ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 18, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tabbas Za A Kai Ga Mayar Da Tsibiran Chagos Kasar Asalinsu

by CGTN Hausa
3 months ago

Fadar firaministan kasar Birtaniya ta sanar a ranar 11 ga wata cewa, kasar
za ta dakatar da shirin mika tsibiran Chagos ga Mauritius, sakamakon
rashin samun goyon baya daga shugaban kasar Amurka Donald Trump.
“Mun sha bayyana cewa, ba za mu aiwatar da shirin ba sai da goyon
bayan Amurka”, in ji gwamnatin Birtaniya. Lallai abun ban mamaki ne
cewa maido da yankin wata kasa mai mulkin kanta hannunta, sai da
amincewar wata kasa ta daban.

Tsibiran Chagos suna tekun Indiya da ke da nisan kilomita 750 daga
arewa maso gabashin kasar Mauritius. Bisa yarjejeniyar Paris, Birtaniya
ta kwace Mauritius da ma tsibiranta daga hannun Faransa a shekarar
1814, kuma daga nan ta fara mulkin mallaka na sama da shekaru 150 a
kasar. Ya zuwa shekarar 1965, Birtaniya ta tilasta wa Mauritius bayar da
tsibiran Chagos bisa sharadi na “ba ta ’yancin kai”. A shekarar 1966
kuma, Birtaniya ta daddale yarjejeniya tare da Amurka, inda ta ba da
hayar tsibirin Diego Garcia ga Amurka don ta gina sansanin sojojinta a
wurin, tsibirin da ya kasance mafi girma daga cikin tsibiran Chagos,
kuma domin gina sansanin, har an tilastawa mutane kimanin 2000 ’yan
asalin tsibirin barin muhallansu. Ma iya cewa tsibiran Chagos sun shaida
tarihin mulkin mallaka na yadda kasashen yamma suka yi abin da suka ga
dama ga wata kasar Afrika mai mulkin kai.

Mauritius ta dade tana ja-in-ja da Birtaniya game da batun ikon tsibiran
Chagos. A shekarar 2019, kotun kasa da kasa karkashin MDD ta yanke
hukuncin cewa, ya kamata Birtaniya ta maido da tsibiran Chagos ga
Mauritius. Daga nan kuma har zuwa watan Mayun shekarar 2025, aka kai
ga cimma yarjejeniyar maido da tsibiran a tsakanin kasashen biyu. Sai dai
bisa yarjejeniyar, dole ne Mauritius ta ci gaba da ba da hayar tsibirin
Diego Garcia ga Birtaniya da kuma Amurka.

ADVERTISEMENT

To, amma me ya sa Amurka ta ki yarda Birtaniyata ta mayar da tsibiran
Chagos hannun Mauritius? Dalilin shi ne sansanin soja da Amurka din ta
kafa a tsibirin Diego Garcia, wanda ke da matukar muhimmanci ga
Amurka. Tun bayan da aka fara aiki da sansanin, Amurka ta girke
nau’o’in jiragen saman kai hari a sansanin, don yin amfani da shi wajen
shawo kan mashigar tekun Hormuz da ta Bab El-Mandeb, har ma da
gabar tekun Aden da ke kusa da tsibirin. Musamman ta yin la’akari da
yanayin rikicin da ka iya kara tabarbarewa a tsakanin Amurka da Iran,
Amurka na bukatar tsibirin wajen shawo kan Iran da yankin gabas ta
tsakiya.

A hakika, abin da ya faru ga tsibiran Chagos ya tono mana ainihin
yanayin kasashen yamma na nuna fin karfi, baya ga nuna wahalhalun da
ake fuskanta wajen kawar da mulkin mallaka daga fadin duniya. Duk da
haka, hannun agogon tarihi ba zai koma baya ba, saboda wani shingen danniya na dan lokaci.

LABARAI MASU NASABA

Majalisa Ta Yi Watsi Da Bukatar MDD Ta Bincikar Badakalar Satar Daliban Oyo

Yadda Gano Ma’adanin ‘Lithium’ Zai Sauya Rayuwar Al’ummar Kudancin Kaduna

A cikin ’yan shekarun baya, har kullum kungiyar tarayyar Afirka na mai
da hankalinta a kan batun tsibiran Chagos, kuma a ganinta, yadda
Birtaniya ta balle tsibiran daga yankin Mauritius ya saba wa kudurori da
dama na MDD, kuma batun a maimakon a ce takaddama ce tsakanin
Birtaniya da Mauritius, batu ne mai muhimmanci kan ko za a kai ga
kawar da mulkin mallaka kwata-kwata daga nahiyar Afirka ko a’a. Sai
kuma a game da matakan da Birtaniya da Amurka suka dauka, Dhananjay
Ramful, ministan kula da harkokin waje, da dunkulewar shiyya, da
cinikayyar kasa da kasa na Mauritius, ya ce kasarsa za ta yi iyakacin
kokarin kawar da mulkin mallaka daga shiyyar ta hanyoyin diplomasiyya
da kuma na shari’a.

Kawar da mulkin mallaka daga fadin duniya abu ne da ba za a iya hana
shi ba, duk da matsalolin da ake iya fuskanta, amma tabbas za a ga
bayansa. Kamar dai yadda masani kan ilimin tsarin mulkin duniya na
Nijeriya Livingstone Wechie ya ce, lokaci ya wuce da za a bari kasashen
yamma, ta fakewa da duk wani dalili su rika cin zalin wani bangare na
kasashe masu tasowa.

CGTN Hausa
+ postsBio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ta Nuna Matukar Adawa Da Matakin Burtaniya Na Mallake Kamfanin Karafa Na British Steel
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Masanin Kimiyya Na Sin Ya Lashe Kyautar UNESCO-Russia Mendeleev A Fannin Tushen Kimiyya
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Omar M. Yaghi: Kalaman Xi Sun Kara Mana Kwarin Gwiwa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Manufar Sin Ta Ba Da Jagoranci Ga Tafiyar Da Fasahar AI A Duniya

MASU ALAKA

Majalisa Ta Goyi Bayan CBN Kan Sauya Fasalin Naira Bayan Tafka Muhawara 
Labarai

Majalisa Ta Yi Watsi Da Bukatar MDD Ta Bincikar Badakalar Satar Daliban Oyo

July 18, 2026
Yadda Gano Ma’adanin ‘Lithium’ Zai Sauya Rayuwar Al’ummar Kudancin Kaduna
Rahotonni

Yadda Gano Ma’adanin ‘Lithium’ Zai Sauya Rayuwar Al’ummar Kudancin Kaduna

July 18, 2026
Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota
Kotu Da Ɗansanda

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

July 18, 2026
Next Post
Wakilin Musamman Na Shugaban Sin Zai Halarci Bikin Rantsuwar Kama Aiki Ta Shugaban Congo (Brazzaville)

Wakilin Musamman Na Shugaban Sin Zai Halarci Bikin Rantsuwar Kama Aiki Ta Shugaban Congo (Brazzaville)

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Nuna Matukar Adawa Da Matakin Burtaniya Na Mallake Kamfanin Karafa Na British Steel

Sin Ta Nuna Matukar Adawa Da Matakin Burtaniya Na Mallake Kamfanin Karafa Na British Steel

July 18, 2026
Tasirin AI (Artificial Intelligence) A Harkokin Al’umma Na Yau Da Kullum

Tasirin AI (Artificial Intelligence) A Harkokin Al’umma Na Yau Da Kullum

July 18, 2026
Xavi Ya Ce A Shirye Yake Ya Karɓi Ragamar Horar Da Tawagar Ƙasa

Xavi Ya Ce A Shirye Yake Ya Karɓi Ragamar Horar Da Tawagar Ƙasa

July 18, 2026
Masanin Kimiyya Na Sin Ya Lashe Kyautar UNESCO-Russia Mendeleev A Fannin Tushen Kimiyya

Masanin Kimiyya Na Sin Ya Lashe Kyautar UNESCO-Russia Mendeleev A Fannin Tushen Kimiyya

July 18, 2026
Burina Zama Daya Daga Cikin Fitattun Masu Daukar Hoto A Nijeriya –Ibrahim Aminu

Burina Zama Daya Daga Cikin Fitattun Masu Daukar Hoto A Nijeriya –Ibrahim Aminu

July 18, 2026
Omar M. Yaghi: Kalaman Xi Sun Kara Mana Kwarin Gwiwa

Omar M. Yaghi: Kalaman Xi Sun Kara Mana Kwarin Gwiwa

July 18, 2026
Manufar Sin Ta Ba Da Jagoranci Ga Tafiyar Da Fasahar AI A Duniya

Manufar Sin Ta Ba Da Jagoranci Ga Tafiyar Da Fasahar AI A Duniya

July 18, 2026
CDC Ta Afirka Ta Yaba Wa Sin Bisa Goyon Bayanta Ga Dakile Cutar Ebola

CDC Ta Afirka Ta Yaba Wa Sin Bisa Goyon Bayanta Ga Dakile Cutar Ebola

July 18, 2026
Yadda Ciwon Hanta Ke Yaduwa Tsakanin Ma’aurauta

Yadda Ciwon Hanta Ke Yaduwa Tsakanin Ma’aurauta

July 18, 2026
Xi Jinping Ya Bukaci A Gudanar Da Aikin Ceto A Tsanake Bayan Rugujewar Bangaren Wani Tsauni A Chongqing

Xi Jinping Ya Bukaci A Gudanar Da Aikin Ceto A Tsanake Bayan Rugujewar Bangaren Wani Tsauni A Chongqing

July 18, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.