ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zaɓen Fidda Gwani na APC: ‘Yan Majalisar Wakilai 12 da Suka Rasa Tikitin Komawa Takara

by Sulaiman
4 months ago
Majalisa

Wasu daga cikin mambobin Majalisar Wakilai masu ci a yanzu sun gaza samun tikitin komawa takara a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC da aka gudanar a faɗin ƙasar nan gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Daga cikin fitattun ‘yan majalisar da suka rasa tikitin akwai Jagoran Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Julius Ihonvbere, wanda ƙoƙarinsa na neman wa’adi na uku a mazaɓar Owan ta Tarayya a Jihar Edo ya ci tura. Ya sha kaye ne a hannun tsohon Kwamishinan Ma’adinai, Andrew Ijegbai.

A Jihar Edo kuma, wani ɗan majalisa mai ci, Eseosa Iyawe, ya rasa tikitin APC na mazaɓar Oredo ta Tarayya ga tsohon Kwamishinan Ilimi, Dakta Paddy Iyamu.

ADVERTISEMENT

Iyawe na daga cikin ‘yan majalisar da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar Labour Party amma daga baya suka koma APC.

A Jihar Imo, mambobin majalisar wakilai guda huɗu masu ci sun rasa tikitin komawa takara.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Sun haɗa da Matthew Nwogu mai wakiltar Aboh Mbaise/Ngor Okpala, Miriam Onuoha ta Okigwe South, Harrison Nwadike mai wakiltar Isu/Njaba/Nkwerre/Nwangele, da Emeka Martins Chinedu na mazaɓar Ahiazu/Ezinihitte.Haka kuma, Ismail Kayode, mai wakiltar mazaɓar Ifelodun/Oyun/Offa ta Tarayya a Jihar Kwara, ya rasa tikitin APC ga tsohon Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, Rafiu Ajakaye.

A Jihar Kebbi, ɗan majalisa mai ci Mansur Musa Jega ya rasa tikitin APC na mazaɓar Jega/Gwandu/Aleiro bayan wata yarjejeniyar maslaha da ta bai wa tsohon Kwanturola Janar na Hukumar Gyaran Hali ta Nijeriya, Jafar Ahmed Jega, tikitin.

Haka zalika, ‘yan majalisar wakilai guda huɗu masu ci a Jihar Jigawa sun rasa tikitin komawa takara yayin zaɓen fidda gwani.

Sun haɗa da Muktar Muhammad mai wakiltar Kazaure/Roni/Gwiwa/Yankwashi; Ibrahim Usman Auyo na Hadejia/Auyo/Kafin Hausa; Sa’adu Wada Taura mai wakiltar Ringim/Taura, da Yusif Sa’idu Miga na Jahun/Miga.

Majalisa
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Next Post
Za A Gudanar Da Jadawalin Cancantar Shiga AFCON 2027 A Alkahira Ranar Talata

Za A Gudanar Da Jadawalin Cancantar Shiga AFCON 2027 A Alkahira Ranar Talata

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.