ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsadar Kuɗin Ganin Likita Da Gwaje-gwaje Sun Sa Mutane Ƙaurace Wa Asibitocin Gwamnati

by Sani Anwar
2 weeks ago

Tsadar gwaje-gwaje da kuɗaɗen ganin likita a asibitocin wannan ƙasa daban-daban, na korar marasa lafiya da dama daga asibitocin gwamnati a Arewa- maso-gabas, sakamakon taɓarɓarewar tattalin arziƙin wannan ƙasa.

Lamarin ya tilasta wa wasu adadi mai yawa na marasa lafiya yin watsi da asibitoci tare da dogaro da magungunan gargajiya.

Ƙwararru a fannin kiwon lafiya, sun bayyana lamarin a matsayin mai matuƙar haɗari, inda suka yi gargaɗin cewa; hakan na iya haifar da munanan matsaloli dangane da lafiya da kuma haɗari ga lafiyar al’umma.

ADVERTISEMENT

Hari la yau, tsadar magunguna na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke tilasta wa marasa lafiya yin amfani da magungunan gargajiya, domin guje wa zuwa asibiti, don yin gwaje-gwaje da kuma biyan kuɗin ganin likita. Wannan dalili ne ya sa yanzu, marasa lafiya da dama suke ƙaurace wa ayyukan kiwon lafiya daga ƙwararru.

Masu aiko da rahotanni na na jaridar Daily trust, waɗanda suka ziyarci asibitoci a Jihohin Borno, Taraba, Adamawa da Yobe, sun tattaro cewa; majinyata da dama na kokawa wajen biyan maƙudan kuɗaɗe a duk lokacin da suka nemi ganin likita ko yin gwaje-gwaje ko kuma sayen magani.

LABARAI MASU NASABA

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Marasa Lafiya Sun Koka Kan Tsadar Ayyukan Lafiya A Yobe

A Jihar Yobe, majinyata dama sun koka kan yadda tsadar gwaje-gwaje da kuɗaɗen ganin likita da sauran makamantansu, suka ta’azzara a asibitocin gwamnatin jihar.

Haka zalika, a asibitin ƴansanda na Ultra-Modern da ke Damaturu, wakilin namu ya bayyana mana yadda ya ga cincirindon marasa lafiya da ke jiran ganin likita, domin duba lafiyarsu.

Kusan dukkan majinyatan da aka zanta da su a asibitin, sun koka da hauhawar farashin da aka samu na gwaje-gwaje da magunguna, sakamakon mawuyacin halin da aka samu kai na tattalin arziƙi.

Kazalika, sun kuma yi tir da hauhawar farashin na gwaje-gwajen da kuma magunguna, musamman idan aka yi la’akari da bara, duk da cewa; ba a samu wani ƙar ta fuskar hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ba.

Hafsat Makama, wata majinyiya ce da ke zaune a kan keken guragu, yayin da take jiran ganin likita, ta ce; ayyukan kiwon lafiya, sun yi matuƙar ta’azzara a wannan lokaci, domin kuwa babu wani sauƙi ko kaɗan.

“Lokacin da na yi rashin lafiya a shekarar da ta gabata, bayan na zo nan, sai likita ya buƙaci a yi min gwaje-gwaje na ciwon sukari da na ƙoda, akwai kuma wasu gwaje-gwajen, amma ba zan iya tunawa da su duka ba, har da magunguna, abin da na kashe ya kai kimanin naira 15,000,” in ji ta.

Ta bayyana cewa, a lokacin da ta ziyarci asibitin a bana, domin yin irin wancan gwaje-gwaje, an sanar da ita cewa; ɗakin gwaje-gwajen, ba su da kayan aikin da ake buƙata, inda aka tura ta zuwa asibitin ƙwararru na Jihar Yobe da kuma asibitin koyarwa da ke Damaturu.

“Na san ayyuka a asibitin koyarwa sun fi tsada, don haka na yanke shawarar zuwa asibitin ƙwararru, irin gwaje-gwajen da aka yi min na kusan naira 10,000 a shekarar da ta gabata, yanzu ya kai kusan naira 20,000.

“Naira 10,000 kawai nake da shi, yayin da gwaje-gwajen da magunguna suka doshi kusan naira 30,000.

Sai da na kira yayana ya aiko min da kuɗi kafin na iya cikawa na biya kuɗin,” in ji ta.

Wani majinyaci mai suna Bukar Modu, mazaunin Nayi-Nawa a Damaturu, ya ce; sai da ya nemi tallafin kuɗi daga ƴan’uwansa, bayan ya kashe maƙudan kuɗaɗe wajen kula da matarsa.

“Ranar Juma’ar da ta gabata, na kawo matata wannan asibiti, inda aka kwantar da ita don jinya,” in ji shi.

“Bayan na kawo ta, na biya kuɗin ganin likita naira 500. Bayan haka, likitan ya tura mu sashen ɗakunan gwaje-gwaje.

“A ɗakin gwaje-gwajen, mun biya naira 7,000, yayin da kuma biya naira 2,000 na hoto da aka yi mata. Bayan duk waɗannan abubuwa da muka yi, sai likitocin suka ce akwai buƙatar a kwantar da ita.

“Duk da cewa, wannan asibitin na gwamnati ne, amma har yanzu ina biyan naira 1,500 a matsayin kuɗin gado a kowace rana, daga ranar Juma’a zuwa Talata, mun kashe kusan dukkanin kuɗaɗen da muke da su, shi ya sa na kira ƴan’uwanta su taimaka mana da kuɗi,” in ji shi.

Marasa Lafiyar A Adamawa Sun Bayyana Takaicinsu

A Jihar Adamawa, wasu majinyata da aka zanta da su a asibitin koyarwa na jami’ar Modibbo Adama (MAUTH) Yola, sun bayyana damuwarsu kan tsadar aikin jinya duk da cewa, asibitin mallakar gwamnati ne, wanda ake sa ran zai bayar da tallafin ayyukan kiwon lafiya.

Wata majinyaciya mai suna Maryam Mahmud, ta koka kan yadda aikin jinya ya yi tsada a asibitocin MAUTH Yola da kuma asibitin ƙwararru na Yola.

Maryam ta ce, gwaje-gwajen da aka yi mata a kan kuɗi naira 5,000 zuwa 6,000 a asibitin MAUTH, irinsa ake yi a kan naira 3,000 zuwa 4,000 a ɗakunan gwaje-gwaje na masu zaman kansu.

“Hari la yau, gwajin da ake yi wa masu juna biyu a kan naira 2,000 a dakunan gwaje-gwaje na masu zaman kansu, a kan naira 10,000 ake yi a asibitocin gwamnati,” in ji ta.

Mahmud ta kuma yi zargin nuna son kai, wajen kula da marasa lafiya, tana mai cewa; hakan na kawo cikas ga daidaito a fannin kiwon lafiya.

Wata mai suna Jamila Tanko, ita ta bayyana ce; a baya-bayan nan, farashin aikin jinya ya yi tsada matuka ga marasa galihu, waɗanda su ne suka fi yawa a tsakanin marasa lafiya.

Jamila ta ce, halin da ake ciki yanzu na taɓarɓarewar tattalin arziƙi da tsadar magunguna, ya sa majinyata da dama barin asibitoci.

Ita ma wata mai suna Amina Usman, ta ce; ƙawayenta da sauran ƴan’uwanta a halin yanzu, ba sa iya zuwa asibiti, don duba lafiyarsu. Ta ce, sun gwammace su sha magungunan gargajiya kyamis-kyamis, don neman magani.

Har ila yau, ta koka da cewa; babu yadda za a yi su samu cikakkiyar lafiya, saboda wannan yanayi da suka tsinci kansu a ciki. Sannan, ta yi kira ga gwamnati, da ta yi ƙoƙarin shawo kan wannan lamari tare da sanya ayyukan kiwon lafiya, a gaba ta hanyar ba su fifiko, musamman domin marasa galihu a Nijeriya.

Marasa Lafiya A Borno Sun Nemi Ɗaukin Gwamnati

Majinyata a Jihar Borno, sun amince da samun ci gaba da aka yi a fannin kiwon lafiya, amma duk da haka, sun roƙi gwamnati da ta sanya baki wajen rage tsadar ayyukan da suka shafi lafiyar.

Mohammed Adamu ya bayyana cewa, an kai matarsa asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri, inda aka tabbatar da cewa; tana fama da matsalar ƙarancin ‘Calcium’, aka kuma buƙaci a yi mata ƙarin gwaje-gwajen da kuɗaɗensu ya kai kimanin naira 4,000.

“Wannan gwaji da aka yi, a baya a kan naira 1,500 ake yin sa. Na san da cewa, an samu hauhawar farashin kayayyaki ya shafi komai da komai, amma ya kamata gwamnati, ta fi bayar da tallafin kiwon lafiya fiye da komai,” in ji shi.

Haka zalika, ya yi kira ga gwamnati, da ta tausaya wa majinyata, musamman ta hanyar rage kuɗaɗen magunguna ko bayarwa kyauta, kamar yadda ya bayyana.

A Asibitin jinya da ke Maiduguri, wani majinyaci mai suna Ahmed Abubakar, wanda aka yi masa tiyatar ‘appendicitis’, ya ce; har yanzu kuɗaɗen da ake kashewa daga suna da matuƙar yawa a jinya.

Abubakar ya ce, ya kashe maƙudan kuɗaɗe wajen gwaje-gwaje, kafin daga bisani likitoci su gano ciwon da yake fama da shi.

“Ya kamata a yi aikin tiyatar a jiya, amma ban iya kawo sakamakon gwajin ba, saboda za a kashe kusan naira 5,000, kuma ba ni da kuɗin,” in ji shi.

Wani majinyaci, Alhaji Mohammed Bulama, ya amince da ingantattun ayyukan asibitin, amma ya buƙaci gwamnati, da ta ɗinke ɓarakar da ke tsakanin ingantaccen kiwon lafiya da kuma samun sauƙin kuɗi.

Mazauna Taraba Sun Koka Kan Halin Ƙaƙa-na-kayi

A Jihar Taraba ma, mazauna jihar sun koka kan tsadar kuɗaɗen aikin jinya a asibiti tare da yin kira ga gwamnatin jihar da ta tarayya, da su duba lamarin.

Bincike ya nuna cewa, da yawa daga cikin mazauna yankin, sun koma amfani da magungunan gargajiya, saboda tsadar kuɗaɗen magunguna da na gwaje-gwaje a asibitoci.

Jibrin Adamu, wani ma’aikacin gwamnati mai ritaya, ya bayyana cewa; ya shafe sama da shekara guda yana fama da rashin lafiya, amma ba zai iya biyan kuɗin gwaje-gwaje da magani ba a asibitocin gwamnati ko masu zaman kansu.

Ya ce, fanshonsa na wata-wata, ya kai naira 70,000, inda ya ce; a lokacin da ya ziyarci Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Jalingo, an nemi ya biya naira 2,500 na katin asibiti, naira 12,000 na gwaje-gwaje da kuma naira 23,000, na magungunan da aka rubuta masa.

Adamu ya ce an nemi ya dawo, domin a yi masa magani, amma bai iya biyan waɗancan kuɗaɗe ba.

“Na gode wa Allah da cewa, maganin da na yi amfani da shi yana taimaka min, yanzu na fi na da,” in ji shi.

Haka zalika, wasu mazauna yankin sun koka da tsadar aikin tiyatar ƙashi, inda suka ce; yanzu ya fi ƙarfin talakawan Nijeriya.

Lami James, wadda ta samu karaya a ƙafarta a wani haɗarin mota a shekarar 2019, ta ce; an kai ta asibitin ƙashi da ke Kano, inda a ƙarshe ta samu kulawa bayan ta kashe maƙudan kuɗaɗe.

Wani mazaunin garin, Nuhu Muhammad, ya ce; kafa asibitin ƙashi a Jalingo, ya ceto mazauna garin, maimakon zuwa Kano neman magani.

Duk da haka, ya lura cewa; tsadar ayyukan gyaran ƙashi, ya tilasta wa marasa lafiya da yawa zuwa wajen masu ɗori na gargajiya.

Daraktan kula da lafiya na asibitin ƙashi na tarayya da ke Jalingo, Farfesa Chubado Tahir, ya kare tsadar aikin gyaran ƙashin.

“Ayyukan tiyatar ƙashi, suna da matuƙar tsada a duk duniya, saboda yanayin aikin na musamman ne,” in ji shi.

Ya ce, kafa asibitin a Jalingo, ya kawo sauƙi ga mazauna garin da a da suke zuwa Kano neman magani.

Tahir ya ce, a cikin shekara ɗaya da aka fara aikin, asibitin ya karɓi marasa lafiya sama da 400, tare da gudanar da manyan ayyuka kusan 200, ciki har da aikin gyaran kwankwaso.

Ya ƙara da cewa, asibitin na ci gaba da faɗaɗa, yayin da Gwamnatin Jihar Taraba, ta ƙara masa fili mai tsawon hekta 12, domin gina shi na din-din-din.

“A sannu a hankali, asibitin zai ba da duk wani aikin tiyatar ƙashi da ake buƙata, ciki har da aikin tiyatar ƙashin baya,” in ji shi, inda ya ƙara da cewa; ana samun ƙarin kayan aiki, don biyan buƙatun da ake samu na kula da ƙashi a Taraba da jihohi maƙwabtanta.

A asibitin ƴansanda na Ultra-Modern da ke Damaturu a Jihar Yobe, majinyata sun ce; idan suka isa wurin, sai sun biya naira dubu ɗaya kafin a buɗe musu babban fayil, da kuma naira ɗari biyar na kuɗin ganin likita.

Haka zalika kuma, suna biyan naira 1,500 a matsayin kuɗin gado na kowace rana.

Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Sojoji Sun Ceto Mutum 92 Tare Da Daƙile Harin Ƴan Ta’adda A Borno
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Uzodimma: Babu Dimokraɗiyya Idan Babu Hamayya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Alamomin Fara Ruɓewar Hannu Bayan Ɗorin Gida
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ministocin Da Suka Ajiye Muƙamansu Ba Su Samu Tikitin Takara Ba

MASU ALAKA

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli
Labarai

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro
Manyan Labarai

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya
Manyan Labarai

Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

June 3, 2026
Next Post
He Lifeng Ya Halarci Taron Ministocin Cinikayya Na Kungiyar APEC Karo Na 32

He Lifeng Ya Halarci Taron Ministocin Cinikayya Na Kungiyar APEC Karo Na 32

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026
Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

June 3, 2026
Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

June 3, 2026
An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Magadan Gari Na 2026 A Beijing

An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Magadan Gari Na 2026 A Beijing

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.