ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Trump Ya Ce Har Yanzu Bai Gamsu Da Tattaunawar Yarjejeniyar Da Ake Yi Da Iran Ba

by Sadiq
4 months ago

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce har yanzu bai gamsu da shawarwarin Iran ba a tattaunawar da ake yi kan yarjejeniyar zaman lafiya, duk da rahotannin da ke cewa an riga da cimma matsaya.

A wani taron majalisar ministoci a Fadar White House, Trump ya ce Iran na son yarjejeniyar amma har yanzu ba ta cika sharuɗan Amurka ba.

Ya kuma ce ba zai yi gaggawa wajen kammala tattaunawar ba.

ADVERTISEMENT

“Iran na matuƙar son yin yarjejeniyar, amma har yanzu ba su kai ga inda ake so ba. Ba mu gamsu ba,” in ji Trump, yana mai gargaɗin cewa Amurka na iya “kammala aiki” idan tattaunawar ta faskara.

Kafofin yaɗa labarai na Iran sun ruwaito cewa akwai daftarin yarjejeniyar da zai sassauta takunkumi da kuma buɗe muhimman hanyoyin jiragen ruwa kamar mashigar Hormuz.

LABARAI MASU NASABA

Nijar Da Canada Sun Ƙulla Yarjejeniyar Gina Sabuwar Matatar Mai A Jihar Dosso

Kotun ICC Ta Yi Watsi Da Sabbin Takunkuman Amurka Kan Jami’anta

Sai dai Fadar White House ta ƙaryata rahoton, tana mai cewa ƙarya ne.

Trump ya ce Amurka ba za ta amince Iran ko wata ƙasa ta mallaki ko sarrafa wannan muhimmin mashigar ruwa ba.

Ya kuma yi barazanar ɗaukar matakin soja idan ya zama dole.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio ya ce an samu ɗan ci gaba a tattaunawar, amma ba a kai ga cimma matsaya ba.

Trump ya kuma danganta yarjejeniyar da sauran batutuwan diflomasiyya a Gabas ta Tsakiya, yana mai cewa yarjejeniyar na iya danganta da ƙarin ƙasashen da suka ƙulla dangantaka da Isra’ila.

Ya ce ko da yake zai iya amincewa da yarjejeniyar na wucin gadi kan batun nukiliyar Iran, ba zai yadda Rasha ko China su riƙa ajiyar uranium na Iran ba.

Tattaunawar na ci gaba a daidai lokacin da ake fuskantar tashin hankali a duniya da kuma matsin tattalin arziƙi gabanin zaɓukan Amurka masu zuwa.

MASU ALAKA

Kasashen Ketare

Nijar Da Canada Sun Ƙulla Yarjejeniyar Gina Sabuwar Matatar Mai A Jihar Dosso

August 23, 2026
Kasashen Ketare

Kotun ICC Ta Yi Watsi Da Sabbin Takunkuman Amurka Kan Jami’anta

August 23, 2026
Kasashen Ketare

Rasha Da Ukraine Sun Zafafa Hare-hare Kan Juna Bayan Yaƙinsu Ya Ɗauki Sabon Salo

August 22, 2026
Next Post
Ramadan: ‘Yansanda Sun Buƙaci A Sanya Ido A Kano A Goman Ƙarshe

'Yansanda Sun Kama Wasu Kan Zargin Ɓarnata Kayan Gwamnati Da Fashi A Kwara

LABARAI MASU NASABA

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

September 11, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang

September 11, 2026

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris

September 11, 2026

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.