ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Ya Yaba Wa Jami’an Tsaro Kan Ceto Dalibai 100 Da Aka Sace A Neja

by Rabi'u Ali Indabawa
9 months ago
Neja

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa jami’an tsaro saboda kokarinsu na ceto dalibai 100 na wata makarantar Katolika da aka kai wa hari a Jihar Neja.

Yayin da yake bayyana farin cikinsa kan dawowar daliban, Shugaba Tinubu ya umarci jami’an tsaro da su tabbatar da gaggauta kuButar da sauran dalibai 115 da malamansu da har yanzu suke tsare a hannun masu garkuwa da su.

Wannan bayani ya fito ne daga Bayo Onanuga, Mashawarci na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai da Tsare-tsare, a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, ranar Litinin.

ADVERTISEMENT
  • Ƙirƙirar Hisbah Mai Zaman Kanta: Kungiyar Lauyoyi ‘Yan Kano Ta Shigar Da Tinubu Ƙara
  • Tinubu Na Ɗaukar Ƙwararan Matakai Don Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya – Shettima

Onanuga ya ce Shugaba Tinubu ya tabbatar wa iyayen daliban cewa gwamnatin tarayya da ta Jihar Neja suna aiki tare don ganin an hada dukkan daliban da aka sace da iyalansu cikin koshin lafiya.

A wani bangare na sanarwar an ce, “An sanar da ni game da dawowar dalibai 100 na makarantar Katolika da ke Jihar Neja cikin koshin lafiya. Ina murna tare da Gwamna Umar Bago kuma ina yaba wa jami’an tsaro bisa jajircewarsu wajen tabbatar da komawar daliban wurin iyalansu tun bayan mummunan lamarin da ya faru a ranar 21 ga Nuwamba.

LABARAI MASU NASABA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

“Umarna ga jami’an tsaro har yanzu ita ce cewa dole ne a ceto dukkan daliban da sauran ‘yan Nijeriya da aka yi garkuwa da su a fadin kasar nan, a dawo da su gida cikin aminci. Dole ne mu tabbatar da an kirga duk wanda lamarin ya rutsa da shi.

“Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da aiki tare da Jihar Neja da sauran jihohi don tsare makarantu da kuma samar da ingantacciyar muhalli mai aminci da dacewa domin karatun ‘ya’yanmu.

“Daga yanzu, jami’an tsaro tare da gwamnonin jihohi dole su hana afkuwar garkuwa da mutane a nan gaba. Ya kamata yaranmu su daina zama abin hari ga mugayen ‘yan ta’adda da ke kokarin dakile iliminsu tare da jefa su da iyayensu cikin azaba marar misaltuwa.”

Neja
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro
Manyan Labarai

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 11, 2026
Neja
Manyan Labarai

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026
Neja
Manyan Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Next Post
Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Hukuncin Kisa Kan Maryam Sanda

Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Hukuncin Kisa Kan Maryam Sanda

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

September 11, 2026
Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 11, 2026
Sanata yari

Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari

September 11, 2026
Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

September 11, 2026
SAW

Ɗabi’un Annabi (SAW) Kan Abubuwa Na Al’adar Rayuwa

September 11, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Horar Da Malamai 250,000

Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Horar Da Malamai 250,000

September 11, 2026
Neja

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

September 11, 2026
Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

September 11, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang

September 11, 2026
Neja

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.