Wani manomi a kasar Ghana mai suna Kofi Atta a halin yanzu na kwance a asibiti cikin wani mawuyacin hali bayan da ya yanke marainansa a lokacin da yake tsaka da barci.
Atta, ya shaida wa BBC a kan gadon jinya ya yi bayanin yadda lamarin ya faru daki-daki, inda likitoci ke ta kokarin duba yadda za su yi masa aiki.
- Dangantakar Sin Da Kasashen Afirka: Yabon Gwani Ya Zama Dole
- Sanata Uba Sani Ya Karyata Rahoton Kudurin Kirkiro Sabuwar Jihar Zazzau
Ya ce a yanzu dai ana sa masa karin ruwa ne tare da wasu allurai da ake ta yi masa, amma dai sai an yi masa tiyata.
Ya kara da cewa a yanzu ba shi da ko kudin da zai biya motar asibitin da za ta dauke shi zuwa babban asibitin koyarwa na Komfo Anokye, da ke Kumasi a kasar ta Ghana, inda a can ne za a iya yi masa babbar tiyata.
Mutumin ya ce, yana barci ne na kailula ne a kan wata kujera sai ya yi mafarki cewa yana yanka nama da ke ajiye a gabansa, wanda zai dafa abinci da shi, inda a cikin barcin ya janyo wuka ya yanke marainan nasa.
Atta, ya ce abin ya ba shi mamaki kwarai domin har lokacin da wasu makwabtansa biyu suka kawo masa agaji bai san me ya faru ba, sai da ya tashi daga kan kujerar ya rika jin wani zafi a gabansa ga kuma jini na zuba.
Mutumin ya ce, har lokacin da aka kawo masa daukin ba shi tabbacin kan abin da ya faru, ji yake kamar yana mafarki ne.
Ya ce shi kansa bai san yadda aka yi ya dauko wukar ba, ”abin ya daure min kai,” in ji shi.
Manomin mai shekara 47 wanda ke garin Assim Akomfode a kasar, har bayan da ya yanke marainan nasa yana cikin barci har ya yi kururuwar neman taimako bai farka ba yana cikin mafarki ne domin shi duk bai san abin da ya faru ba a lokacin.
Ya ce duk da cewa makwabtansa sun kawo masa dauki inda ya rika jin zafi a gabansa ga kuma jini yana zuba, bai fahimci abin da ya faru ba, sai daga baya a gadon asibiti hankalinsa ya dawo ya san abin da ya faru.
A fagen ilimin kula da lafiya, akwai wata larura wadda ake kira ‘Parasomnia’ a Turance, inda mutum kan aikata wasu abubuwa sabanin na hankali a lokacin da yake barci.
Wannan larura takan sa mutum ya rika tafiya ko maganganu ko fitsarin kwance ko mugun mafarki ko kikkifta ido da dai sauran abubuwa na daban a lokacin da yake barcin.
A lokacin da mutum yake cikin wannan hali wasu da ke tare da shi ko kusa da shi za su ga kamar ba barci yake ba yana farke ne, to amma yana cikin yanayi ne na barci bai san abin da yake yi ba.
Mutanen da ke cikin wannan yanayi ba ma sa iya tuna abin da ya faru da su ko abin da suka aikata a lokacin da suke cikin halin.
Bayanai sun nuna cewa abin da mutum kan yi a wannan lokacin kamar yana aikata abin da mafarkinsa ya kunsa ne a zahiri.