Shugaban Amurka, Donald Trump, ya buƙaci Iran ta biya diyyar sojojin Amurka da fararen hular da ya ce an kashe ko raunata a hare-haren da Iran ta kai.
Trump ya bayyana hakan ne bayan wasu jami’an Iran sun buƙaci Amurka ta biya diyya kan ɓarnar da suka ce ta yi wa Iran a lokacin rikicin da ya faru tsakanin ƙasashen biyu.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce batun biyan diyya bai taɓa fitowa a tattaunawar da jami’an Amurka da Iran suka yi ba.
Sai dai ya ce yanzu shi ma yana son Iran ta biya diyyar mutanen da hare-haren Iran suka kashe ko suka raunata.
Trump ya kuma zargi Iran da hannu wajen mutuwar ko raunata sojojin Amurka ta hanyar bama-bamai da aka dasa a gefen tituna da kuma wasu hare-hare da ya ce an kai su ƙarƙashin jagorancin Janar Qassem Soleimani.
Ya ce ya umarci wakilan Amurka da su gabatar da buƙatar biyan diyya a duk wata tattaunawa da za a yi da Iran nan gaba.
Trump ya kuma buƙaci Iran ta biya diyya ga iyalan dubban masu zanga-zangar da ya zargi gwamnatin Iran da kashewa cikin shekaru 50 da suka gabata.
Ya ƙara da cewa ya kamata a biya diyyar mutanen da aka kashe cikin watanni biyar da suka gabata.














