ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tarihin Shugaban Makaranta Na Farko A Arewa (Hedimasta) (1)

by Idris Aliyu Daudawa
4 months ago

An haifi Magajin Gari Muhammadu Sambo a Zariya a shekara ta 1888  marigayi Magajin Gari Sambo shi ne wanda ya ƙirƙiri Kaduna ta zamani, bugu da ƙari kuma shi ne Malamin makarantar Boko na farko ɗan asalin Arewa,

Alaƙarsa da ilimi ta fara ne daga shekara ta 1903 a Makarantar Lardi ta Kano, inda ya ke shi ne ɗalibi na takwas da aka rubuta sunansa a rajista. Daga 1903 zuwa shekarar 1908, ya shimfiɗa tubalin sadaukar da rayuwarsa ga neman ilimi, wayewa, da kuma koyar da shi.

A shekarar 1910,ya zama Malami mai kulawa da sauran Malaman makaranta da yadda ake tafiyar da ita (Hedimasta) ɗan asalin ƙasa ɗan Arewa na farko a Makarantar  Lardi ta Zariya (wadda a yanzu ake kira da suna Alhuddahudda College ko kuma Kwalejin Alhuddahudda). Nasarar da ya yi ta nuna irin jajircewar da yake da ita wajen ci gaban ilimi. A 1912, aka naɗa shi Hedimasta na farko a Makarantar midil ta Bauchi (wacce daga baya aka sani da sunan Kwalejin ilimi ta Sambo ).A can ne ya koyar da ilimi tare da ƙarfafa tunani mai zurfi da neman ilimi.

ADVERTISEMENT

A shekarar 1916, sai aikinsa ya ɗauki sabon salo a lokacin da Sarkin Zazzau Aliyu Ɗan Sidi ya naɗa shi Wamban Zazzau kuma Hakimin Jaji. A wancan lokacin ya fara gina wani gidan baƙi (guest house) wanda daga baya ne ya zama Command and Staff College Jaji, wato babbar cibiyar  horar da manyan  Sojoji ta Nijeriya.

Sai dai a 1920, Sarkin Zazzau Dalhatu ya ƙwace masa Sarauta, amma hakan bai sa ya fid da rai ba.

LABARAI MASU NASABA

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

A shekarar 1923, aka sake karrama shi a lokacin da aka zaɓe shi ya jagoranci ƙungiyar Turawan Birtaniya da suka gudanar da ƙirga mutane ta farko (ƙidaya) a Arewacin Nijeriya. Sakamakon haka ne, sai Sarkin Ingila, Sarki George, ya ba shi takardar nambar yabo (Certificate of Honor) a 1924.

A 1925, aka dawo da shi Sarautar Hakimci tare da ba shi  muƙamin Sarautar Hakimi mai kula da Sabon Gari Zariya. Ya taka muhimmiyar rawa wajen gina Sabon Garin, na Zariya, inda ya kafa makarantar firamare, da kuma haifar da sabbin unguwanni irin su Muchia da Dogon Bauchi daga 1927 zuwa 1930.

An samu maku wannan ne daga Dandalin Tarihin Magabata za mu ci gaba a mako mai zuwa,

Idris Aliyu Daudawa
+ postsBio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tarihin Rayuwar Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim (2)
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kyamar Baƙi: An Sake Kwaso Ƴan Nijeriya 83 Daga Afirka Ta Kudu
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Manoma 60 Da Kayan Aiki A Edo
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tsohon Shugaban Ƙasa Jonathan Ya Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Ƙasa 18 A Jihar Bauchi

MASU ALAKA

Ilimi

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

August 31, 2026
Ilimi

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

August 29, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Ilimi

Kano Ta Yi Zarra Wajen Kashe Kuɗi Don Raya Ilimi A Yammacin Afirka

July 11, 2026
Next Post
Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda, Sun Ƙwato Makamai Da Abubuwan Fashewa

Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta'adda, Sun Ƙwato Makamai Da Abubuwan Fashewa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.