ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai Na Aikin Hajjin Bana Na Bauchi Ya Rasu A Saudiyya

by Khalid Idris Doya and Sulaiman
4 months ago
Aikin hajji

Hukumar Jin Daɗin Alhazai Musulmi ta Jihar Bauchi ta sanar da rasuwar ɗaya daga cikin jami’an kula da jin daɗin alhazan jihar, Alhaji Shehu Yahaya Jalam, a asibitin Al-Noor da ke Makkah a ƙasar Saudiyya, bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Kafin rasuwarsa, marigayin ya kasance shugaban kwamitin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na aikin Hajjin 2026, sannan kuma babban Sakatare (permanent secretary) ne a ofishin sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi (SSG).

Marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen raba masauƙin alhazan jihar Bauchi a lokacin gudanar da aikin Hajjin bana a ƙasar Saudiyya. Haka kuma marigayin Shehu ya jagoranci harkokin ciyar da alhazan jihar Bauchi, inda ya kasance sakataren kwamitin ciyarwa.

ADVERTISEMENT

Jalam ya rasu ne a daren ranar Asabar bayan gajeruwar rashin lafiya yayin da yake ci gaba da gudanar da ayyukan kula da jin daɗin alhazan jihar.

A wata hira ta wayar tarho da wakilinmu daga Saudiyya, tsohon daraktan ayyuka na hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Bauchi, kuma ɗaya daga cikin masu kula da aikin Hajjin 2026 na jihar, Alhaji Sabiu Barau Ningi, ya tabbatar da rasuwar Jalam.Ningi wanda babban sakatare (PS) ne a ofishin mataimakin gwamnan jihar Bauchi, ya ƙara da cewa, “Ya rasu ne sakamakon gajeruwar rashin lafiya. Tun bayan sauƙarsu a Madina ya ɗan koka wa abokan zama cewa baya jin dadi to kuma ya je asibiti a Madina an duba shi an ba shi magani.”

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

To sun dawo sun ci gaba da aikinsu. Ka san shi cikin tawagar farko (advance team) tun ma kafin alhazan jiha su iso Makka, su sun iso Makka kuma sun zo sun ci gaba da aiki har jirgin ƙarshe wanda ya shigo daren shekaran jiya ke nan.

Cikin hukuncin Allah sun raba wa kowa ɗakuwa cikin hukuncin Allah daman na cikin waɗanda suka shugabanci kwamitin rabon ɗakuna wa alhazai to sun raba duk ɗakuna sun bai wa kowani Alhaji har da muma officials duk shi ya raba mana ɗakuna.

Ningi ya kuma bayyana cewa daga baya rashin lafiyar marigayin ta tsananta, inda aka mayar da shi sashen kulawa ta musamman (ICU) na wani asibiti a Makkah, inda daga bisani ya rasu a daren Asabar.

“Alhaji Shehu Yahaya Jalam ya rasu jiya da misalin ƙarfe 2:00 na dare agogon Saudiyya, wanda ya yi daidai da ƙarfe 12:00 na dare agogon Nijeriya, a Asibitin Al-Noor da ke Makkah,” in ji jami’in kula da aikin Hajjin.

Ya ce Babban Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Bauchi, Imam Abdurrahman Ibrahim Idris, ya sanar da Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), kuma ana ci gaba da shirye-shiryen jana’izarsa a Masallacin Harami da ke Makkah.

Ya ce rashin lafiyar da suka fi tunanin ita ce ta yi ajalin mamacin ita ce bugun zuciya saboda daman marigayin na kan shan maganin hawan jini. Ya bayyana marigayin Shehu Jalam a matsayin ɗaya daga cikin jami’an da suka fi sadaukar da kai wajen hidimtawa alhazan jihar Bauchi, tare da yabawa jajircewarsa, ƙarfin hali da rashin son kai.

“Mun yi rashin mutum mai ƙwazo da sadaukarwa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da jin daɗi da walwalar alhazan Bauchi,” in ji Ningi.

Ya miƙa ta’aziyyarsa ga Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, iyalan mamacin, al’ummar masarautar Jalam da ƙaramar hukumar Dambam, al’ummar jihar Bauchi, Amirul Hajjin Bauchi na 2026 da Sarkin Misau, Alhaji Ahmad Sulaiman, bisa wannan babban rashi.

Ya kara da cewa a da shekarun baya marigayi Shehu Jalam ya kasance mai zuwa aikin hajji domin hidimta wa alhazzai a matsayin ɗan sa-kai inda hakan ya sa gwamnan jihar Bala Muhammad ya lura da ƙoƙarinsa tare da jawo shi cikin kwamiti kula da jin dadin alhazzai na jihar.

Ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya karɓi ayyukansa na alheri, Ya ba shi Aljannatul Firdausi, sannan Ya bai wa iyalansa, abokan aikinsa da daukacin tawagar aikin Hajjin 2026 juriyar wannan babban rashi.

“Allah Ya sanya kabarinsa ya zama ɗaya daga cikin lambunan Aljanna.”

Aikin hajji
Khalid Idris Doya
+ posts Bio
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Yaro Ya Harbe Kansa Har Lahira Bayan Mafarauci Ya Yi Sakaci Da Bindigarsa A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    An Kama Mutane 5 Da Sassan Jikin Ɗan’Adam Za Su Yi Tsafi A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Tsohon Mai Neman Takarar Gwamnan Bauchi, Bala Jibrin, Ya Fice Daga APC Kan Zargin Ɗoki-ɗora
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    ‘Yansanda Sun Cafke Tsoho Mai Shekara 70 Kan Zargin Yi Wa ‘Yar Shekara 8 Fyaɗe A Bauchi
Aikin hajji
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

Zaɓen Fidda Gwani na APC: ‘Yan Majalisar Wakilai 12 da Suka Rasa Tikitin Komawa Takara

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.