Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarin albashi tsakanin kashi 30 zuwa 80 cikin 100 ga jami’an rundunar sojojin Nijeriya, inda kusan sojoji 250,000 za su amfana da sabon tsarin.
A cewar wata sanarwa da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, sabon tsarin albashin zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Satumba, 2026.
A sabon tsarin, jami’an da ke sama da muƙamin Kanal, ciki har da Birgediya Janar, Manjo Janar, Laftanar Janar da Janar, za su samu ƙarin albashi na kashi 30 cikin 100.
Jami’ai daga muƙamin Kanal zuwa Warrant Officer za su samu ƙarin kashi 50 cikin 100, yayin da sojoji daga muƙamin Private zuwa Sajan za su samu ƙarin kashi 80 cikin 100.
Sabon tsarin zai sa albashin rundunar sojojin Nijeriya a shekara guda ya ƙaru daga naira biliyan 660 zuwa naira biliyan 924.
Shugaba Tinubu ya ce ƙarin albashin na nuna ƙudirin gwamnatinsa na inganta walwalar jami’an sojoji domin girmama sadaukarwar da suke yi wajen yaƙi da ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da kuma ta’addanci.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bunƙasa rundunar sojin ta hanyar samar da makamai da fasahohin zamani, yana mai cewa tsaro shi ne ginshiƙin ci gaban ƙasa.
Shugaban ya kuma buƙaci jami’an sojojin da su ɗauki wannan ƙarin albashi a matsayin godiyar da ƙasa ke yi musu bisa hidimar da suke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.














