A ranar 30 ga Yuli, 2026, Ma’aikatar Tsaro ta Tarayya ta shirya taron farko na Tsaro na Yankin Kudu maso Gabas a Umuahia, Jihar Abia, domin tattaunawa da amincewa da dabaru daban-daban ba na amfani da karfin soja ba (non-kinetic strategies) wajen magance matsalolin tsaro a yankin Kudu maso Gabas.
Wannan shi ne taro na farko cikin jerin tarurrukan da aka tsara gudanarwa a dukkan shiyyoyin siyasar kasar.
An zabi fara wannan shiri a yankin Kudu maso Gabas ne bisa wata manufa ta musamman, domin isar da sako mai karfi ga wadanda ke haddasa rashin tsaro a yankin cewa, daga yanzu, za a fara wani sabon zamani na maido da zaman lafiya a kasar Igbo (Igboland).
Wadannan su ne tunanina, kuma sun samo asali ne daga cikakken kudurina na tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya.
Mun zabi fara wannan shiri ne da yankin Kudu maso Gabas, domin yanki ne mai matukar muhimmanci kuma mai manyan damarmaki ga ci gaban kasa.
Hakan ya samo asali ne daga yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke da kwazo da jajircewa wajen tabbatar da dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, baya ga manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa da ake aiwatarwa.
A Ma’aikatar Tsaro, mun fahimci cewa tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankin Kudu maso Gabas yana da matukar muhimmanci domin samar da ci gaba da bunkasar tattalin arziki da rayuwar al’umma.
Taken taron shi ne “Hadin Gwiwa Wajen Karfafa Tsaro da Zaman Lafiya a Yanki.” Wannan jigo ya nuna muhimmancin aiki tare, tare da tabbatar da karin maganar da ke cewa “Hannu daya ba ya daukar jinka,” wato hadin kai ya fi karfin mutum daya.
Haka kuma ya tabbatar da cewa cin nasarar yaki da rashin tsaro na bukatar hada dabarun amfani da karfin soja (kinetic) da kuma dabarun zaman lafiya da tattaunawa.
Na yi matukar farin ciki da irin yawan mahalarta taron, wadanda suka hada da sarakunan gargajiya, shugabannin siyasa da na gwamnati, malaman addinai, kungiyoyin kwadago, kungiyoyin matasa, jami’an tsaro da na tattara bayanan sirri, malamai, dalibai, masu sana’o’in hannu da sauran jama’a, har da tsofaffin sojoji daga yankin.
Na gamsu kwarai da irin jawabai da gabatarwar da aka yi a taron. Na lura da irin kuduri da jajircewar da mahalarta taron suka nuna, wanda ba kasafai ake samu ba.
Tattaunawar ta fi mayar da hankali kan hanyoyin da za a bi domin magance matsalolin tsaro da tabbatar da makoma mai kyau.Haka kuma, taron ya ba ni damar fahimtar ainihin yanayin matsalolin tsaro da ke addabar yankin Kudu maso Gabas kai tsaye.
A matsayina na Ministan Tsaro, hakan ya kara mini fahimta sosai, wadda za ta taimaka wajen tsara manufofin tsaro na gaba a Nijeriya.
Wannan alkawari ne da nake yi.
Darusa daga dattawa
Shugabana, mai ba ni shawara kuma tamkar uba a gare ni, Janar Ike Omar Sanda Nwachukwu, GCMG, CFR, COM, psc+, mni, finiia, da sauran manyan mukamai da karramawa da yake da su, ya halarci taron, lamarin da ya kara wa taron armashi da daraja.
Jawabin da ya gabatar ya tabo muhimmin jigon hadin gwiwa wajen karfafa tsaro da tabbatar da zaman lafiya a yankuna. Babban darasin da na koya daga jawabinsa shi ne cewa:”Amfani da karfin soja yana da matukar muhimmanci, amma karfin soja kadai bai taba warware matsalar siyasa, tattalin arziki ko zamantakewa har abada ba.”
Ya kuma jaddada cewa alhakin tabbatar da tsaro bai kamata ya kasance na Rundunar Sojoji ko sauran hukumomin tsaro kadai ba.
A cewarsa, ana samun nasara a fannin tsaro ne idan al’umma sun zama masu taka rawa a ciki, ba masu kallo kawai ba.Ina mika godiyata ta musamman ga Janar Nwachukwu bisa ware lokacinsa mai daraja domin halartar wannan taro.
Mun yaba matuka da wannan karamci da gudummawar da ya bayar.
Shugabana kuma tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Onyeabo Azubuike Ihejirika, CFR, ya faranta min rai kwarai da halartar da ya yi taron, da kuma ingantaccen jawabin da ya gabatar a matsayin babban mai gabatar da jawabi.
Kamar yadda aka saba da shi, ya yi jawabi cikin hikima da kwarewa, inda ya jaddada muhimmancin cewa: “Ya kamata a auna nasarar kowace hukuma ba kawai da irin nasarorin da ta samu a ayyukanta ba, amma da irin yadda jama’a ke more ‘yanci, samun kwarin gwiwa da kuma rayuwa cikin kwanciyar hankali da tabbas a harkokinsu na yau da kullum.
Sai dai cimma hakan na bukatar cikakkiyar fahimta game da barazanar tsaro, hanyoyin sadarwar masu aikata laifi da kuma yanayin da ke ci gaba da kawo cikas ga zaman lafiya da harkokin yau da kullum a yankin.”
Ya kammala jawabinsa da wata muhimmiyar hikima inda ya ce: “Domin hadin gwiwa ya samar da sakamako mai ma’ana, dole ne ya fara ne da fahimtar barazanar da ake fuskanta iri daya kuma daidai.
Idan ba a samu fahimta ta bai daya game da matsalar ba, hukumomi na iya bin manufofi mabambanta, su maimaita ayyuka iri daya, ko kuma su dauki matakan da ba za su magance ainihin tushen matsalar ba.
“Wannan sako ya kasance a sarari kuma mahalarta taron sun karbe shi da zuciya daya.Ina amfani da wannan dama wajen mika godiyata ta musamman gare shi bisa halartar taron da kuma gudummawar ilimi da gogewa da ya bayar.
Ba zan manta da ambaton dan’uwana kuma abokina, Gwamnan Jihar Abia, Dr. Aled Otti, ba, wanda ya kasance mai masaukin baki na kwarai. Ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar wannan taro.
Gudummawar da ya bayar ta kasance mai matukar amfani, kuma kasancewarsa tare da mu tun daga farkon taron har zuwa karshe ya nuna cewa shi abokin hadin gwiwa ne na gaskiya wajen kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Kudu maso Gabas.
Hakazalika, wakilan sauran gwamnonin jihohin Kudu maso Gabas da suka halarci taron sun kara wa taron armashi, tare da bayar da gudummawa mai muhimmanci ta hanyar shawarwari da ra’ayoyinsu masu amfani.
Alhaki ne da ya rataya a wuyan kowaTaron farko na Tsaro na Yankin Kudu maso Gabas ya kasance cikin nasara.
Hakan ya fito fili a cikin sanarwar da aka fitar bayan taron, inda mahalarta suka sake jaddada muhimmancin ci gaba da hadin gwiwa tsakanin duk masu ruwa da tsaki a yankin domin tabbatar da zaman lafiya, tsaro da ci gaba mai dorewa a Kudu maso Gabas.
Wannan ya ba ni kwarin gwiwa, kuma na bar Umuahia da tabbacin cewa masu ruwa da tsaki a yankin sun yanke shawarar daukar nauyin aiwatar da shirye-shiryen tsaro da aka samar domin tabbatar da dorewar zaman lafiya da tsaro.
Irin wannan hadin gwiwa ne muke nema a Ma’aikatar Tsaro, ba a yankin Kudu maso Gabas kadai ba, har ma a sauran yankunan Nijeriya.
Samun ra’ayoyi kai tsaye daga jama’a yana da matukar muhimmanci, domin babu wata dabara guda daya da za ta iya magance matsalolin tsaro a duk fadin Nijeriya.
Nijeriya kasa ce mai yawan al’adu da bambance-bambance, kuma abubuwan da ke haddasa rashin tsaro sun bambanta daga yanki zuwa wani.
Saboda haka, hanya mafi dacewa ita ce a tattaro duk masu ruwa da tsaki domin jin ra’ayoyinsu.
Hakan ma za a iya kwatanta shi da taron tattaunawa da jama’a (Town Hall Meeting), domin babu wata takurawa kan wadanda za su halarta.
An tsara taron ne ta yadda ya hada mutane daga kowane bangare na al’umma, domin tattara ra’ayoyi da shawarwari masu yawa kamar yadda aka bayyana tun farko.Tsaro alhakin kowa ne.
Wannan ita ce gaskiyar da dole mu runguma, kuma shi ne dalilin da ya sa muke daukar hanyar hadin gwiwa wajen karfafa tsaro da zaman lafiya a yankuna daban-daban na kasar nan.
Da wannan tsari, muna kaddamar da sabon salo na tunkarar matsalolin tsaro, wato tsarin “Whole-of-Society Approach” (Hanyar da ke hada dukkan sassan al’umma), wanda Ma’aikatar Tsaro ta runguma a karkashin jagorancina domin magance kalubalen tsaron kasa.
Babban abin da ya fito daga taron, kamar yadda aka bayyana a cikin sanarwar bayan taron, shi ne, amincewar cewa jihohi biyar na Kudu maso Gabas su yi aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro da na tattara bayanan sirri na gwamnatin tarayya domin karfafa hadin kai da samar da ingantattun hanyoyin magance barazanar tsaro da ke wuce iyakokin jihohi.
Haka kuma, an dora wa hukumomin tsaro alhakin kara karfafa hulda da al’ummomi ta hanyar tattaunawa, gina amincewa tsakanin jama’a da hukumomin tsaro, da kuma aiwatar da shirye-shiryen hadin gwiwa tsakanin fararen hula da sojoji domin karfafa amincewar jama’a da kuma sa su taka rawa wajen tabbatar da tsaro.
Wannan shi ne ainihin manufar hadin gwiwa wajen gina ingantaccen tsarin tsaro a kasar nan.
Godiya Ta MusammanMataki na gaba shi ne yankin Arewa ta Tsakiya (North Central), sannan kuma za a ci gaba da gudanar da irin wannan taro a sauran shiyyoyin kasar ba tare da wani takamaiman tsari ba. Babbar manufar wannan shiri ita ce tabbatar da tsaro da zaman lafiya a dukkan yankunan Nijeriya.
Wannan umarni ne kai tsaye daga Shugaban Kasa kuma Babban Kwamandan Rundunonin Sojin Tarayyar Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, kuma yana nuna irin zurfin tunaninsa da cikakken kudurinsa na magance matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta.
Ina amfani da wannan dama wajen mika godiyata ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa irin jagorancin da yake bayarwa, musamman yadda yake bai wa kare rayuka da dukiyoyin ’yan Nijeriya a fadin kasar muhimmanci.
Haka kuma, ina mika godiyata ga duk wadanda suka bayar da gudummawa wajen cimma wannan gagarumar nasara, musamman Babbar Mataimakiya ta Musamman ga Shugaban Kasa kan Hulda da Al’umma (Yankin Kudu maso Gabas), saboda jajircewarta da hadin gwiwar da ta bayar.
Kuma mafi muhimmanci, ina cewa ga al’ummar yankin Kudu maso Gabas: Na gode, Kudu maso Gabas.














