ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shekarau, Ganduje Da Abba Kabir Sun Ci Taliyar Ƙarshe – Kwankwaso

by Abubakar Sulaiman
3 weeks ago

Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya ce tsofaffin gwamnonin Kano, Malam Ibrahim Shekarau da Abdullahi Ganduje, da kuma Gwamna Abba Yusuf, sun kai ƙarshen siyasarsu a jihar. Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa (NAN) a Abuja, inda ya yi tsokaci kan makomar wasu tsofaffin abokan siyasarsa da suka raba gari.

Kwankwaso ya ce nasarar siyasa da aka gina bisa “cin amana” ba ta dawwama, yana mai cewa gogewarsa cikin sama da shekaru 25 ta nuna masa cewa ’yan siyasar da suka ci amanar abokan hulɗarsu kan rasa tasirinsu daga baya. Ya bayar da Ganduje a matsayin misali, yana cewa tsohon gwamnan ya yi aiki tare da shi na tsawon shekaru takwas a matsayin mataimaki kafin ya zama gwamna a 2015, amma daga lokacin da suka fara samun saɓani ne, a cewarsa, matsalolin siyasarsa suka fara.

Ya ce da Ganduje ya ci gaba da kasancewa cikin tsarin siyasar da suka gina tare, da ya samu ƙarin karɓuwa a Kano da sauran sassan ƙasar. Kwankwaso ya kuma soki Gwamna Abba Yusuf, yana zarginsa da nisantar mutanen da suka yi aiki domin ganin ya zama gwamna. Ya ce tsarinsu na Kwankwasiyya ya yi aiki tuƙuru wajen tabbatar da zaɓen Gwamna Yusuf a matsayin ɗan takara domin guje wa maimaita abin da ya ce ya faru tsakaninsa da Ganduje.

ADVERTISEMENT

Kwankwaso ya ce Kwankwasiyya ta sake taimaka wa Abba Kabir wajen samun nasara a zaɓen 2023, amma daga baya gwamnan ya nisanta kansa daga ɗariƙar. Ya ce Gwamna Abba ba ya tare da Ganduje kai tsaye, amma kuma ya ƙi a kira shi da “Dan Gandujiyya”, yana mai cewa yunƙurin gwamnan na neman zama babban jigon siyasa a Kano na iya haifar masa da matsaloli. Ya kuma bayyana cewa rikicin neman gado da ikon siyasa ba sabon abu ba ne a Kano ko Nijeriya.

Da yake magana kan sauyin dangantakar ’yan siyasa, Kwankwaso ya tuna da wata tattaunawa da Shugaba Bola Tinubu, inda ya ce shugaban ya taɓa roƙonsa ya sasanta da Ganduje.

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Kwankwaso ya ce ya tunatar da Tinubu kan wasu tsofaffin abokan siyasarsa da suka taɓa kasancewa kusa da shi amma daga baya suka rasa tasirinsu, ciki har da tsohon mataimakin gwamnan Legas, Kofoworola Bucknor-Akerele, da tsohon gwamnan Legas, Akinwunmi Ambode. Sai dai ya ce har yanzu yana ɗaukar tsohon gwamnan Osun, Bisi Akande, a matsayin ɗaya daga cikin abokan siyasarsa na kusa.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Next Post
Hadin Gwiwa Tare Da Sin Na Bude Sabbin Damarmaki Ga Bunkasar Sana’ar Noma A Afirka Ta Kudu

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.