyar ADC a Jihar Gombe, Abdulrahman Buba Zaune, ya yi murabus daga jam’iyyar nan take.
A cikin wasiƙar murabus ɗinsa mai ɗauke da kwanan watan ranar 5 ga watan Agusta, 2026, wadda ya aike wa shugaban jam’iyyar na mazaɓar Zaune da ke Ƙaramar Hukumar Dukku, Zaune ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi na yin aiki a matakin ƙaramar hukuma, jiha da ƙasa.
“Ina miƙa godiyata ga jam’iyyar bisa damar da ta ba ni na yin aiki a matakai daban-daban na ƙaramar hukuma, jiha da ƙasa. Ina yi wa jam’iyyar fatan alheri a nan gaba,” in ji shi.
Murabus ɗin nasa ya haifar da hasashen cewa yana iya komawa Jam’iyyar APC nan ba da jimawa ba.
Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan ɗan takarar gwamnan APC a Jihar Gombe, Jamilu Isiyaka Gwamna, ya kai ziyara Ƙaramar Hukumar Dukku.
Murabus ɗin Zaune ta kuma biyo bayan ficewar Sakataren Jam’iyyar ADC na Jihar Gombe, Ahmed Gana, wanda ya koma APC.
Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa wannan sauyin na iya ƙara wa APC ƙarfi a Jihar Gombe gabanin zaɓe mai zuwa.














