ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sakon Da Aka Isar Bisa Yadda Zimbabwe Ta Fitar Da Sinadarin Lithium Sulfate Da Ta Sarrafa A Gida Zuwa Ketare

by CGTN Hausa and Sulaiman
4 months ago
Lithium

Kwanan nan, an samun labari mai muhimmanci daga Zimbabwe da ke canza tarihin bunkasar ma’adinai a Afirka. A karkashin taimakon kamfanonin Sin, a karon farko ne nahiyar Afirka ta samu nasarar fitar da sinadarin Lithium Sulfate da aka sarrafa a cikin gida. Wannan gagarumin ci gaba ne da Zimbabwe ta samu wajen fita daga kangin “hako ma’adinai kawai, ba tare da sarrafa su ba”, kuma sabon ci gaba ne da Sin ta samu a tarihi wajen taimaka wa kasashen Afirka dogaro da karfinsu don sarrafa ma’adinai da kuma fitar da su.

Allah ya albarci Afirka da albarkatun ma’adanai masu dimbin yawa a duniya, amma tun da dadewa, Afirka ta sha wahala wajen mayar da fa’idar albarkatun zuwa fa’idar ci gaba, har ma ta dade tana fuskantar matsalar “fitar da albarkatun kasa ba tare da riba mai dacewa ba”, sakamakon irin tsarin hako ma’adinai da Turawan yamma suka aiwatar a nahiyar.

Wannan gagarumin ci gaban hadin gwiwar Sin da Afirka ya ba da damar canza wannan yanayin, inda kamfanonin kasar Sin suka tsara jerin sana’o’i masu alaka a cikin gidan Zimbabwe, wanda ya baiwa Afirka damar samun kwaskwarima a bangaren sarrafa ma’adinin Lithium ya zama Lithium Sulfate, wanda ya kawo karshen tarihin Afirka na fitar da ma’adinan da aka hako ba tare da sarrafa su ba da kuma rashin ikon magana a harkar masana’antu.

ADVERTISEMENT

Don haka ma, Farfesa Carlos Lopes daga kwalejin nazarin mulki ta Nelson Mandela ta jami’ar Cape Town a kasar Afirka ta kudu ya ce, nasarar fitar da sinadarin Lithium Sulfate yana da matukar ma’ana, wanda ke nuna cewa Afirka ta yi ban kwana da tsohon tsarin hadin gwiwa iri yadda kasashen yamma ke kwace albarkatunta, kuma ba za ta kasance wurin samar da albarkatu kawai ba, kana ta sauya yanayinta na dogaro da jarin waje.Hakika darajar wannan ci gaba ta wuce batun kasuwanci, kuma alama ce da ke nuna hadin gwiwar Sin da Afirka ta shiga sabon mataki.

A baya, hadin gwiwar Sin da Afirka ya fi mayar da hankali kan “hadin gwiwar ababen more rayuwa” kamar hanyoyi da tashoshin wutar lantarki da tashoshin jiragen ruwa. Aikin sarrafa sinadarin Lithium da Sin da Zimbabwe suke yi cikin hadin gwiwa a wannan karo, alama ce da ke nuna yadda hadin gwiwar bangarorin biyu ya shiga sabon mataki na zurfafa hadewar masana’antu. Abin da bangaren Sin ya fitar ba jari ba ne kawai, cikakken tsari ne dake hada fasaha mai muhimmanci da ma’auni da tsarin samar da kayayyaki, kana da kasuwanni.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Yanzu haka Zimbabwe na mallakar wani muhimmin bangare na samar da sabbin makamashi ta sinadarin Lithium, duba da cewa tana da tsarin da ke iya samar da sinadarin Lithium Sulfate har tan 50,000 a ko wace shekara, matakin da ya sa ta iya shawarwari da tsai da farashin sinadarin a kasuwannin duniya.

A halin yanzu, yawancin kasashe masu tasowa suna neman kubuta daga kangin da suke ciki na fitar da albarkatunsu da ba a sarrafa ba, da daga matsayinsu a tsarin masana’antu a duniya. Nasarar da Zimbabwe da Sin suka samu a wannan karo, ba wai kawai tarihi ne na ci gaban masana’antun ma’adinai ta Afirka ba, har ma ta kasance wani sako da kasashe masu tasowa ke aikewa cikin hadin kai na kawar da yanayin maras adalci da Turawan yamma ke jagoranta, da tabbatar da makomarsu tare da gina tsarin tattalin arziki na duniya mafi adalci.(Marubuciya: MINA)

Lithium
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030
Lithium
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Xi Ya Gana Da Modi A New Delhi
  • Sulaiman
    2027: Masana Sun Yi Gargaɗi Game Da Bangar Siyasa Da Kalaman Ɓatanci
  • Sulaiman
    Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa
  • Sulaiman
    Abinda Kasafin Gwamna Raɗɗa Na Shekarar 2027 Ya Ƙunsa

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
INEC Ta Kara Wa’adin Karbar Katin Zabe

Kotu Ta Tabbatar INEC Na Da Ikon Fitar Da Jadawalin Zaɓe

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Gana Da Modi A New Delhi

Xi Ya Gana Da Modi A New Delhi

September 12, 2026
2027: Masana Sun Yi Gargaɗi Game Da Bangar Siyasa Da Kalaman Ɓatanci

2027: Masana Sun Yi Gargaɗi Game Da Bangar Siyasa Da Kalaman Ɓatanci

September 12, 2026
Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa

Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa

September 12, 2026
Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan

Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan

September 12, 2026
Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

September 12, 2026
Gwamnatin Katsina

Abinda Kasafin Gwamna Raɗɗa Na Shekarar 2027 Ya Ƙunsa

September 12, 2026
Ɗalibai Sun Yi Watsi Da Tallafin Data, Sun Nemi Wi-Fi Kyauta A Makarantu Daga Gwamnati

Ɗalibai Sun Yi Watsi Da Tallafin Data, Sun Nemi Wi-Fi Kyauta A Makarantu Daga Gwamnati

September 12, 2026
Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

September 12, 2026
Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

September 12, 2026
An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

September 12, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.