Malamin addinin Musuluncin na Jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya kare Sheikh Sani Yahaya Jingir kan kalaman da ya yi na baya-bayan nan, inda ya nuna goyon bayansa kan takarar siyasar Musulmi da Musulmi gabanin babban zaɓen 2027.
Kalaman Jingir, waɗanda ya yi a wani taron auren gata don nuna goyon baya ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, sun jawo kakkausar suka daga wasu ’yan Nijeriya.
A ranar Litinin, yayin da yake mayar da martani kan cece-kucen da kalaman suka haifar a shafinsa na Facebook, Sheikh Gumi, ya ce ya kamata a yi wa Jingir uzuri saboda tsattsauran ra’ayinsa a harkar siyasa.
Gumi ya ce Jingir yana tsananin adawa da nuna wariya ga Musulunci.
Ya kuma ce jam’iyyun adawa ba su daina amfani da addini wajen samun ƙuri’un jama’a ba.
A cewar Gumi, bai kamata a jawo addini cikin abin da ya kira “dattin siyasa” a ƙasa mai addinai daban-daban kamar Nijeriya ba.
Gumi ya ce: “Ya kamata a yi wa Jingir uzuri kan tsattsauran ra’ayinsa a siyasa. Yana cikin guguwar tsananin nuna wariya ga Musulunci.”
Ya kuma kawo cece-kucen da ya biyo bayan naɗin wani Musulmi a matsayin mataimakin shugaban jami’a a Jihar Filato a matsayin wani misali na rikicin addini a siyasa.
Gumi ya ƙara da cewa jam’iyyun siyasa daga ɓangarori daban-daban a wasu lokuta suna amfani da addini domin samun ƙuri’u.
Saboda haka, ya gargaɗi ’yan siyasa da shugabannin addini da su guji barin addini ya zama hanyar raba kan jama’a gabanin zaɓen 2027.
Nijeriya ƙasa ce mai bin addinai daban-daban, inda Musulmi da Kiristoci su ne manyan ƙungiyoyin addini.
Batun tikitin takarar Musulmi da Musulmi ko Kirista da Kirista ya kasance batu mai matuƙar muhimmanci a siyasar ƙasar














