ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojoji Sun Hallaka Babban Kwamandan ISWAP, Sun Cafke Ƴan Fashi A Borno Da Adamawa

by Abubakar Sulaiman
7 months ago
Sojoji

Sojojin rundunar Operation HAƊIN KAI (OPHK) sun samu gagarumar nasara a yankin Arewa maso Gabas, inda suka hallaka manyan jagororin ’yan ta’adda, suka kuma tarwatsa ayyukan ISWAP da Boko Haram, tare da daƙile wasu laifuka ta hanyar samun bayanan leƙen asiri da kai farmaki cikin tsari.

A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na OPHK, Laftanar Kanar Sani Uba, ya fitar a Maiduguri, an tabbatar da hallaka Julaibib, wani babban kwamandan ISWAP da ke aiki a yankin Gujba na Timbuktu Triangle, a wata arangama da ta faru a kusa da Kimba, ƙaramar hukumar Damboa, a ranar Juma’a, 30 ga Janairu, 2026. Ya ce kisan jagoran ya jefa ’yan ISWAP cikin ruɗani, inda aka ce an kuma hallaka wasu daga cikinsu yayin farmakin.

  • Gwamnatin Jihar Borno Za Ta Dawo Da ‘Yan Gudun Hijira 3,000 Daga Kamaru
  • ’Yan Ta’adda Sun Kai Wa Ƙauyuka 2 Hari A Adamawa

Uba ya ƙara da cewa, a wani artabun na daban, sojoji tare da haɗin gwuiwar Civilian Joint Task Force (CJTF) sun yi kwanton ɓauna tsakanin Ngazalgana da Lamusheri a Jihar Borno, inda suka hallaka ’yan ta’adda uku. An ce sojojin sun yi amfani da bayanan sirri wajen kafa tarko a wata hanya, lamarin da ya sa suka yi nasara, tare da kwato bindigogi AK-47 guda biyu daga wajensu.

ADVERTISEMENT

A ranar 29 ga Janairu, 2026, sojoji sun kuma yi arangama da ’yan Boko Haram/ISWAP a Tsokorok, ƙaramar hukumar Gwoza, inda suka tilasta musu ja da baya bayan sun hallaka guda ɗaya daga cikinsu, tare da kwato babura guda biyu. A Adamawa kuma, sojoji sun amsa kiran gaggawa daga al’ummar Barama a Mubi North, inda suka dakile yunƙurin fashi, suka cafke mutane biyu da ke ƙoƙarin kai hari ga wani ɗalibi na Federal Polytechnic, Mubi, tare da ƙwato adda, da kwamfutoci tafi-da-gidanka, wayoyi da na’urar caji.

Hakazalika, a wani sintiri da aka yi tare da ’yan sa kai a hanyar Amtasa–Washim a ƙaramar hukumar Hong, sojoji sun fafata da ’yan ta’adda, suka tilasta musu guduwa, tare da ceto wata mata da aka sace. An kuma ƙwato bindigar AK-47 da harsasai da sauran makamai.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Sojoji
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Wannan Wasika Ta Bayyana Kaunar Dake Tsakanin Sin Da Afirka

Wannan Wasika Ta Bayyana Kaunar Dake Tsakanin Sin Da Afirka

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.